← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GIMBIYA NAFEESAH
[7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Baba Rabi tasa ‘kuyangi aikin ‘kosai kamar
yadda suka saba wani lokacin sannan aka
rabawa yara a waje.
Da yamma Amina da Jamila suka gama shirin
islamiyya tun da wuri sannan suka nufi dakinsu
Nabila,sun isa lokacin ma ta fito daga wanka
tana shafa mai a hankali. Jamila ce tafara
magana tace “Laa!! Nabila dama baki gama
shiri ba?kinga fah hudu ya kusa kuma ana
dukan latti” charaf Amina ma ta ‘karba tace
“Allah Nabila baki kyautawa,don ke baki tsoron
bulala saisa kullum kike samu lattin amma ai
mu muna tsoro” mtswww Nabilah taja wani
dogon tsaki tace “Subhanallahi,kai ni fah kun
cikamin kunne kun takuramin,d’aure ‘kafafunku
nayi neh da dole saikun jirani mun tafi tare? In
bazaku iya ba Bismillah ku kama hanya,saimun
hadu a aji”. Jamila ta bude baki zata yi magana
amma Amina ta girgiza mata kai akan tayi shiru
gudun kar daga magana kadan cibi yazama
‘kari,asanyaye Amina tace “Allah yabaki
ha’kuri,barimu jiraki a ta ‘kofar gida” batare da
ta kallesu ba tace “Naji,saiku fita bari nasa
kaya”. Jamila ta ‘kulu iya ‘kuluwa don itakam
ta tsani hali irinna Nabilah,hali na gadara da ji
da kai kamar ‘yar MULKI KO SARAUTA. Basu
sake cewa komai ba suka juya suka fita daga
dakin.
Nabila bata fito ba har wajen 4:15,ta iso
wajensu tana taku d’ad’d’aya,tace “Mutafi
ko?”,suka kama hanya sai islamiyarsu da ke da
d’an nisa da masarautar. Suna shiga gate na
islamiyar sukaga an tara ‘yan lattin kuma
malam Dawud neh yake duka,zo kuga su Amina
da Jamila jikinsu sai rawa yakeyi,Nabila kuwa
ko a jikinta tunda dai ita ba tsoron bulala takeyi
ba. Malam Dawud yamusu bulala biyar-
biyar,Amina da Jamcy sai kuka sukeyi harda
ajiyar zuciya,nan duk suka kama hanyar ajinsu
da yake aji uku suke dukkansu. Suna wucewa
neh sai wata ‘yar aji biyar mai suna Aceey
tafara musu dariya tana nunasu da
hannu,Nabilah taja tsaki tace “Kutuma,kuna
ganin yarinyar nan wai dariya take mana,kuzo
muje muci ubanta” Amina tace “Nikam wlh
bazanje ba” Jamila ma tace “Nabilah ki raba
kanki da fada,ba sai tayita dariyan ba in
tanaso” Nabilah tayi wani mahaukacin dariya
tace “Ai wlh in na bari an sha da ni”. Dasauri ta
nufi wajen da Aceey take zaune,Aceey ta
sunkuya tana daukan pencil nata da ya fad’i
a’kasa kawai saitaji an tureta,jikake ta fadi
a’kasa tim,dama Aceey irin yarannan neh
marasa ‘karfi amma sai tsokana. Nabilah
dukanta takeyi ba ji ba gani har saida aka kira
malamai da kyar suka raba fad’ar,fuskar Aceey
duk yayi ja tsaba naushin da tasha,aka tattara
su aka kaisu office na headmaster,nan aka ma
Aceey bulala takwas tunda ita fara tsokanar sai
akama Nabilah kuma guda uku.
Haneefah Usman da Maman Khalil
[7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Nabilah haushi bibbiyu ya hadun mata,ga
haushin an rabata fad’a da Aceey ga kuma
dukan da tasha. Har aka tashi daga islamiya ba
wani walwalar kirki a tare da ita.
