← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya numfasa bayan ya janye hannunsa. Ya ce "Ashe kun sake hadewa da yaron da autar momi ta ce ƙiris ya rage ya shiga sahun zabiya".
Na kasa amsawa domin nasan babu labarin da yafi wannan tashe a cikin jaridar Abida.
Murya babu amo ya ce "Wai har iyayensu sun zo wajen baba babba?".
Na ɗaga masa kai dan ya gane tabbas zancen da ya ji a wajenta gaskiyar lamari ne.
Murya babu amo ya ce "Anya baki yi rushing ba kuwa Maigado?
Kina kallon kan ki a madubi kuwa? Ke fa gaba ɗaya ba'a miki zubin da ƙananun maza zasu same ki ba. Kin fi dacewa da zaratan maza musamman na jami'an tsaro".
Na kiɗeme ainun domin na kasa gane shima son nawa yake yi ne ko kuwa? Ni kuwa me zan yi da shi? Ban so yaya Usman ba a matsayin saurayi, sai shi? A ture ma yaya Faruku bai zama serious da maganarmu ba, amma kaf ya'yan baba babba shi kaɗai zan iya yin haƙuri na karbe shi a matsayin mijin aure ba dan komai ba sai dan tarin alherinsa da sadaukarwarsa, sannan ina jin zuciyata tana bugawa akansa. Ban da shi kuwa ban ga wanda zan iya yiwa alkunya ba a cikinsu, domin na tsani auren zumunci har zuciyata. Bare yaya Asad kwata kwata bai mini a matsayin mijin aure ba. Ya mini baƙi da yawa, ba shi da kyawu irin wanda nake so, sannan ƙarfinsa ya yi mini yawa, a lokacin sai nake ganin kuskure kaɗan zan yi masa ya targaɗa ni. Bare kuma ga matarsa da ta fini ilimi da gogewar rayuwa dan kuwa da kaɗan ya girme mata shekarar da suka yi aure ta kammala digirinta na farko a jami'ar Maiduguri. Yayin da shi kuma a lokacin shekararsa ɗaya da kammalawa.

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*
*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*
*08163761797*
Da suka yi aure ta yi digirinta na biyu a Ɗanfodiyo University Sokoto a lokacin yana aiki a Kebbi. Dan haka ya ajiyeta a Sokoto yake jele tsakanin Kebbi da Sokoto.
Yanzu kuma ƴaƴansu uku tana shirin dire masa na hudu. Waya kai ni cusa kaina a tsakaninsu ta riga da ta fini wayewa da dabara, shi ɗin ma kamar a hannunta yake.
Ganin na kiɗima ainun da furucinsa, watakila kuma ya hango ban taɓa tunanin zai iya ƙulla wata alaƙa ta daban da ni ba, sai ya yi maza ya ce "Wani abokinane matarsa ta rasu watanni uku shine ya ganki ya ce yana son ki, mutumin kirki ne yaransu huɗu suma".
Yana rufe baki na ce "Abokinka fa! Tabdi gaskiya he is too big for me. Ka bashi haƙuri kawai!
Na faɗa bayan na tsuke fuskata ainun .
A tausashe ya ce "Ai na bashi haƙuri tunda na samu labarin kin bada damar da aka je gaisuwa wajen baba babba ai magana ta ƙare".
Jin haka na ɗan saki fuska kaɗan.
Sai kuma ya ce "Amma shi kuma ya ce "Tunda ba ƙudin aure aka kai ba, ba kuma auren aka ɗaura miki ba, zai jarraba sa'arsa domin kin shiga zuciyarsa kin yi kane kane".
Yana rufe baki na ce "Wallahi ka ba shi haƙuri dan kuwa ba zan yarda na saurarere shi ba, tsoho da shi zai ce yana sona?"
Jikinsa ya yi sanyi ya ce "Shi ke nan zan ba shi haƙuri tunda na gane da gaske ba zai ci albarkacina ba. Dama gani na yi mutumin kirki ne, kuma zai yi miki adalci.
