← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikin nutsuwa da tattali muke rayuwarmu. Babu damuwar komai, sai dai ni duk yadda Ake fadin ango na gajiyar da amarya ta hanyar kusantarta a kai kai da sunan doki ban ga hakan ba.
Don kuwa ina amarya ma ba wani sosai ba, sai mu debi kwanaki bai yi ba, illah iyaka idan zamu kwanta zai rungume ni mu yi barcinmu. Hakanan da rana yana dan rungamata da sumba idan zai fita ko idan ya dawo shima ba wai dole ba.
Tuni muka koma makaranta.
Abida ga dawo tana hostel, duk yadda na so ta dawo mu zauna a gidana ki ta yi tare da gabatar mini da hujjar ba zata taba munafuntar iyayenmu ba . Don kuwa ba zasu yadda ta dawo ta tare mini a gida ba. Dan haka ba zata yi kuma a boye ba.
Ko weekend Ina son ta dinga yi mini amma yar ra'ayin rukau din bata gamsu ba. Asalima sau biyu tak ta zo mini gidan.
Duk da na shafe watanni da auren.
Zuwa lokacin kuma na riga na gane Sahal na cikin jerin maza da basu damu da harkar auratayya sosai ba.
Sai dai kuma yana kokarin ya ga ya gamsar da ni idan har an hadun.
Watanni biyar da aure ya samu aiki da Nigerian airways na lokacin. Sun dauke shi cikin jerin lauyoyin da zasu yiwa kanfanin aiki.
Dan haka ya wadata ni da komai na more rayuwa tun daga kan abinci har tufafi duk da yana ganin na lefe da yawa ban waiwaiyesu ba.
Duk satin duniya zai bar Kano ya taho Zaria.
Ranar jumaa da yamma zai zo sai ya yi sammako ya tafi litinin da asuba.
Duk wannan jelen da yake yi, sau daya tak zai neme ni, ma'ana idan ya zo jumaar nan aka hadu to fa sai wata jumaar. A kasan raina ina son ace had'uwar tafi hakan yawa ko da sau biyu ne sai dai kunya da nauyi sun hana ni magantuwa ko nuna wata alamar ina bukatarsa sama da yadda yake.
Mamakin da nake yi, idan har yana gida to kuwaa kusa da ni daf yake zama koma nace a jikin juna, haka idan ina kicin ina aiki to yana gefe yana taya ni tare kuma da kai hannunsa duk inda yake son tabawa baya damuwa ko ya zama sanadin da zai ja ni dakin, yayin da ni kuma nake tsintar kaina na jike jagab.
Sadda muka kammala aji biyu zamu shiga na uku muka koma Kano da zama, baban Zaria ya yi cukun cukun da na koma jamiar Bayero na shiga aji ukun na cigaba da karatuna a can.
Na yi kewar Abida sosai. Duk ba wani zuwa gidana take yi ba. Amma kullum sai na yi mana girki na tafi mana da shi makaranta.
Ban wani sha wahala a B.U.K ba saboda Basma Maska anan take, k'awancenmu ya sake zama sabo mai cike da aminci da nutsuwa.
A lokacin kuma ina a dauke da ciki na watanni biyar.
Ban nemi komai na rasa ba, komai daidai gwargwadon iyawarsa yana yi mini. Haka na yi goyon ciki, cikin kulawa da tarairaiya don kuwa duk abin da nuna sha'awarsa ya dinga siyowa har sai ya gundure ni.
Cikin marka markan ruwa irin na watan Augusta na haifo kyakkyawar yarinya mai kama da Babanta sak. Murna kamar me domin ina son abu maikyau a rayuwata.
Daga shi har danginsa sun nuna mana gata da kulawa domin kaya har rasa inda zan ajiye su na yi.
Haka nawa dangin suka dinga zarya tsakanin Funtua zuwa Kano.
An kawo mini yayar Mami da suke 'yay'an mata zar wacce jininsu ya jitu. Zata zauna da ni idan an yi suna sai mu koma Funtua tare tunda na yi sa'a cikin hutu haihuwar ta zo.
Ya dade da fada mini idan mace na haifa to sunan maman Zaria(Hajiya Rabi) zai saka domin kuwa ta yi masa alakairai daban daban da ba kowacce mace zata yiwa d'an k'anin mijinta haka ba.
Dan haka tuni an yiwa yarinya huduba da Rabi'a
Na lank'aya mata Amrah wanda Abida ce ta zabo inkiyar.
Ranar da ta zo ganin baby ta kula da yadda nake yawan kallon jinjirar ga shi ko ya ya ta yi kuka zan mika hannu na karbe ta.
Tana ganin inna ta shiga bayi ta ce "Wato Maigado kina da zurfafa soyayya. Soyayyar Babanta ce ta shafe ta kike kasa kawaici, ko kuwa kina cikin iyaye masu tsananta soyayyar 'ya'yansu ta yadda basa iya boyewa a gaban kowa?"
Na yi k'asa da kaina domin kuwa na sani Abida ta na fahimtata tamkar yadda ta fahimci kanta.
Ta numfasa ta ce "ki sassauta, ki danne, na sani dole ki so ta, amma dinga yin kawaici a gaban manya, sannan fa ki sani wannan ba taki ba ce tawa ce, domin dai ni ce zan haifo miki ta ki"
Na murmusa na ce "Abida to yaushe za ki mayar da ni uwa tunda har yanzu k'in ki kula kowa bare ki yi aure na saka ran zaki haifo mini tawa".
Ta murmusa ta ce "lokaci ne ai Bilkisu! Idan Allah ya kawo lokacin sai ki ga an yi ko da ban so ba".
Na tabe baki tabbacin ban gamsu ba. Dan dai ban isa yin musu da ta mai yawa bane yanzun nan zata murde mini.
Tunda na yi aure bata yarda ta kwana a gidana ba sai sanadin haihuwar. Daga Zaria ta taho kai tsaye har aka yi suna tana nan. Bayan suna da kwanaki uku ya kaimu Funtua da kansa tare da uban kayayyakinmu.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t

*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

14
Chapter 28 · 0% Book details