Suna isa gida tawuce da’kin Nene don tasan
bazata rasa rake ko aya awajenta ba,a ‘ka’idar
ta inhar ranta ya’baci toh fah abu biyun nan
neh kawai suke sata nishadi. Ta shiga ‘dakin
Nene da sallamarta,cikin sakin fuska Nene ta
amsa mata sannan suka gaisa,chan sai Nabilah
tace “Nene rake nakeso” ko da Nene taji haka
tasan dawar garin,ta tashi ta dauko mata rake
sanda daya da aya ‘kulli daya. Nabila ta cire
himar nata ta gyara zama tanashan rakenta
suna hira da Nene,sun dad’e kad’an sannan ta
tashi ta koma d’akinsu tacire uniform nata
sannan tayi alwala tayi sallah da ‘yan nafiloli
don Nabila ba baya ba wajen ibada duk da
‘karancin shekarunta.
Wajen ‘karfe 8pm baba Rabi takai ma mai
martaba abinci,Nabila tagaji da zama ita kadai
kawai saita tashi ta nufi sashen Yabi. Sun dade
suna hira,acikin hirar neh ma Yabi tace
“Nabee,auta nah zai dawo gobe fah” Nabila
tadanyi murmushi tace “Ayyah,ni bansanshi
bama” Yabi tace “Ehh,lokacin da yatafi kina
bakida wayo saisa”,Nabilah ya jinjina kai tace
“Hakane kam,Allah ya kaimu”,Yabi tayi
murmushi tace “Ameen Nabee”
Haneefah Usman da maman Khalil
[7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman
Da asubah bayan sun idar da sallah baba Rabi
tace “Nabilah”,Nabilah ta amsa a nutse “Na’am
ummu”,baba Rabi ta gyara zamanta tace “Yau
d’ana zai dawo wato saleem,autar
gidannan”,Nabila tayi murmushi tace “Eh jiya da
dare Yabi ta gayamin”. Baba Rabi ta d’anyi jim
sannan tace “Inaso ki nitsu,banda wawanci da
sakarci,banda raini don shi ba sa’ar ki bane,duk
abinda yace kiyi inhar bai sa’bama addini
ba”,Nabila ta sunkuyar da kanta ‘kasa asanyaye
tace “Toh umma,nagode kuma zanyi abinda
kikace” baba Rabi tayi murmushi tace “Allah
yasa miki albarka ‘yata” Nabila ta amsa da
“Ameen”.
Gida ya kachame da shirye shiryen dawowar
Saleem,abinci kala-kala,ga wasu decorations da
akayi an rubuta WELCOME HOME AUTA(dayake
Auta iyayenshi ke kiranshi).
Misalin ‘karfe biyar na yamma Saleem ya iso
masarautar Yura,motocin da suka tarboshi ni
kaina kasa ‘kirgasu nayi,jeeps neh masu
numfashi ba’ka’ke sai she’ke sukeyi,aka
shimfid’a red carpet daga ‘kofar motar da zai
fito har zuwa sashen mai martaba sarki
Mu’awiyah. Fuskokin ‘yan gidan cike yake da
murna. Yadau lokaci kad’an sannan yafito,black
jeans yasa da t-shirt fari,kyakkyawa neh irin
chocolate in complexion haka. Taku yakeyi irin
na ‘ya’yan sarauta masu ji da kudi da
mulki,mutane sai kwasan gaisuwa
sukeyi,bakinshi ya kasa rufuwa tsaba jindadin
dawowarshi cikin familynshi.
Yana shiga fada dagudu yaje ya rungume Yabi
yace “Ummi,I missed u very badly,kullum ‘kara
kyau kikeyi” Yabi sai murmushi takeyi tace
“Auta,kai baka girma ko?” dariya yayi sannan
yace “Inhar a wajenku neh kam toh bana girma”
duk sukasa dariya sannan yaje ya rungume mai
martaba. Aka gaggaisa sannan ‘yan fada suka
watse suka barsu su ukun,chan sai saleem
yami’ke,Yabi tace “Auta ina zuwa daga
dawowarka?” murmushi yayi yace “Ummi banga
baba Rabi ba shine zanje na dubota” girgiza kai
kawai mai martaba yayi don shi har mamakin
sha’kuwar da ke tsakanin baba Rabi da Saleem
yakeyi
Haneefah Usman da maman Khalil
[7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Haka kuwa akayi,yana shiga d’akin Baba Rabi
itakuma lokacin tana shirin fitowa,wangale baki
tayi tana murmushi harda d’an
kwallarta,rungumeta Saleem yayi sosai yace
“Baba Rabi na sameku lafiya?ina
kanwata?”,baba Rabi tace “Dazun nan ta tafi
islamiya” saleem yayi murmushi yace “Ashe dai
ta girma”. Suna hira suna tafiya har suka isa
fadar sarki,nan aka jejjera abinci kala-kalar da
juices,snacks,tarkace dai daban-daban. Akaci
aka ‘koshi sannan aka tafi sallar maghrib.
