← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 23

Sashe 1

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read



GIMBIYA NAFEESAH
[6:58pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
©ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Wata yarinya muka gani ta rugo dagudu tana
kwala ma baba Rabi kira,baba Rabi dake kitchen
tana ma kuyangu bayanin abinda sarki zaici da
dare jin k’iran yayi yawa yasata fitowa.
Yarinyar ta iso wajen baba Rabi tafara
hak’i,alamun dai tasha gudu ta gaji,yarinyar
tace “ba….ba….Rabbb….iii…na….bi…” baba Rabi
tayi saurin tsaidata tace “Ni fah bana gane meh
kike fada,ki nitsu saikimin bayani” yarinyar tayi
shiru tana maida numfashi,sai bayan ‘yan
seconds sannan tadawo daidai,baba Rabi tace
“Inajinki Amina,biyoki akayi neh kikazo da irin
wannan uban gudun?” yarinyar da aka k’ira da
Amina tace “A’a wlh baba,Nabila ce take dukan
Jamila achan wajen bishiyar da muke zama”
baba Rabi ta dafe k’irji gamida yin salati tace
“Ohh ni Rabi,wacce irin hasabibiyar yarinya neh
wannan?,muje” cikin sauri suka nufi wajen
bishiyar da Nabila ke zama tareda sauran
sa’anninta suyi hira da yamma. Muma dai
muna biye da ita don ganin ma idanunmu
abinda ke faruwa
Baba Rabi na isa wajen taga Nabila akan Jamila
sai jibgarta takeyi kamar an aikota,bata ma san
baba Rabi tazo wajen ba,cikin zafin nama da
bacin rai baba Rabi ta buga mata wani uban
dundu wanda saida yayi k’ara. Bashiri Nabilah
ta bar jibgar Jamila ta duruma ashar tace “Kan
ubanchan!!! Wani dan iskan neh yamin wannan
dundu haka? Wlh saina rama” sannan ta tashi
daga kan Jamila da bakinta yafara jini tafara
karkade jikinta ta k’ara tamk’e damarar ta
yanda zataji dadin dambe,tana juyowa tayi karo
da baba Rabi wanda fuskarta yana murtuk’e ba
alamar wasa a tare da ita. Cikin in’ina Nabila
tace “Ba…ba…wlh….” baba Rabi ta wanketa da
mari tace “Ke wace irin yarinya neh wai?ba
ranar da gari zai waye har dare yayi bakiyi
dambe ba” idon Nabilah suka ciko da kwallah
amma ta danne don ta tsani aga
hawayenta,acewarta wai in an gani za a rainata
don ita batason raini. Tajuya wajen da Amina
take rak’ube ta wurga mata harara tace “Toh
munafuka algunguma,kinji dadi tunda kin kai
gulma kuma anzo an mareni,wlh karki yarda
muhadu don saina miki lis kuma…” baba Rabi ta
gubje bakin tace “Yi min shiru,kuma ki wuce
d’aki kizauna sanna karki kuskura kice zaki
tab’a Amina in ba haka ba saina mugun sab’a
miki” Nabila ta share hawayen da yafito daga
idonta sakamakon bugun bakin da baba Rabi
tamata yayi zafi sosai,batace komai ba tajuya
tana guna guni tayi cikin gida
Nan baba Rabi tadago Jamila da har yanzu ta
kasa tashi daga inda Nabila ta barta sannan
tace “Jamila meh ya hadaki fada da Nabila?”
cikin kuka Jamila tace “Ba abinda namata
wlh,muna wasa neh sai kawai tahau kaina ta
fara naushi nah” baba Rabi ta girgiza kai tace
“ki gayamin gaskiya,duk da nasan Nabila
mafad’aciya ce na karshe amma nasan bata
fada sai an nemi tsokanarta,share hawayenki”
nan Jamila ta share hawayenta sai tace “Wai
fah don kawai nace mata ‘yar duma-duma
shine ta dakeni” baba Rabi ta jinjina kai tace “Yi
hak’uri kinji Jamila,tunda kinsan batason sunan
sai kibar kiranta dashi” Jamila ta k’ara share
kwalla tace “Toh baba”. Baba Rabi tayita bata
baki har ta hak’ura ta karkade jikinta tayi
dakinsu.
