← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 33

Sashe 5

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amrah ta kadasu suka fice bayan ta rufe k'ofar dakin. Na sani ta kawo sune dan kada barci ya sure ni su tashe ni.
Bai shigo ba sai bakwai da mintina daidai lokacin da muke fara karyawa.
Da kulawa ya ce "A kwance kike, ba ki da lafiya ne?"
Na kasa amsawa domin ji na yi gabad'aya haushinsa ya turnike ni har wuya.
Ya zauna a bakin gadon. Ya tab'a jikina ya ji da zafi, ya ce "Zazzabi ne a jikin ki, amma kin kwanta. Ki tashi ki shirya na ajiye ki a asibiti idan kin kammala sai ki dawo gida ki kwanta."
Na girgiza kai na ce na sha magani yanzu, barci zan yi, nasan zai sauka in sha Allah ".
Ya mik'e ya ce "Allah ya kara lafiya sai na dawo "
Ya saka kai ya fita, ya karya sannan ya fita da yara gabad'ayansu.
Hawaye ya sake silalo mini, ba dan komai ba sai na takaicin yadda na dauki dukkan so da yarda na damkawa Baban Amrah. A haukana na dauka a yanzu ne zan ci moriyar hak'uri da sadaukarwa da na yi. Ashe wanccan tunanin nawa ne ni kad'ai. Domin a yanzu ko bai bude baki ya ce mini ba na burge shi, na yi masa tsufa ba, ayyukansa da yadda yake mu'amalantata ya fahimtar da ni. Na goge hawaye na kalli fanka yadda take wulwulawa da k'arfi. Na saki ajiyar zuciya. Ina sake gane haka alamuran duniyar nan suke jujjuyawa tamkar fitar kibau a jikin mashi.
Na rufe ido ina tariyo abubuwan da suka yi ta faruwa a tsakaninmu da ya kamata na fahimci al'amarin da yake ransa, amma saboda na riga na bashi total submission sai nake dada nausawa tare da zama bagidajiya a kansa.
Dirin wayata ya ankarar da ni, ana kirana, domin na saka ta a vibration ne.
A kasalance na dauka ganin sunan aminiyata kuma y'ar uwata ya sanya na dauka babu b'ata lokaci. Karon farko da na dauki wayarta ba tare da na yi tsaki ba.
A sanyaye na ce "Maman Abdul ya family?"
Ta amsa da ce wa "A kwance kike ne?"
A hankali na ce "Eh bana jin dad'i ne fever da ciwon kai suka taso ni a gaba."
Ta bude murya ta ce "Kuma sun taso ki a gaba, sai kika nade a gado, kika kasa gane kamata ya yi ace kina gaban likita, dan a duba ki a d'ora ki kan magani?"
Na saki ajiyar zuciya na ce "Maman Abdul na sha magani idan bai sauka ba zuwa anjima zan je na ga Dr din".
Ta ja tsaki ta ce "Nan da mintina kad'an zan zo na raka ki, tunda shi ya fice ya barki a kwance."
Na kasa bata amsa domin ba k'aramin aikinta ba ne ta hau zagina tunda tana cikin jerin mutane masu hangulalliyar zuciya. Kazalika bata sassauci akan lamarina da Baban Amrah.
Ilai kuwa sai ji na yi ta yi tsaki ta katse wayar.
Na ajiye wayar na yunkura na zauna da k'yar a dalilin yadda nake jin rashin k'arfin jikina na tsananta.
A hankali na muskuta na sauka na doshi bayi.
Na sakarwa kaina shower. Domin na tabbatar sanyin ruwan zai rage mini dumin da jikina ya had'a.
Na kammala saka undies na zura doguwar rigar batik ta Malaysian Fabrics.
Babu nauyi haka dinkin ma plane ne. Na daura dankwalin. Na feshe rigar da tauraren kaya tunda na fesa na jiki kafin na saka kayan. Na shafawa lebena wet lips.
Na fito da mayafin da ya dace da atamfar. Hakanan takalmi da jakar kalar mayafin ne.
Na makala barima wacce a cikin jakar na dauko.
Na dauki wayata na fita falo.
