Sashe 8
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Mahaifiyarsu kakarmu ke nan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu.
Dan haka bata yi aure ba sai da suka girma suka zama samari duk da akwai tazarar shekaru biyar tsakanin Baba babba da Baba k'arami. A lokacin da suka girma kuma ta yi aure ta wuce shekarun haihuwa.
Sun taso cikin wata irin soyayya da ririta junanmu don kuwa mahaifiyarsu ta yi matukar cusa soyayya da tausayi a tsakaninsu. Bayan haka kuma sun samu Ilimin addini da na boko.
Baba Babba tsohon ma'aikacin gwamnati ne, haka tsohon d'an majalisar dokokin jihar katsina ne tun a jamhuriya ta biyu. Sannan mashahurin manomi ne dan kuwa sai an sako shi a cikin sahun manoma a k'asa gabad'aya ba wai jihar Katsina kawai ba.
Baba Babba gabjejen attajiri ne da Ubangiji kad'ai yasan yawan arzikin da ya bashi. Dan na yi imani shi da kansa bai san adadin dukiyarsa ba. Ni bansan hekta nawa yake nomawa a shekara ba balle na hakaito.
Idan na ce manomi ina nufin kololuwar manomi ne da yake noman da gaske. Dan kuwa makudan milyoyin kudi yake narkawa a gonaki. Idan kaka'a ta yi kuwa shima ba k'aramin dukiya yake cika dakuna da manyan shaguna ba.
Baba k'arami kuwa likitan dabbobi ne. Shima da nasa arzikin tunda yana kasuwancin siyar da lafiyayyun dabbobi, tunda ga kan awakai, tumakai, dokuna, shanaye da rakuma.
Shiyasa gidan gonar Baba Babba cike take da lafiyayyun dokuna, rakuma da kuma raguna harma da shanaye da tsuntsaye daban daban. Danginsu dawisu da tatalo, jimina, geese, agwagi, da sauransu. Gidan gonar duk fad'in Funtua da kewaye babu ta biyunta. Domin cike take ainun da dukiyar dabbobi, hatta kaji ana zuba sama da dubu ashirin na k'wai da na ci, kajin Hausa ma birjik ne iya ganinka. Tattabarun da suke ciki kuwa baza su kayyadu ba. Gidan gonar Ladi farms ta yi bunkasar da har Madara ake sarrafawa a cikinta domin shanayen waje masu bada Madara zallah ma yawansu ya kai kurewa. Kifaye kuwa ba'a magana. Baba k'arami ke kula da ita a dalilin shi din kwararren likitan dabbobi ne. Samun kulawa da kiwo na mussaman da suke samu ya sanya dabbobin suke ta bunkasa suna haihuwa akai akai. Idan ana lissafin manyan gidajen gona a Nigeria ba wai a Funtua ko arewacin Nigeria ba sai an sako gonar Ladi farms ta Baba babba.
Gidanmu da muke ciki na Funtua tare suka yi ta siyan filayen suka kuma gina abunsu. Kowa zuba kudi yake yi, dan haka mallakinsu ne su biyu.
Bayan haka suna da kadarori daban daban da suka yi tarayya a kai. Misali gadonsu basu raba ba. Sannan akwai wasu kadarori da suke siya tare.
Amma a zahirin gaskiya Baba babba ya fi mahaifinmu dukiya nesa ba kusa ba. Duk da namu mahaifin ma attajiri ne na gaske.
Ina wannan bayanin ne dan ku fahimci labarin da kyau. Iyayenmu biyu hamshakan alhazai ne, sai dai dole wani ya fi wani.
Dukkan iyayenmu maza matayensu guda daya ne.
Haka kuma Ubangiji ya azurtasu da haihuwa sosai. Ya'yan Baba babba guda shida ne. Wacce matarsa Hajiya Saratu ta haifa masa, muna kiranta da Momi.
Ukun farko maza ne Yaya Abubakar, amma Asad ake kiransa, Yaya Umar Faruku, Yaya Usman. Sai Yaya Salaha. Daga kanta an jima sosia kafin a haifi Yaya Munira. Sai Abida da take auta, kuma ita kad'ai na girma duk da dai ba wani fiko ne mai yawa ba, tare aka yi goyonmu.
Sunan mahaifiyata Haj Habiba, muna kiranta da Mami. Mu bakwai ta haifemu. Yaya Sulaiman, Yaya Hamida, sai ni Bilkisu, Ansar, Anisa sai autarmu Saddiqa.
Idan aka had'amu da y'aya'n Baba babba mun zama sha biyar ke nan.
Kusan kowa na da abokin haihuwarsa. Yaya Sulaiman da Yaya Usman. Yaya Hamida da Yaya Salaha.
Daga nan sai abin ya juya.
Gabad'aya mun taso ne bisa jagorancin Baba babba. Domin baba k'arami idan ya tafi Katsina ranar litinin sai alhamis da yamma yake dawowa. Idan ya dawo din ma mafi yawa yafi zama a Ladi farms sai dare ake samunsa.
Gabad'aya mun fi shakuwa da Baba babba, akan mahaifinmu tunda yafi shi haba haba da yara, sannan shi muke ga ni kullum yaumin.
Amma kuma Ya Munira tafi shakuwa da baba k'arami, matuk'ar yana gari to duk inda zaka gan shi tare da Munira a gaban motarsa ta shiga ransa ainun fiye da mu ya'yan cikinsa.
Iyayenmu mata suna zaune lafiya duk da babu abin da suka had'a. Misali ko wacce bangarenta daban sannan akwai tazara mai yawa.
Sai dai dukkan ahalin gidan k'wai da kwarkwata da hadiman gidan ana cin abinci ne daga tukunya guda. Domin akwia sashe guda da na y'an aiki maza masu kula da gyara harabr gidan da shuke shuken gidan, da mata masu girki da gyara cikin gidajen.
Kawai umarni ake basu.
Mu kuwa yaran gidan kowa na da yancin ya zauna a sashin da yake so ko dai na Baba babba ko sashen Baba k'arami.
Idan an fahimce ni bamu taso mun ga banbanci ko wani rikici a tsakanin iyayenmu maza ko mata ba. Shiyasa soyayya ce mai yawa a tsakaninmu gabadaya.
Bamu zama yan mata ba aka yi auren Yaya Salaha da Yaya Zainab da Kuma Yaya Hamida fiko mai yawa suka yi mana, amma da yake sai da suka yi digiri a fannoni daban daban mun data kafin a aurar da su. Amma dai ko sakandire bamu shiga ba, kawai muna ita tuna sadda aka yi auren ne.
Mun taso mu uku Yaya munira da ni da kuma Abida.
*Assalamualaikum barkanmu da lokaci ya hak'uri da ni?*
*Ina gabatar muku da wannan labarin nawa, tare da fatan zaku karbe shi da kyau, zan yi matukar farinciki idan har kun bibiye shi cikin nutsuwa*.
*Ina kuma bada hak'uri ta yadda bana iya tsallake rubuta labarin da yake d'amfare da zumunci wala na jini ko na abota ko kuma na surukunta.*
*Wannan karon labarin harshe biyu gare shi don haka zaku ga ya kasu biyu*
*Haka nan labaran Surayya basa nufin habaici ko shagube ga wani ko wata. Dan haka idan an ci karo da abin da ya yi dai dai da rayuwarki, ko ta waninki ba da niyya bane. Akasi ne kawai*.
*Fatana dai a yi karatun cikin nutsuwa har a fahimci darasin cikin labarin.*
*Surayya Dee*
✍️
[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2347020695644
4
*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.