Sashe 12
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Abida ta yi caraf ta ce "Yaya Faruku na rantse maka nafi Bilki hankali, green snake ce ita. Da kasan abin da ke zuciyarta da ka fasa yin amaryar da ita."
Na galla mata harara na ce "Yo ni ma tuni na fasa yin da shi, tunda ya riga da ya yi aure har ya haihu ai ya zama cus".
Baba ya yi dariya ya ce "Ai kuwa dai Mai gado tunda bai jira ki ba, ba zai same ki ba".
Cikin barkwanci Yaya Faruku ya kalle ni ya ce "Kada ki bari su ruguza ginina a zuciyarki? Ba kin ce ko matana uku ke ce ta hudu ba?"
A zabure na ce "Da ne Wallahi! Ai garama Yaya Usman da kai, tunda dawowa kawai na yi na ga ka yi aurenka! Ko a fuska baka tab'a nuna kana da wata budurwar ba".
Baba babba ya fashe da dariyar da bai cika yinta ba. Abida kuwa har wani juyi take yi, tana fad'in "Yau an ji kanku da Yaya Faruku" Domin mutumina ne na gaske. A zahiri kuma yake nunawa yafi sona akan Abida. Kafin ya bata abu d'aya ya bani sau biyar. Idan kuwa tare ya siyo mana sai na zaba sannan zai bata wanda na bari, ko kuma ni ya tambayi ra'ayina kafin ya siyo abu, ita kuwa baya tambayarta.
Hakan da yake yi yana dadawa Baba babba da Momi zuciya. Tunda haka siddan Yaya Asad ya tisa ni a gaba ina k'arama a dalilin ba ni da gashi. Ina kuma shan majina sannan shiru shiruna ya yi masa yawa.
Matukar yana falon momi bana iya ko da wucewa ne. An yi anyi ya daina mini muzurai da razana ni, amma fir ya ki, shiyasa na taso da matsanancin tsoronsa. Bama shiri ko kadan Kamar dai yadda Yaya Sulaiman ya tisa Abida a gaba Duk da Shi ba cin zalinta yake yi ba, kushe ya yake tare da gwasaleta.
Sadda muke firamare shine yake kaimu makaranta a mota idan ya zo hutu daga makarantar horar da y'an sanda ta Wudil.
Matukar Baba babba ya ga na bace masa a gidan to Yaya Asad na gari.
Wata rana na shiga wajensu, banbsan dodon ya zo ba, sai ganinsa na yi gurfane gaban Baban yana sanye da kakin yansanda wanda a lokacin bai fi wata da fara aikin ba.
Ina ganinsa na juya zan zura a guje. Yaya Faruku ya yi maza ya ruko ni ya ce "Ke ba abin da zai yi miki."
Yayin da shi kuma ya galla mini harara tare da ce wa "Nutsu ki zauna ko na d'ora miki duniya a kanki ".
Ai kuwa jikina ya hau tsuma domin kakinsa yasa na sake tsorata da shi, hakanan ni da Abida muna matukar tsoron ya d'ora mana duniya.
Wani abu ne da shi mulmulalle mai tsananin nauyi da yake dagawa na motsa jiki, idan ya so mana mugunta sai ya ce sai mun yi kama kama mun matsar da shi gefe wanda bama iyawa ko motsa shi, a haka zamu yi ta yi har sai mun gaji sannan zai ce mu bari.
Baba ya kalle shi ya ce "Ba dan ka yi mata tsufa ba da na baka aurenta na ga yadda zaka yi, ka takura sarauniyar shaiba da yawa Asad."
Yaya Faruku ya yi fit ya ce "Haba Baba a gabana zaka bawa tsoho auren amaryata, ai Bilkisu tawa ce".
Yaya Asad ya ce "ina da shekaru ashirin da bakwai kana da ashirin da biyar menene banbancin namu da zaka jingina mini tsufa?
Ni mai zan yi da wannan y'ar tastitsiyar yarinyar da har yau da ta ke cika shekaru goma bata bar cin tasono ba".
Sanin da na yi ya hana ni cin tasono ya sanya ina rawar murya na ce "Wallahi ban ci ba, ko rannan da Abida ta ga nasa hannuna a hanci na kai baki ba tasono ba ne, amma ta ce sai ta fad'a maka ".
Gabadaya suka saka dariya ban da ni da nake ta zufar fargaba.
Domin wahalar gaske yake ba ni wajen cewa sai na d'ora duniya a kaina.
Baba babba ya ce "Ke rabu da shi kin ji.
Daga shi har Faruku duk sun yi miki tsufa".
Da sauri na ce "A a Baba Yaya Faruku ne"
Suka sake yin dariya, yayin da Yaya Faruku ya yi ihun murna tamkar ba a gaban Baba yake ba. Da alfahari ya ce "ai tuni mun saito ta da Bilki komin tsufana ita ce amaryata".
Na numfasa daga hakaito kuruciyata da ban yi nufin budewa gabad'aya ba, na kalli yadda Abida take murnar gwale Yaya Faruku da na yi, tunda har yau da muka zama y'anmata yafi jana a jikinsa fiye da ita, ko gidansa muka je yafi haba haba da ni, lamarin da yasa matarsa ta washe ni ainun tun ban fahimci inda ta dosa ba har na gane, shiyasa da na yi wayo sai na daina zuwa, domin muddin muka je hutu to fa ba shi ba zama lafiya a gidansa har sai mun bar gidan. A garin Funtua yake zaune, shine kuma yake kula da shige da ficen kudi na Ladi farms, tunda Yaya Asad ya yi nisa yana Kebbi shekaru biyu kenan ya bar Asaba. A lokacin kuma yaransa biyu duk mata.
Yayin da Yaya Faruku yake da yaro namiji.
Na tausashe murya na ce "Har gobe ni ce amaryar Yaya Faruku"
Da yake shi mai haba haba ne yafi dukkan mazan gidanmu wayayyen kai, domin idan ya shiga cikin mata sai ka rantse shima mace ne, idan biki ake yi a gidanmu kuwa cikin su Yaya Salaha yake shiga a yi rawa da shi yana musu liki, gabadaya rayuwar Yaya Faruku abin sha'awa ce, baya da damuwa, ba shi da tsanani ga shi dan gaye na sosai kuma fari irin wanda nake so. Amma Yaya Asad ga bak'i, ga shi mummuna, duk da dai Abida ta ce nice nake ganin muninsa tunda na rufe zuciyata a kansa, ni kuwa bana yarda da maganarta duk da ban tab'a tsayawa na masa kallo sau biyu ba, amma nasan dogo ne mai murdadden jiki tunda ma'abocin motsa jiki ne ainun tun tasowarsa. Tabbas sifarsa ta dace da jami'in tsaro.
Ya yi tafi ya ce "Ni nasan duk yadda ake kushe ni nasan sarauniyar shaiba tawace".
Baba ya sake murmusawa, yayin da Abida ta yi gum alamun bata da tace wa.
Tamkar jifa sai gani muka yi mai gadi na bude tangamemen get din gidan.
Moto kirar pegoeat ta shigo, sai kuma wata irin ta y'ansanda mai dauke da logon y'ansandan k'asa reshen jihar Kebbi.
Motocin na tsayawa wani ya yi saurin fitowa ya bude k'ofar Yaya Asad ya fito da alamu shine jagorar tafiyar gabad'aya.
Yana fitowa suka fito da azama.
Shi kuwa ya durfafi Baba babba kai tsaye.
Yana zuwa gabansa ya cire hular kansa ya kame tare da sarawa Baban wanda hakan shine kololuwar gaisuwar girma a gidan jami'an tsaro.