Sashe 4
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya akayi,tiryan tiryan ta bata labari,dariya tayi sosai sannan tace “Auta zuciya,Nabilah neman magana” dariya sukayi gaba dayansu. Da aka gayama mai martaba ma girgiza kai yayi sannan yayi dariya yace “Allah ya kyauta” Abangaren Saleem tunani yakeyi a zuciyarshi “Ashe dai yarinyar bata da matsala,saidai daga jin magananta akwai yarinta a tattare da ita,matsalarta dai shine akwaita da tsiwa,nasamu ‘kanwa”,Nabila ma dai maganar takeyi da zuciyanta “Yanada fara’a,ashe shi ba mugu bane kaman yanda na tsamman,naji dadi nasamu yaya wanda zamu dinga hira mu fita yawo tare” Yinin ranar haka sukayi shi cike da nishadi,sukaje lambu suna ta hira sai Nabila tace “Ya Saleem wlh guava nakeso naci,barinje na tsinka” dasauri ya tashi tsaye yana dariya yace “wa?ke zan bari kije ki tsinka?saidai in inaso ki rusa min kai” dariya Nabila tayi sosai saitace “Kai haba,ai ranan ma bansan kana nan bane saisa” kama hannunta yayi yace “A’a,ki dai zo muje na tsinka miki”. Hanee da maman Khalil [9:14pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Haka kuwa akayi,yaje ya dauki dogon sanda ya bubbuge musu guava dewa,dama akwai tap a wajen so sai kawai sukaje suka wawwanke suka baje sunaci. Gaskiya Saleem daban yake,yanda yake abu kaman ba d’an sarauta ba,sarautar ma mai ‘karfi na garin Yura,masarautar da ake ji dashi sosai a Kaduna state,bai da ji da kai da kuma nuna yafi wani,he is just living a simple life. Duk bidirin da Saleem da Nabila ke yi a lambu ashe dai Sumayya tana la’be tana ganinsu (Sumayya ‘yar mai yin goge-goge neh agidan,tafi su Nabila da kad’an). Mai martaba neh yakira Saleem awaya yace ya sameshi a ‘karamin parlour,ya gayama Nabilah sannan yace “ki jirani fah,ina dawowa yanzu” ta amsa mishi da “Toh”. Yana tafiya ba da dadewa ba Sumayya ta iso inda Nabila ke zaune,tsayawa tayi tana girgiza kwankwaso,Nabila ta kalleta ta watsar,a wula’kance tace “Ya da tsayamin akai?in ma neman fad’a kikeyi da ni toh a shirye nake”,tsaki Sumayya taja sannan tace “Uwar shishshigi,uwar kinibibi,uwar ‘kwazo,meh ya hadaki da Auta da har kike wani shishshige mishi haka?in ma sonshi kikeyi toh gwara ki cireshi daga ranki don shi nawa neh ni kad’ai” dariya Nabilah ta kwashe dashi,tayi mai isarta saitace “Wayyo Allah,an gayamiki ni bunsura ce kamar ke?ke wani abu wai so ya dama,ni banma sanshi ba balle na ma wani shi” Sumayya taji zafin maganar sosai tace “shegiya munafuka,kinsani kam” Tsaki Nabila taja tace “Wannan kuma sai ki tsaya in yazo saiki gayamishi,shi da bai masan da zamanki ba” nan fah fad’a ya kaure tsakaninsu,jibgar juna sukeyi ba kad’an ba,Saleem yadawo da kyar dai yasamu ya raba fad’ar,cikin kuka Nabila ta labarta mishi abinda ya faru. Wanka ma Sumayya mari yayi,yanuna ta da yatsa sannan yace “Sumayya kike ko meh?daga yau kika ‘kara kuskuren kama Nabila da fad’a wlh saina hukunta ki,wuce ki bani waje!!!” a firgice Sumayya ta tattara dankwalinta tabar wajen Hanee da maman Khalil [9:42pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Saleem ya zauna ya dinga lallashin Nabila har dai tayi shiru suka ci gaba da hiransu. Akwana a tashi ba wuya wajen Allah,Nabilah ta zama cikakkiyar budurwa,ta ‘kara kyau,ga ta ‘bul-‘bul da ita gwanin ban sha’awa,ga uwa uba dirin da Allah yabata. Ayanzu shekarunta sunkai 18,tagama secondary school,mai martaba yace zai turata ‘kasar waje tayi karatu,ranar baba Rabi tayi kuka ta godema Allah da