← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 33

Sashe 4

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Na kifa kaina a hannun kujerar na yi kuka tamkar hawayen idanuwana zasu kare.
Ina layi na tashi na mayar masa da wayarsa na dauki wayata.
Duk yadda na so na yi nafila na kaiwa Ubangiji damuwata kasawa na yi.
Ba abin da zuciyata take yi irin tafarfasa, tamkar na ciro ta na wanke komai ko na huta da tsananin da nake ciki.
Da k'yar na dinga ambato ya Hayyu ya Kayyum bi rahamatika astagisu.
Na jima kafin na fara samun sassauci. A raina na fahimci manufar shari'a da ta yi togaciyar tsananta bincike kan abin da ake boye maka ko wanda baka san da shi ba. A da zato nake yi wanda ban gasgata ba. A yanzu kuwa na bankadowa kaina damuwa da kunci. Domin zan rayu ne cikin zullimi da zargi.
Na saki gauron numfashi. A fili na furta k'arin aure ba laifi ba ne a wajen namiji mai ra'ayin k'arawa. Sannan Ubangiji da bibbiyu ya ce su fara domin yasan ya haliccesu da son mataye da yawa. Ba kuma zan bijire wa ayar Ubangiji ba ne ta hanyar kin amince wa da k'arin aurensa ba. Zan bijire ne don na tserar da shi tashi da shanyayyen bangare daya ranar alkiyama. Domin yadda na shaida Annabi manzon Allah ne haka na shaida k'arin aure bana maza irinsa ba ne. Ba zai iya adalci ba tabbas.
Har aka k'ira assalatu ban iya tsinana komai ba, sai kuka da sake saken zuciya.
Har ya fito ina zaune ko yunkurin tashi ban yi ba.
Ya k'araso kusa da ni murya babu amo ya ce "Ashe kina nan?"
Bai jira amsawata ba ya fara tafiya yana fad'in sai na dawo.
Na bi bayansa da kallo ba tare da na iya fad'in uffan ba.
Da k'yar na tokara na tashi, na dauro alwallah. Ba k'aramin jarumta na yi ba, kafin na samu hankalina ya daidaita na yi sallar cikin nutsuwa ba.
Gabadaya fuskata ta aune, na yi fiyau da ni.
A yadda nake jina ko ina da darasin da zan bayar da safe ba zan iya halatar makaranta ba.
Sai kuma ya kasance sai karfe 4-6 nake da darasi.
Dan haka ina layi na nufi dakina na kwanta, sabon kuka ya k'wace mini tamkar dai ba kwana na yi ina yi ba.
Da k'yar na yi k'ok'ari hadiye kukan saboda sanin da na yi a ko wanne lokaci yarana na iya shigowa idan basu ganni a kicin ina hidima kamar yadda na saba ba.
Na ja duvet na lullebe jikina.
Ilai kuwa sai ga Amrah ta shigo. Da kulawa sosai ta ce *Mahmah* ba kya jin dad'i ne yau?"
Murya ta babu amo na ce "Kwana na yi da ciwon kai da zazzabi. Na sha magani yanzu shine na kwanta ko zan samu na rintsa."
"Ayyah sorry Mahmah! Allah ya baki lafiya".
A hankali na ce "Ameen. Ki je kicin ki tayasu ku shirya komai, ki kula da Farha".
"To Mahmah". Ta amsa a nutse ta fice ba tare da ta ja k'ofar ba.
Ko minti daya ba'a yi ba, suka dawo dukkansu har Faruk. Suka gaishe ni sannan suka mini sannu.
*Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*
*Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa*
*Malaysianfabricsng*
07020695644.
Chapter 4 · 0% Book details