← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ha’kuri,wallahi ba abinda yake tunani bane,ni anan ma na ganshi”, sai sannan neh ta lura Sultee ne ke jan Nabila, duk da bata san kan zancen ba tace “Ya Sultee ko ma meh tayi don…..” juyowa yayi ya d’aga mata hannu yace “Ban sa bakinki ba kuma ban nemi kisa bakinki ba,karki yadda ki had’ani da Allah”, ta bud’e baki zata sake magana amma Nabila ta girgiza mata kai alamun tayi shiru kawai kar ya Sultee ya mai da laifin kanta. Sultee ya cigaba da jan Nabilah har motar, yabud’e ‘kofar baya ya turata ciki, ran Amira sai tafasa yakeyi, tama rasa meh ke mata dad’i tsaba kishin da ke damunta. Ji tayi kaman numfashinta yana neman d’aukewa,karanto addu’o’i ta fara sai da taji sanyi sannan ta fara takawa kaman wanda ‘kwai ya fashewa a ciki, wata shegiyar horn da Sultee ya matsa neh yasa Amira ta firgita, ai tuni ta fara sauri. Ta shiga motar ko kallonta baiyi ba ya tada motarshi. Suna isa gida tun kafin Sultee ya gama parking Nabila ta fara kiciniyar bud’e ‘kofa, kallonta yayi ta rear view mirror yace “Karki kuskura ki fita daga motar nan”, ai bai ma gama maganar ba Nabila tayi unlocking na ‘kofar ta kwasa da gudu,parking yayi cikin zafin nama zuciyarshi sai ‘kara tafasa takeyi. © Hanee da maman K [8:54pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Nabila batayi birki a ko ina ba sai d’akinta, tana shiga shikuma lokacin yake shigowa parlour, gwalo ta mishi sannan ta rufe ‘kofar sai tasa key, jingina tayi da jikin ‘kofar tana maida numfashi tana kuma neman tsari daga bala’in Sultee, azuciyarta tana cewa “Tab!! Ni wawiya ce da zan tsaya?, Yanda naga ranshi ya ‘bacin nan komai zai iya min, mtswww, ya takuramin ma wallahi, ni shikenan bazanyi aure ba yakeso ko meh? Dole ne ma na nemi shawara daga wajen Anty Jamcy ko ta whatsapp neh”, nan dai ta cigaba da ‘yan tunane-tunanenta. Sultee ranshi ya kai ‘kololuwar ‘baci,afili yace “Ni kika ma gwalo?wallahi ki bud’e ‘kofar nan tun kafin raina ya gama ‘baci in ba haka ba next had’uwar mu bazaiyi kyau ba”, Nabila tana jinshi sai ta murgud’a baki kaman yana ganinta, d’aga muryanta tayi yanda tasan zai jita “Ba sai mun sake had’uwa bane zaka min iskanci, ai wallahi kayi dama nayi hagu daga yau, mutum sai takuri ko ubana albarka, kai kayi aure nikuma kanaso namutu a gobruwa?”, girgiza kai yayi yana ‘kara jin zafin maganganunta,shi kad’ai yake magana “Ni yarinyar nan zata gaya ma magana?, no problem, in ta shiga hannuna sai na yi maganinta”. Ranshi a ‘bace ya juya fuu yabar wajen sai side nashi. Duk abinda akeyin nan a idon Amira, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta, da gudu tashige d’akinta ta fashe da kuka. Kishi neh yake cinta ba kad’an ba, kukan neh kad’ai zai sa zuciyarta tayi sanyi, dama ance kuka rahma neh. Haka gidan ya kasance a ranar kaman gidan zaman makoki, shuru kakeji sai kukan tsuntsaye. Da dare ya shigo musu da kayakinsu, ajiye ma Nabila nata yayi a ‘kofar ta sannan yayi sallama ya shiga d’akin Amira. Ganinta yayi ta kifa kanta a guiwowinta tana kuka akan sallaya, da gani ta idar da sallah neh kukan yaci ‘karfinta. Ko kad’an baiji