wannan sarki mai sonsu da son cigabansu. Saleem yanzu yana da shekaru 28,tsakanin shi da Nabila kuwa wani sha’kuwa neh wanda bazata misaltu ba yashiga tsakaninsu,wasu har tsammani suke ko suna soyayya amma ko d’aya,shi a matsayin ‘kanwa ya dauketa itama kuma a matsayin yaya ta daukeshi. Mai martaba yayi-yayi da Sultan ya fitar da mata don yanzu yakai 36 amma kullum maganarshi daya “Abba kayi ha’kuri,aure lokaci neh sannan ni har yau banga wacce ta kwantamin a rai ba” wani lokacin mai martaba har yayi tunanin “ko dai Sultan baida lafiya neh?” Ranar wani talata dangin Sarki Mu’awiya sukaje neman aure a garin yola,’yar sarkin garin Hamaz,sarkin Hamaz abokin Sarki Mu’awiyah neh na sosai da sosai,shine ya nema ma Sultan auren ‘yar sarkin Hamaz mai suna Amirah. Sunje garin Yola lafiya lau kuma an ‘kar’besu hannu bibbiyu sannan aka yanke ranar biki nan da wata biyu. Duk abinda akeyin nan uban gayyar wato Sultan bai sani ba,yana chan Qatar yana aikinshi hankali kwance. Yarima neh zaune a office shi da abokinshi,mai martaba ya kirashi,cikin girmamawa ya gaisheshi da tambayar lafiyar gida,mai martaba yayi gyaran murya yace “Yarima,tunda naga bakada niyan aure gashi shekarunka ‘kara gaba sukeyi shine na nema maka auren ‘yar abokina mai suna Amirah kuma Alhamdulillah sun baka,an sa ranar biki nan da wata biyu” da yake Sultan mai biyayya neh sai yace “Nagode,zan dawo kwanan nan don hidimar bikin,Allah ya ‘kara nisan kwana” mai martaba yayi murmushi yace “Ameen Yarima,Allah ya maka albarka”,yarima ya amsa da “Ameen” sannan sukayi sallama ya katse wayar. Abokinshi mai suna Abdul yace “Yadai mutumina?naji kana maganar hidiman biki,daman aure zakayi?” girgiza kai Sultan yayi yace “Unexpected aure ba don ni bansani ba sai yau”. Nan dai suka cigaba da tattaunawa Wacece Ameerah? Kudai biyomu ni Hanee da maman Khalil kusha labari;);) GIMBIYA NAFEESAH [10:36pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sarki Ibrahim Umar sarkine na babbar masarauta mai suna Hamaz dake jihar Adamawa,yanada mata biyu-Na farkon sunanta Sarauniya Fatima,na biyun kuma sunanta Maryam. Fatima tanada ‘ya’ya uku-Gimbiya Ameerah,Yarima Ukasha sai autar ta mai suna Gimbiya Nafeesah wacce tun tana ‘yar kankanuwar ta wata rana an kwantar da ita tana bacci a d’aki shikenan aka nemeta aka rasa,ba ‘karamin tashin hankali suka shiga ba musamman ma mai martaba da ya d’auki son duniya ya d’aura ma Nafeesah don sunan mahaifiyarshi taci,neman duniyar nan sunyi amma har yau ba ita ba labarinta.. Sarauniya Maryam kuma tanada ‘ya daya mai suna Hauwa wacce take sa’ar batacciya Gimbiya Nafisah. Ameerah tanada shekaru 24 dayake sarkin Hamaz bai samu haihuwa dawuri ba,tana karatu a AUD tana final year ayanzu haka,sarkin Yura da sarkin Hamaz abokai neh tun tashinsu,tare sukayi skul har suka gama sannan kowa ya koma garinsu daga baya kuma kowanne yazama sarki bayan iyayensu sun rasu. Awani meeting na sarakuna neh da suka hadu shine suke tattauna matsalolin familynsu,a hirar neh ma sarkin Hamaz ya tambayi sarkin Yura “Nikam ina Sultan neh?ya batun aure?ko har yanzu bai shirya bane?” sarkin Yura ya sauke wani ajiyar zuciya yace “Wani aure?mutumin da har yau yakasa fitar da mata,ni fah in gayama har nafara tunanin ko baida lafiya kokuma aljanu sun aureshi,ace mutum shekara 36 amma har yau shiru” sarkin Hamaz yayi dariya irin tasu ta manya yace “Allah sarki,inkaga haka toh fah lokacinshi neh baiyi ba,adai ta addu’a Allah ya za’ba ma ‘ya’yanmu abinda yafi zama alheri” sarkin Yura ya amsa “Ameen” sannan ya d’anyi jim na wani lokaci,sarkin Hamaz ya d’an ta’bashi yace “Lafiya kake dogon tunani haka?” murmushi sarkin Yura yayi saiyace “Nasamo mafita neh”,gyara zama sarkin Hamaz yayi yace “Inajinka,wani irin mafita kenan?”