Haneefah Usman da Maman Khalil
[7:15pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
©ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Baba Rabi tajuya takoma kitchen don k’arasa
ma mai martaba abincinshi.
Abangaren Nabila kuwa tunda tabaro wajen
damben nata tak’i tafiya d’akinsu,d’akin Nene
ta nufa(Nene wata kuyanga ce wacce take
aminiyar baba Rabi acikin gidan sarkin,tana
sayar da kayan yara).
Bayan maghriba baba Rabi tayi d’akin Nene don
suyi hira kamar kullum,tana dosar d’akin taji
muryar Nabila tana ta kyalkyala dariya,tayi
sallama suka amsa mata sannan ta shiga. Tana
zama akan taburma tajuya wajen Nabila ta
mata wani kallo wanda yasa Nabila mik’ewa
bashiri tayi hanyar dak’insu,tana fita Nene tace
“Haba Rabi,mesa zakizo ki koranmin ‘yata
bayan kinzo kin samemu muna hira cikeda
nishadi?” baba Rabi ta furzar da iska tace
“Nene,wlh al’amarin yarinyar nan ya isheni,ni
sam bansan ma ya zanyi da ita ba,fad’an yau
daban na gobe daban” Nene tace “Kiyi hak’uri
Rabi,in ta girma zata bari,yanzu ma don yarinta
neh yake damunta saisa” baba Rabi tace “Toh
dai,Allah yasa hakan amma fah yanzu kamar
abun nata k’ara gaba yakeyi” Nene ta danyi
murmushi tace “Nabilah kenan,zata bari fah”
nan dai suka cigaba da tattauna matsalolinsu
har wajen tara na dare sannan tayima Nene
sallama ta nufi d’akinta.
Tana shiga d’akin taci karo da Nabila tana
zaune akan sallaya tana karatun Qur’ani,saura
kadan dariya ya kubce ma baba Rabi don kuwa
tasan Nabilah tayi hakan neh gudun masifar da
zata mata. Saida ta gama karanta surah din
sannan tarufe Qur’anin ta maidashi mazauninshi
sai ta tsugunna agaban baba Rabi tace
“Umma,don Allah kiyi hak’uri kinji,bazan sake ba
na rantse miki” baba Rabi tayi ma Nabila nasiha
sosai,Nabila ta k’ara bata hak’uri sannan suka
kwanta bacci.
Wacece Nabilah???
Haneefah Usman da Maman K
[7:33pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
©ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Sunanta Nabeelah Musa,’yar Baba Rabi wacce
take matsayin jakadiya a gidan sarki Mu’awiyah
Abubakar,sarkin garin Yura dake Kaduna state.
Sarki Mu’awiyah sarki neh meh matuk’ar adalci
da son talakawanshi,yanada mata daya mai
suna Sarauniya Hafsat wacce yaran gidan da
ma duk ma’aikatan gidan ke kira da
“Yabi”,macece saliha wacce bata muzgunawa
wadanda ke aiki a k’ark’arshinta. Sarki
Mu’awiyah yanada ‘ya’ya biyu kuma dukkansu
maza neh,na farko sunanshi yareema Sultan sai
na biyun kuma Saleem. Sultan bai cika zama a
garin Yura ba sabida yanayin aikinshi,ahalin
yanzu ma yatafi k’aro karatu neh while Saleem
kuma yanzu yana University a China ,akwai
tazaran shekaru kusan 8 tsakanin Sultan da
saleem. Sultan fari neh kyakkyawa,miskili neh
na karshe,saidai inya saba da mutum yana da
fara’a. Saleem on the other hand kuma yanada
surutu ba kadan ba,ko baisan mutum ba
akwaishi da tsokana saisa yawancin mutane
suka fi son maganar Saleem. Sultan yafi Saleem
kyau nesa ba kusa ba
Nabeelah yarinya ce wacce ta tashi a cikin
gidan sarkin Yura,’yar kimanin shekaru
12,tanada d’an jiki sannan kuma batada tsayi
shiyasa yawancin yara suke tsokananta da “‘yar
duma duma”,tanada kyau wanda yananan
daidai don kyaunta irin na boyen nan
neh,batada haske sosai but tanada gashi irin na
fulanin usul,mutane har mamakin rashin
kamanninta da baba Rabi sukeyi,dayake mijin
baba Rabi yarasu kuma yawanci basu sanshi ba
saisa suke tunanin ko kamannin babanta na
fulanin usul ta dauka don bata kama da baba
Rabi ko kadan. Nabeelah tanada tsiwa ba kadan
ba,batada tsoro,duk girman mutum da
matsayinshi inhar ya takulo ta toh fah za aga
rigima,yaran da ke zama agidan duk tsoronta
sukeji don tana jibgarsu ba kadan ba,tanada
surutu sosai.