Da Nabilah tadawo fuskar baba Rabi cikeda
annushuwa,Nabilah take tambayarta “Umma,yau
dai naga farincikin ki daban neh” baba Rabi tace
“Kwarai kuwa,auta yadawo”. Nabilah tace
“Ohhhh kinga ni wlh na ma manta” baba Rabi ta
d’an harareta tace “Amma shikuma yana isowa
saida ya tambaye ni ina kike”,Nabila tayi
murmushi tace “Allah sarki”. Itama sallar tayi
sannan tayi isha anan bacci ya kwasheta,ba ita
ta farka ba sai asubah.
Washegari da yake thursday neh ba islamiyya
kuma tunda ana hutun boko Nabila sai bacci
takeyi har 9 ta tashi,tayi wanka sannan ta
gyara da’kin,tunda ta tashi take jin kwadayin
guava sai kawai ta yanke shawarar zuwa
lambun gidan ta tsinko amma kuma bata iya
ba. Ta gama komai nata sai ta nufi dakin su
Amina,da yake ta wajen akwai kule saita ruga
dagudu,tana d’aga labulen taci karo da Uwani
(Maman Amina). Uwani taja tsaki tace “kai
Nabilah,kekam bansan yaushe zakibar yarinta
ba,kina abu kamar zararriya” maganar yama
Nabilah ciwo, sai tace “Saidai in ‘yarki neh
zararriya badai ni ba”. Ta juya dagudu tabar
wajen,Uwani ta girgiza kai kawai ta bita da
kallo tana mamakin irin rashin tsoron Nabila.
Nabilah d’akin su Jamila tanufa,tare suka jera
har lambun. Da yake dukkansu biyu basu iya
hawa bishiya ba sai Amina kuma batanan sai
kawai Nabila tace “Barin dauki manyan duwatsu
na dinga jefawa a saitin guava din,zamu samu
ko kad’an neh” Jamila tace “Ehh kin kawo
point”. Hakan kuwa akayi,tayita jefawa kuma
tasamu mai d’an yawa sun zubo ‘kasa,da taga
duwatsu biyu neh kawai suka rage mata a
hannu kawai saita dage iya ‘karfinta ta jefa
nafarko,Saleem dake zaune acikin lambun
dayake yana son zama awajen yaji sau’kar
dutse daga sama,daga kan da zaiyi lokacin
kuma Nabila ta ‘kara jefo wani dutsen,ai ba shiri
ya mi’ke dasaurin shi ya nufi ta inda dutsen
yafito. Yana isa yaga suna kwashe guava dinsu
hankalinsu kwance,afusace ya nufi wajen,jamila
na ganin haka ta arche da gudu,Nabila kuwa ko
ajikinta. Yana isowa wajen ya cafkota ya ja
gashinta yace “Hey!!!bakida hankali neh??” ta
fara ‘ko’karin kwace kanta amma takasa saitace
“Yadai malam,kai waye da kawai zakazo ka
cakumoni” tsaki yaja ya saketa yana mamakin
‘karfi hali irin na yarinyar. Ta tsugunna ta
kwashe sauran guava din,har tayi nisa sai kuma
ta tsaya tajuyo ta gyara skirt nata sosai sannan
tace “Sssssssss malam” yasan dashi takeyi
amma sai ya basar,ita ba haka taso ba saita
sake “Ko kana tsoro neh?kazo mana” abun
haryaso bashi dariya wai tsoro,yana juyowa ta
mishi gwalo,yabita da gudu itama kuwa daman
da riga tayi ready ta kwasa da gudu. Da yaga ta
gudu saiya tsaya yafara dariya azuciyarshi yace
“Yarinyar nan batada kunya amma zanyi
maganinta”. Tana isa daki taga Jamila
azaune,nan itama ta zube tafara maida
numfashi.
Afuwan don Allah,wlh naje biki neh saisa
banzauna ba kuma maman Khalil tana jinyar
sistanta amma In Sha Allahu daga yau zamu
dingayi kullum.
Haneefah Usman da Maman
Chapter 2 · 0% Book details