Sashe 9
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni da Yaya Munira mun taso cikin wata irin soyayya da shakuwa. Da wahalar gaske mu yi fad'a sabanin da babu jituwa ko kad'an tsakanin ta da Abida. Koda yake ita Abida da ta kasance k'aramarmu tana da wani irin hali murdadde, bata kaunar ka tab'a mata abinta ko kad'an, hakanan ta yi matukar kyamar ka kwanta mata a gadonta. Duk da dama gado uku ne a cikin dakunanmu na kowanne sashe. Bayan haka kuma tana cikin mata masu high taste bata amfani da kowanne irin garabitin abu, sai zababbe. Y'ar kwalliya ce ta sosai tun tana k'arama. A zahiri mun fita kyau, amma da yake tafi mu gayu sai ta fimu daukar ido. Kusan kullum sai ta sani kuka domin ni tun tasowa ta haka nake sanyi kalau mai matukar raunin zuciya. Yaya Munira ke k'watata a hannunta sanadin da ya ta'azzara rashin shirinsu ke nan. Amma kuma bata yarda a ci zalina a makaranta. Nan da nan Abida zata yi makarbiya ta mayar da fad'an kanta ko da kuwa bata yi mini magana. Kazalika basa shiri da Yaya Sulaiman kwata kwata basa jituwa, a cewarta shi din mai nuna son kai ne da tak'ama, a gabanta yake nunawa nice k'anwarsa alhalin yana ganin yadda Yaya Farouk yake mini alkunya fiye da ita. Shi kuma ya ce ra'ayinta da iyayyinta ne basu yi masa ba, yarinya ta yi ta juya mutane, matuk'ar yana gidan to kuwa sai an musu shari'a don sai ya yi mata abin da zata harzuk'a sai da Baba k'arami karami ya yi masa wuta wuta sannan ya daina fitinarta, don kuwa gaban Baba karami ta kai maganar tana rusa ihun ya mata iyaka da shi ko ta kira masa yan civil defence. Ba k'aramin dariya Baban ya yi ba, karshe ya wanke Sulaiman ya ce "ka fitinar mini Abida fa Sulaiman. Maimakon ka jata jikin ka, har ku k'ulla alheri sai ka dinga yi mata sheganta to ina ruwanka da bak'inta? Ina ce dakin Allah ma bak'ine ashe kuwa bak'i ba muni ba ne ba kuma tawaya ba ce! Ya ce "Na daina Baba amma lallai ka ja kunne ta akan gatsinen da take mini tare da harara ko da ban mata magana ba, sannan duk ranar da ta sake kwashe mini takalma idan na ajiye a bakin k'ofa, komai na yi mata ita ta ja". Baba ya gintse dariyarsa ya ce "Kin ji ko Abida ki daina, shima ba zai kara bata miki ba". Ta ce "Shike nan yanzu dai ka sake jaddada masa ka yi mana iyaka babu ni, babu shi har gaban abada". Baba ya kwashe da dariya ya ce "A a ba haka za'a yi ba, ba dhi ba tsokanar ki bare ya saka ki kuka, kema ba ke ba masa rashin kunya, wannan kam na shata muku layi. Duk wanda ya tsokani wani kuwa to la shakka da ni yake fad'an! Daga haka ya sallame su. Shike nan aka samu saukin rikicinsu. Ni mamakin Yaya Sulaiman nake yi idan ya sako Abida a gaba da wulak'anci don magana ma da kyar yake yin ta baya son hayaniya ko kad'an, yayin da Abida take y'ar kwarfniya ta gaske watakila wannan banbancin ya sake hab'aka yar tsamarsu. Muna kammala firamare aka kaimu Makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori(F G.C Bakori). A lokacin Yaya Munira na aji uku(J.S.3) na k'aramar sakandire a Makarantar. Tare ake yi mana komai. Kayanmu a hade