Aminanta guda biyu neh-Amina da Jamila,suma
yaran masu aiki agidan sarki neh,dayake duk
masu aiki sarki yana basu daki daddaya saisa
yawanci sukazo da ‘ya’yansu mata.
Amina,Jamila da Nabila tare suka taso tun suna
‘yan kanana suke tare saidai fah duk da
sha’kuwar dake tsakaninsu da Nabila bai hanata
jibgarsu,inka shiga fadarsu ma mutum zaiji
kunya saisa iyayen ma basu magana ko sun
dawo da ciwuwwuka,duk fadar da sukayi zuwa
safiya suke ‘kara shiryawa su koma kamar basu
ba.
Wannan kenan
Haneefah Usman da
Maman Khalil
[11:02pm, 06/01/2016] Haneefah :
GIMBIYA NAFEESAH
Na Haneefah Usman
©ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Washegari kamar kullum suka tashi sukayi
sallah sannan suka zauna tilawar Qur’ani har
rana ya fito. Baba Rabi ta tashi tsaye tace
“Yauwa Nabila kije wajen Yabi ki tambayeta ko
akwai abinda zaki kama mata kamin nazo,yanzu
zanje na hada ma mai martaba karin kumallo
neh” Nabila ta amsa da “Toh umma,barinje
yanzu” sannan ta tashi tazo ta wuce ta gefen
baba Rabi,tare suka jera har ‘kofar kitchen din
sannan Nabila tace “Natafi umma” baba Rabi
tayi murmushi tace “Don Allah yaukam karkiyi
dambe da kowa kinji?bakiga kin girma bane?
kuma ma ai manyan mata basu fada” Nabila
tayi dariya tace “kai umma,shine harda wani
cemin don Allah,In Sha Allahu bazanyi dambe
ba” baba Rabi ta ‘kara murmushi tace “kije
toh,Allah yamiki albarka” Nabila ta amsa da
“Ameen” sannan tajuya tayi hanyar sashen
Sarauniya Yabi
Ta isa parlourn tayi sallama,kuyangu da suke ta
kai komo neh suka amsa mata,ta gaishesu
sannan tace “Yabi fah?” d’aya daga cikin
kuyangun mai suna Zuhura tace “Tana daki”.
Girgiza kai kawai tayi saita wucesu zuwa d’akin
Yabi. Da sallamarta ta shiga,suka amsa mata,ta
tsugunna cikeda girmamawa ta gaida Sarauniya
Yabi,Yabi ta amsa mata cikin sakin fuska don
ita harga Allah tanason Nabilah ba kadan
ba,wata rana har tana cewa inama da ‘yarta
neh. Bayan sun gama gaishe gaishen neh Nabila
tace “Ranki ya dade ko da akwai abinda zan
kama miki?baba Rabi tace kiyi ha’kuri yanzu
tana had’ama mai martaba abin karyawa neh”
Yabi tayi wani ‘kayataccen murmushi tace
“bakomai Nabee,kawai dai kije kice mata ta sa a
toya ‘kosai ayima yara sadaka awaje”. Nabila
tace “Toh angama” sannan ta tashi ta isar da
sa’kon Yabi zuwa ga baba Rabi
Haneefah Usman da Maman Khalil
Chapter 1 · 0% Book details