Na tarar ko ina a gyare. Na leka kicin na tarar da su biyun suna fere doya. Daga k'ofar baya.
Suka hau gaishe ni da yi mini sannu da jiki. Na amsa musu da ce wa na ji sauki.
Na kalli Alawiyya na ce "Ki je ki gyara dakin".
Na dubi Alti wacce ta fita a haife na ce "asibiti zan je. Ki kula da gidan, kada kuma ku je ko ina".
Da ladabi ta ce "Mahmah a dawo lafiya, Allah ya kara sauki".
Na amsa da "ameen na gode "
Har na fara tafiya ta biyo ni ta ce "Mahmah ki dan sha kunu mana. Na dama ya yi kyau."
Na murmusa mata na ce "To zubo mini Alti".
Da murna da rawar jiki ta tafi dauko mug din da nake sha da shi. Ta dauraye sannan ta goge da wankakken kicin towel. Ta ciko shi taf.
Ta tsugunna ta ba ni, na karba na ce "Na gode sosai Alti".
Ina kurban kunun Maman Abdul ta shigo, sanye cikin gown din wani fitinannen material da ya yi matuk'ar yi mata kyau ainun wacce order ce da ba'a samu a koina sai a *Malaysianfabricsng*
07020695644.
Bata zauna ba ta ce "Ta so Malama".
Na kalle ta na ce "Rigimaatu zauna ki sha kunun gyada".
"Na karya already idan mun dawo zan sha."
"To ba ni mintina biyar na kammala Sha". Bata ce komai ba, ta zauna tabbacin zata jira ni din. A hanzarce na shanye.
Na ajiye cup din na mike muka tafi. Su Alawiyya suka biyomu suna mana fatan dawowa lafiya.
Muka gaisa da Baba mai gadi a mutunce muka bude k'ofar k'aramin get muka fita tunda bata shigo da motar ciki ba.
Muna tafe tana tukin ta cikin nutsuwa, ni kuma na yi zurfi a tunanin halin da nake ciki. Ina son na fad'a mata abin da na ga ni a wayar mijina. Ina jin tsoron tention din da zata kara mini. Na riga da na sani ko yanzu aurena ya mutu murna zata yi watak'ila ta had'a da k'warya k'waryar walima. Ba kuma zata yi hakan dan murnar aurena ya mutu na rasa wata daukakar duniya ba. Zata yi ne domin tana ganin zan samu y'ancin zuciyata. da kuma farinciki.
Har muka isa bamu yi maganar da zarta uku ba.
Ba b'ata lokaci muka ga Dr ta rubuta mini magunguna ta kuma gargade ni na k'aranta damuwa domin jinina ya hau sai dai ba sosai ba. Ni kuwa nasan rashin barcin da ban yi ba, da kuma tsananin da na kwana a ciki ya isa ya sababa mini komai.
A hanyar komawarmu ta sassauta fishinta ta ce "Ba zan gaji da fad'a miki ce wa aure is not all about do or die ba ne. Allah da kansa ya yi maganar idan kun fahimci kun kai lokacin da ba kwa burge juna, ko ba kwa son juna ya fad'i yadda al'amarin zai tafi cikin ihisani da kyautatawa. Amma gabad'aya hausawa bama amafanin da wannan nafsin! Sai mu yi ta zama irin wanda babu lada a cikinsa sai zunubi ma. To zunubi mana tunda duk zuciya babu dad'i an koma ana zaman y'aya', ba zaman Allah da Annabi ba. Duk abin da za'a yi ba dan Allah ba, ba zai yi albarka ba.
Y'aya' nawa ne uwayensu suka fad'i suka mutu a wannan duniyar? Sun mutu ne ko sun kasa rayuwa? Bare kuma da ranki da lafiyarki. A lokacin da mijin da ya k'arar miki da kuruciyarki ya gundura da ke, a lokacin kuma Ubangiji zai turo miki wanda shi kuma a hakan yake son ki, yake kaunarki. Bilkisu kin yi hakuri, kin biyayya, kin yi sadaukarwa, kin yi adalci, kin yi komai. Amma fad'a mini what do you have in return?"
Chapter 5 · 0% Book details