suke, amma Abida bata yarda muci abinci tare. Sai dai kwanonta daban. A shekarar kuma babban wanmu Yaya Asad ya yi aure, ya wuce da amaryarsa Asaba da yake d'an sanda ne mai mukamin ASP a lokacin. Sannu a hankali rayuwa take shudewar har muka sami shiga aji uku. Yaya Munira tana aji biyar. Ta fara zama budurwa sosai. Tsayinmu d'aya da ita saboda ni din doguwa ce sosai. Amma siririya sai da ina da kugu sosai. Haka nan farare ne mu tamkar tsada sabanin Abida da take bak'a. Duk gayunta da farar fatarmu basu rudeta ta yi sha'awar sauya launin fatarta ba. Ko mai zata siya sai ta duba ingredient matukar ta ga sinadarin hydroquinone to kuwa zata ajiye shi. Tsayina da sanyin halina ya sanya dalibai suka lankaya mini Bilki sola. Matukar ka ce Bilki sola a lokacin da muke FGC Bakori kowa ya san ni. Ba ni da k'awaye, daga ta botsara Abida sai kuwa Basma Bello Maska. Kawai Ubangiji ne ya k'ulla abotarmu, don tafi dacewa da Abida, masifaffiya ce ta gaske itama. Kawarmu ce gabad'aya tunda ajinmu d'aya haka dakin kwananmu guda. Amma kawancen yafi k'arfi da ni. Da wahala mu yi fad'a sabanin ita da Abida kullum sai sun yi, wani zubin sai su yi sati basu yi magana ba domin dukkansu masu ra'ayin rukau ne, masu ji da kansu ne. Sannu a hankali Yaya Munira ta kammala ta barmu, ta yi sa'a a shekarar ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahamadu Bello ta Zaria. Kafin mu gama FGC mun zama cikakkun yan mata. Da Basma da Abida matsakaicin tsayi ne da su. Sabanin ni da nake doguwa sosai. Na keresu, a wanccan lokacin har kunyar tsayina nake ji, domin bana jin za'a samu wacce ta fini tsayi a makarantar sai dai mu yi taya. Daga sama ba ni da kiba ko kad'an, amma ina da fad'i ta kasana. Gabad'aya kirar jikina ya fi dacewa da kwalbar coca cola. Doguwar fuska gareni mai dauke da siririn dogon hanci tamkar biro. Hakanan bakina d'an tsut mai dauke da jajayen lebuna, da k'ananun hak'ora jerarru farare kal tamkar kankara. Gashin kaina baki mai sulbi har gaban goshina. Sannan a cike take ga kuma tsayi. Kallo d'aya tak zaka fahimci ni din kyakkwar mace ce lamba d'aya sabanin Basma da Abida da suke da boyayyen kyau, irin sai an kallesu da kyau kafin a fahimci kyaunsu. Mun dawo hutun zango na biyu muka yi sa'a Baba babba ya sahale mana muka tafi katsina hutu gidan Yaya Salaha wacce ma'aikaciya ce a ma'aikatar ruwa ta jihar Katsina. Bana manta ranar da muka fara haduwa. Yammacin wata juma'a bayan Yaya Salaha ta dawo daga aiki, ta aike mu, mu karbo mata sak'o a gidan iyayen mijinta a k'ofar bai. Direban mijinta ya kaimu. A k'ofar muka tarar da samari guda biyu. Tun daga nesa muke hangensu da yake fuskar gidan muke nufa. Su kuma a zaune suke kan tebirin da yake girke a k'ofar gidan. Mun fito zamu shiga gidan, idona ya fad'a cikin na dogon saurayi fari tas. Sumarsa ta tabbatar mini yana da alak'a da mutanan Habasha ko Bafulatanin usul. Faduwar da gabana ya yi, a kallon farko ya sanya ni cikin rud'u. K'afafuwana suka hau sark'ewa, da k'yar na daure na bi Abida a baya muka wuce. Zuciyata na cigaba da dokawa da