. Haneefah Usman OHW da maman Khalil [10:53pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sarkin Yura yayi gyaran murya yace “Ni in da zaka yarda da na had’a ‘yarka Ameerah da Sultan aure,yarinyar tanada nutsuwa ga hankali” Hade fuska sarkin Hamaz yayi yace “Banyi tsammanin zaka d’auka akwai bambanci tsakanin ‘ya’ya nah da naka ba,yanda kakeda iko dasu Sultan toh wlh nabaka iko akan ‘ya’yana gaba d’aya,nasan Ameerah bazata bani kunya ba kuma daman batada wani tsayayye” murmushi mai cike da farin ciki sarkin Yura yayi sannan yace “Nagode,amma dai zanturo ayi tambaya kaman yanda yake a al’ada”,fuska a sake sarkin Hamaz ya amsa “Ba komai,sai sun iso,in yaso sai asa date ma kawai” sarkin Yura ya jinjina kai yace “Hakan za ayi kuwa” Da sarkin Hamaz yakoma gida ya tara iyalanshi ya labarta musu yanda sukayi shi da sarkin Yura,Sarauniya Fatima tayi farinciki ba kad’an ba don tasan Sultan yaro neh mai hankali da sanin ya kamata,daga baya yace a kira mishi Ameerah,itama ya sanar da ita,cikeda kunya tace “Bakomai Daddy kuma in Allah ya yarda zaka sameni mai biyayya”. Sarauniya Maryam da Sarauniya Fatima neh zaune a babban parlour suna hira,bazaka ta’ba cewa kishiyoyi bane don suna shiri fiye da tunanin mai karatu,S.Maryam tace “Anty(da yake anty take kiran S.Fatima) ni dai na d’auki nauyin gyara ‘yata ciki da waje,ina fatan ba matsala?” murmushi S. Fatima tayi saitace “Ai dukkansu ‘ya’yanki neh,duk abinda ya dace kiyi” Da hakan neh sarkin Yura ma yakoma gida har akaje tambaya aka saka ranar biki nan da wata biyu shine yakira Sultee ya gayamishi Wannan kenan Haneefah OHW da Maman Khalil [11:09pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Back to labari Bayan kwana biyu kuwa Sultee ya diro garin Kaduna,jallabiya yasaka designer irin dark coffee colour dinnan mai she’ki,gashi fari sai kyaunshi ya ‘kara fitowa wane balarabe(Su sadydy ma saida suka hadiye yawu,ni dai nace yafi ‘karfinku ehe:roll::roll:),yasaka agogo black shima daga gani kud’i yayi kuka a sayenshi. Motocin da suka dira a airport kamar masu tarar President,ga dogaraye neh,securities neh,duk dai gasunan anzo tarar Yarima Sultan mai jiran gado,da muka ganshi maman K ta taboni tace “Ke Hanee anya wannan mutum neh?” nace “Mesa kika ce haka?” atsorace tace “Kina ganin kyau kaman aljani fah,nikam nagudu wlh ina tsoro” nan take ta ari na kare,bironta ma yarwa tayi,nikam dariya nayita mata. Nan aka budemishi motar,nima dai neman motar nayi daga cikin convoy d’in na la’be tunda maman K tagudu tabarni. Ana isa masarautar akayi parking,red carpet aka shimfida a ‘kasa,akan carpet din an rubutu sunanshi in capital letters YARIMA SULTAN,ahankali ya fito da ‘kafafunshi daga motar,dogarai da mutanen gari sai kwasan gaisuwa sukeyi,murmushi kawai yakeyi gamida d’aga musu hannu alamun yagode yagode. Ya isa wajen iyayenshi ya rungumesu,mai martaba bakinnan ya kasa rufuwa don rabon da yasashi a ido yakusa shekaru 10,shi Sultan baison zama a 9ja wai don bayason surutu. Nabilah da Saleem neh suka fito atare,dagudu Saleem ya rungume yayan nashi wane ‘karamin yaro,Nabila acikin sanyayyen muryanta tace “Barka da isowa Ya Sultan”,sai lokacin