tausayinta da halin da take ciki ba, cikin ko in kula yace “Ga kayanki, sai da safe”, ya juya kenan ita kuma ta d’ago kanta, har zai fita daga d’akin asanyaye ta ‘kira sunanshi “Ya Sultee….” © Hanee da maman Khalil [9:59pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Sultee ya tsaya chak amma bai juyo ba, share ‘kwallar da ya zubo mata tayi sannan tace “Ya Sultee inaso na tambaye ka ne”, juyowa yayi yana kallonta, ya saka hannayenshi duka biyu a cikin aljihu. Amira tace “Ya Sultee fisabilillahi abinda kakeyin nan ya dace? Nabila fah ta girma tazama cikakkiyar budurwa kuma yanzu university take, in ka hanata kula samari yanzu sai yaushe kake so ta kulasu? Shekaru ‘karuwa sukeyi fah ba raguwa ba, Life cycle na mace kad’an ne, Daga takai 25 dai toh wallahi samarukan gudu sukeyi, In ka hanata har sukazo suka watse kam ya zakayi da ita?”. Tuni Sultee ya had’e rai, a fusace yace “What do you mean?, Meh ruwanki?, ‘kanwata ce fah and duk yanda naso tayi dolenta hakan za tayi, And da ki ke maganar inta kai 25 samarin zasu watse, Mata nawa suke kaiwa 30+ amma still suna aure?, karki sake samuna da wannan banzan maganar, it’s none of your business”. Hawaye sharkaf a fuskan Amira, ta d’ago da jajayen idanunta ta d’aurasu a kanshi tace “Wai nikam ya Sultee ni kake aura ko kuma Nabila?, Takuran da kake mata ni bakamin irinshi, kulawan da kake bata, damuwar ka agareta, komai ma ita kake ma amma ni baka min, karka manta fah aure ba wasan yara bane, in sonta kake yi gwara ka aureta kawai, kaga in ka aureta ni na huta, kaima ka huta sannan itama ta huta”. A firgice yake kallonta, a razane yace “Kinsan meh kike fad’a kuwa?, ko ina da ra’ayin auren mata biyu you know definitely zan iya tunda ni ba rago bane kuma ina da kud’in, in zanyi ma sai na rasa wanda zan aura sai wannan fitsararriyar? jinjira wacce bata wuce a raineta ba?, mtswww please karki ‘kara ‘batamin rai da daren nan”. Bai jira meh zatace ba ya fita daga d’akin, Amira ta d’anji sanyi a ranta tunda dai Sultee ya ambaci bayason Nabila don ta mishi ‘karama, nafilfilu ta dinga yi sannan bacci ya kwasheta. ©Hanee da maman Khalil [10:12pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ®OHW da ©Khadijah maman Khalil Washegari Nabila bata fito daga d’aki ba har saida taji Sultee yabar gidan, cikin sand’a da alamun rashin gaskiya ta nufi kitchen, nan ta tarar da Amira. Murmushi tayi sannan tace “Good morning anty Amira”, itama murmushin ta mayar mata sai tace “Morning sis,kin tashi lafiya”, Nabila ta d’anyi hamma tace “Wallahi yunwa nakeji,tun jiya da rana rabo na da abinci”, Amira ta d’anyi jim sai tace “Ba kin tsokani ya Sultee ba?, nikam meh kika mishi neh?”, guntun tsaki Nabila tayi sannan tace “Anty Amira mijinkin nan yanada matsala,wai fah don ya ganni da wani shine ya ‘bata rai ya fara ja ma sai kace kayan wanki, ni gaba d’aya ya takurani a gidannan”. Dafata Amira tayi tace “Yi ha’kuri, komai zai wuce in Allah ya yarda, kawai dai ki dinga kiyaye dokokinshi, gashi yanzu yana nemanki ruwa ajallo, hmm ina tsoron ranar da zakuyi karo a cikin gidannan”. Dariya Nabila tayi sannan tace “Ba saina yadda bane zai