← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

✍️
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t

*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

15

*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

*Littafi na d'aya ya kammala*
*Masu son cigaban labarin ku biya kudin karatu a kai ku paida group zamu fara kashi na biyu gobe litinin idan Ubangiji ya so*.
*Idan mun fara kuma babu fashi daga ranakun litinin Har juma'a za'a dinga samun update*

*Babu posting a ranakun asabar da lahadi*.

*Ina mik'a Godiya ga wadanda suka siya littafin nan mussaman wadanda suka fara biya tun kafin na fara sakin shafukan kyauta.*
*Na gode sosai Allah ya bar kauna, ya saka muku da alheri*.

*A madadin Ummiel foods*
*Ina tallata muku kulikuli tamkar kilishi*
*Ba ordinary kulikuli bane.*
*Classic kulikuli da ba'a yaro mai k'iwa, ina wadanda aka Hana iyayensu cun nama kuna suke fama da kwadayin?*
*Maza ku garzaya ku siya musu wannan kulikulin da Idan ana cinsa tamkar kilishi ne*.
*An yi Shi cikin tsabta da ta samu nasarar tantanceqa data Nafdac*.
*Ana siyan daya ana bada sari*.
*Akwai a Abuja*
*Akwai a Kano*
*Akwia a Lagos*
*Sannan nation wide delivery ne*.
*Ana samunsa a wasu daga branches din Rufaida Drinks na cikin birnin Kano*.
*Don saka order a tuntubi Ummiel foods a 08036355535*.

"Gabadaya sai nake ganin tamkar kwanakina sun kusa karewa, kawai Baba babba nake ji, if not Indai zan gama lafiya, ai ba ni da wani zullumi domin mutuwa tilas ne komin dadewar da zaka yi a doron kasa kuwa".
Hawaye ya kece mini, na kasa furta kalma ko guda
Bata yi yunkurin hana ni ba, sai dana daina dan kaina sannan ta numfasa ta kaurara murya ta ce "this will be the last time da zan zo gidanki, ki tisa ni gaba kina mini kuka akan aure Maigado. Zan yi aure idan an kaddara mini, zan mutu idan wa'adina ya yi! Abubuwane da duka ba zan tsallake su ba.
Abin da nake so ku fahimta daya ne.
Na yarda sallah wajibi ce, haka nan na yarda azumin Ramadan wajibine, na kuma yarda zakka dole ce idan kana da arziki. Bayan wadannan na yi imani da manzanni, na yi imani da littafin da Ubangiji ya saukar, na kuma yi imani da mala'iku na kuma hakkkake Ubangiji daya ne shine kuma Ubangiji komai da kowa.!
Ta yi shiru tana sake kafe ni da ido yayin da na kasa ce wa uffan.
Ta zarce da ce wa "Amma kin sani, kamar yadda na sani aure ba dole bane, akwai ma wadanda auren yake zama haramun a kansu. Na san kaina, na tabbatar zan iya tsare kaina, dan haka ba zan je na yi gaggawar yin aure da wanda ban nutsu da shi ba. Dan kawai kawayena da kannena sun yi aure ba. Shekaruna ashirin da hudu kacal, a ajinmu nice mafi karancin shekaru, ni da kika ganni ma ina kammala Housemanship din nan ba wai aiki zan tsaya yi ba, zan koma ne na yi specialized a gynecologist. Ko shekaru talatin na haura ba zai zame mini abin aibu ko na kaico ba, matukar ina cikin kamewa.
Idan Allah ya turo wanda ya cancanta sai a yi da shi. Amma ba zan yiwa kaina gaggawa ba. Ku dai da kuka yi auren, ina yi muku fatan alheri."
Na rike hannunta murya babu amo na ce "Allah ya kawo wanda zaki nutsu da shi da gaggawa Abida".
Ta murmusa ta ce "Ameen Maigado. Ke kam dama ai kina cikin sahun matan da suka tsananta a son aure. Ga shi kuma kin yi gam da katar kina zaune lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Duk yarintarsa da nake gani ashe dattijone a zuci".
Na kyalkale da dariya domin kuwa yadda ta yi maganar tana kyaba baki tabbacin har lokacin kallon yaron da bai kai ya aure ni ba take yiwa Baban Amrah.
Da dariyar na ce "Ina son na ce miki sau tari tunaninmu ba ya zama gaskiya. Sai ki ga wanda aka zatawa kyakkyawan zato ya kunyata mutane. Wanda aka munana masa zato ya bada mamaki ta hanyar sauke nauyi daidai da tsarin shari'a."
Ta sake murmusawa wanda yake matukar kara mata kwarjini ta ce "Hakane Maigado. Allah ya taimakemu gabadaya."
Daga haka ta bude jakar hannunta ta fito da glass ta sanya ta sake ciro littafin Tsuntsu duka tsuntsu ne ta hau karatu.
Hakan kuma alamune ta gama maganar ta kuma sallame ni.

Back to story

Hawaye ya goce mini, domin a yau kewar Abida nake yi sosai ina jin tamkar na yi Tsuntsu na ganni a gabanta duk da ta shata mini layi akan ba zata ji damuwata akan lamarin Sahal ba. A yau kam ba wanda nake so na fadawa tozarta ni da ya yi a wajen yarinya kankanuwa irin Abida ko da kuwa zata gwasale ni, ko da ba zan ji kalma mai dadi ba. Kuka na sosai ya kwace mini, na rasa inda zan tsoma raina a fili nake fadin wayyo Mami, wayyo Abida wayyo Yaya Sulaiman wayyo Baba babba. Ni kam Bilki ina ganin jarabawar rayuwa Allah ka taimake ni ka sassauta mini, Ubangiji ka yafewa mahaifiyata."
Ban san kuka nake yi mai sauti sosai ba, sai da Na ji hannun alti a jikina tare rufe mini baki. Da matukar damuwa ta ce "Mahmah sake dauraewa mana, na sani kina cikin yanayin da zaki yi kuka kwarai da gaske. Amma sake sanya jarumta a cikin kasafinki. Duk abin da kike tunanin kin rasa, indai ba imani da lafiya kika rasa to barka, da sannu komai zai dawo miki. Ubangiji baya kunyata mai jin kan bayinsa. Idan tunanin wargajewar gidanku ce ta taso miki, kalle ni mana Hajiya. Duk duniya ba ni da Wanda zan nuna na ce jinina ne ta fuskar nasaba. Kin sani, kin Kuma tabbatar ni yar tsintuwa ce ban san kowa nawa ba, amma a hakan nake rayuwa cikin k'arfin zuciya da karban kaddara.
Chapter 31 · 0% Book details