tsananin gaske. Bamu wani jima ba muka fito. Muka sake tarar da su , mun gota su kad'an, kafin mu shiga mota, suka taso da azama. Wanda yafi tsayin ne ma'ana wanda na kadu da kallonsa ya yi jarumtar ce wa "Sannunku y'an mata". Zuciyata ta sake tsinkewa domin sai na ji tamkar wanda hausar tasa ma ta dabance. Ya zuba mini ido, yana son mini kallon tsanaki, gangar jikina ta taya zuciyata rawa. Na kasa amsa masa sannun da ya yi mana. Abida cikin ko d'ar ta ce "Sannunku dai Rijalu! Dariya ta k'wacewa d'ayan mai duhun fata da kuma matsakaicin tsayi. Cikin dariya ya ce "Bari na matso kusa da ke da alamu ke na dad'e ina jira". Ta rausayar da kai ta ce "A a kada ka matso, domin kuwa shekaruna sha shida, karatu zan yi, kuma na likitanci ka ga ina buk'atar nutsuwa mai yawa akan karatuna". Ya sake fadada murmushi ya ce "Nima dalibin ilimi ne, hutu na zo, ina karatun Islamic law a k'asar Sudan. Sunana Lawal ". Ta ya mutsa fuska ta ce "Idan daga Allah ne zai sake had'amu kamar yadda muka had'u yanzu babu tsammani." Ta shige mota. Yayin da na bi bayanta tamkar kazar da k'wai ya fashewa a ciki. Domin gabadaya saurayin nan ya yi matukar tafiya da zuciyata a kallon farko. Ya biyo ni yana ce wa "Saka mini lambar wayarki, mu dinga gaisawa". Murya babu amo na ce "Bama rik'e waya sai mun kammala makaranta." Ya ce "Sunana Sahal Sulaiman Mashi. Ya ciro takarda a aljihunsa ya rubuta S.S.Mashi tare da lambar wayarsa ya jefo akan cinyata tunda nice a setin da yake. Ya sanyaya murya ya ce ga lambata nan ki k'ira dan Allah da manzonsa." Kafin na ce komai direban ya ja motar mun tafi. Muna nisa da unguwar ina sake jin zakuwa da son cigaba da tattaunawa da shi. Shine saurayin da ya tab'a tunkarata kai tsaye, ba wanda zasu rubuto wasika ba. Shine kuma namijin da zuciyata ta fara bugawa a dalilin sonsa. Domin kallo d'aya na gane shi din matukar kyakkwa ne, sannan dogo ne na gaske. Bayan haka na gan shi cikin kwalliya ta burgewa. Na dauki takardar ina kallon lambobin da ya rubuta su a jere cikin wani irin salo. Ga mamakina sai na ji hatta rubutunsa ya shiga raina ko tantama bana yi yana cikin dalibai masu baiwar sarrafa rubutu babu shakka. Na shagala k'warai da gaske da kallon lambobin. Ba zato kawai Abida ta fizge, bata tsaya wata wata ba ta cukuikuiye ta yaga ta wullar ta window. Na zuba mata ido zuciyata na sake tsananta bugawa. Idona ya ciko da k'walla. Na kasa bude baki na ce mata uffan. Maimakon itama ta kama bakinta sai kawai ta ja tsaki mai tsayi tare da ce wa "Nasan kina iya buga masa waya domin na k'are miki nazari na ga ya shiga ranki. Ni kuwa ban miki sha'awarsa ba, domin idan namiji ya cika kyau had'ari ne babba a wajen mace bare ke solobiyo". Har muka isa gida bakina a dinke ruf, na shige daki na kwanta sai kawai na fashe da kuka ina yinsa k'asa kasa amma na bacin rai ainun. A haka Yaya Salaha da Abida suka tarar da ni, duk k'ok'arina na hadiyen kukan sai da Yaya ta fahimci kuka nake yi sosai. Ta rikice ta dinga tambayar ba'asun kukan, na kasa cewa komai. Abida ta ja tsaki ta ce "Wani tsalelen