ganni? Dodging nashi zan dingayi, yana shigowa zan gudu d’aki, yana fita kuma zan sake na zauna a parlour abuna”, murmushi Amira tayi tace “Ke dai baki tsoro, ki bar neman magana dashi ni dai na gayamiki, yanzu ga breakfast naki nan ki d’auka kije kici”, Nabila ta d’auki plate tana d’iba tace “Barin je parlour naci”. Yinin ranar tayishi a sake tunda Sultee yana wajen aiki. Haka dai kwanaki suka ta ja har yanzu su Nabila sunyi mid-semester exams, tun da sukayi rikici bata sake bari sun had’u ba, tana jin alamun ya dawo gida take komawa d’aki, in zata tafi lectures na safe kuma tun 6 take fita a hankali tace driver ya kaita, in ta dawo kuma taga alamun yana side nasu toh bazata shiga ba, saidai ta la’be a ta wajen flowers in taga ya shiga side nashi sai ta ruga dagudu tayi d’akinta. ©Hanee da maman Khalil [11:11pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Abinda Nabila bata sani ba shi ne duk ‘boye-‘boye da gudun shi da takeyi duk yana ganinta, da yake yanada time table nata so duk tym da yasan morning lectures take dashi zai zauna a ta wajen window yana le’kenta, har ta gama tafiyar sand’arta zuwa motar, shi kam tun abun yana bashi haushi har yazo yafara bashi dariya, zama yakeyi musamman yayita dariya shi kad’ai. Yau ya kama Thursday kuma yau ne Sultee zai tafi Switzerland don aikin office nashi, ya shirya tsaf sannan ya je ya samu Amira yace “Ni zanyi tafiya, duk abinda zaku bu’kata akwai a store kuma nasa miki kud’i a account haka ma Nabila ita ma nasa mata, karki yadda ki barta ta fita wai don bana gari in har ba school zataje ba, in kin barta ma za a gayamin”. Har ya kai ‘kofa sai ya juyo yace “Ba rakiya?”, murmushin ya’ke tayi sannan ta rakashi har bakin motar wanda driver zai tu’kashi zuwa airport, tana d’aga mishi hannu har motar yabar harabar gidan. Wani ajiyar zuciya ta sauke, a fili tace “Alhamdulillah, zamu huta da bala’i na kwana biyu”. Nabila tadawo daga karatu da yamma tazo ta tarar da wannan good news na tafiyar Sultee, har rawa saida tayi don murna, nan ta zauna take tambayar Amira “Anty, yaushe yace zai dawo? I hope dai ba kwanan nan ba?”, Amira tace “I have no idea don bai gayamin ba and ni kuma ban tambayeshi ba”. Murmushi Nabila tayi sai tace “Allah yasa ya dad’e”. Tana kwance da daddare kawai sai taga text message daga Sultee,yace “Salamu Alaikum, ki ‘kare guje gujenki, yanzu kam kin huta dani for some days amma in na dawo na samu kin tsallake rules nah kema kinsan sauran”, dariya Nabila tayi sosai sannan ta mishi reply “Don Allah karka dawo dawuri”. Sultee na karantawa yayi wani smile kawai ya ajiye wayar. Nabila ta zama free, komai yi takeyi, yau tana mall nan gobe tana chan, ita har ma ta manta da wani Sultee. Bayan kwana shida da tafiyarshi Nabila ta kunna music a parlour sai rawa takeyi, Amira kuma tana zaune tana viewing nata a waya, ihu sukeyi ba kad’an ba. Rawa ya d’au dadi kawai sai ga Sultee da friends nashi su biyu,da yake Nabila ta bama ‘kofa baya so bata san sun shigo ba, Amira kuwa sumar zaune tayi a wajen da take, tana ta ma Nabila nuni da ‘kofa amma ina!! Nabila tayi nisa sai
Chapter 12 · 0% Book details