Wasa ma nake yi miki matarsa da ranta kawai tana Kano tana karatu ne, shi kuma so yake ya samu wacce zata zauna da shi a Kaduna."
Na ce "Ya bincika a wani wajen ka ga nima ai karatu nake yi a Zaria. Ko kuma ga Abida nan ko zasu shirya".
Da sauri ya ce "Ya ga Abidan amma bai nuna ita ba, dama kuma mai irin yanayinki yake so marar hatsaniya, wacce zata ɗauke kai game da sha'anin yara da matarsa."
Na yi kamar na ce "To ba zai samu ba indai sai ni, amma kwarjininsa ya sanya na kame bakina. Amma raina ya ɓaci akan me ba zai ba shi Abida ba sai ni zai liƙawa sa'ansa mai ya'ya da kuma matar da bata iya sarrafuwa. Domin da ya isa da ita ai da ta bar karatun ta zauna da shi, ko ta yi karatun a Kad poly. Ya miƙe tare da sakin ajiyar zuciya ya ce "Na gode Maigado, na gode da girki, yanzu me kike so na baki dan ki san na yaba da karamcinki?"
Na yi murmushi na ce "I need nothing, amma na roƙeka?"
Da sauri ya ce"Ina jin ki?"
"Ka daina ce mini Maigado. Su Baba kaɗai ke faɗa mini, yanzu tunda ka fara faɗa mini Abida da sauran jama'a sun ɗauka".
Ya murmusa ya ce "Ina takaicin sanar miki kin roƙi abun da bazan iya yi miki ba. Domin ina matuƙa jin dad'i idan na ce miki sarauniyar shaibah ko Maigado. Kinsan kuwa duk Bilki ai mai gadon zinari ce."
Na tsuke fuskata na ce "Ni kam bana so, yanzun nan mutanen gidanmu zasu riƙe su bar Bilkin".
"To ki dinga rubuta sunan duk wanda ya ƙira ki da Maigado idan na zo ki faɗa mini, zan yi miki maganinsa ko waye."
Na ce "Ba zaka daina ba ke nan yaya Asad?"
Kai tsaye ya ce "Ina jin daɗin sunan ne, sannan kuma ban iya yaudara ba, tunda bazan iya dainawa ba".
Ya fita waje ya dauko bandir ɗin 500 a motarsa ya ajiye mini akan cinyata, ya ce ki ajiye idan kin koma gida ki siyi abin da kike so, na gode sosai sarauniyar shaibah"
Ya wuce wajensa ba tare da ya sake ce wa uffan ba.
Na kashe kayan kallon na hau tashin Abida.
Abin mamaki ban wani sha wahalar tashinta ba. Mamakin da na yi ita ɗin mai nauyin barci ce, hakanan mai wahalar tashi ce a barci.
Kwanaki biyu Anty Maryam ta haihu still dai mace.
Hidima sosai maigidan ya yi, cikin farin ciki.
Gaba-daya Aysha babbar ɗiyarsu shekarunta takwas, amma an mata ƙanne hudu, shiyasa a jere suke fikon ƙadan kaɗan ne a tsakaninsu. Khadija a ce ta biyu, sai Saudat ta rasu bayan an haifi Hafsat, sai kuma Hafsat da ita aka yaye akan dole.
Duk inda na yi Hafcy nan take yi, hatta da mamanta ta tafi asibiti haihuwa a wajena ta kwana.
Ba kuma ta yi mini rikici ba duk kuwa da yadda take da maƙon uwa.
Kwana da yini kawai ta yi, aka sallamosu bayan an tantance lafiyarta da ta jinjira. Kusan ni ke hidimar gidan, yaya Munirah tana taya ni da shara ne da moping, amma girki da kula da yaran duk ni nake yi, wani zubin ta kan yi wanke wanke. Abida kuwa kullum a naɗe take wai bata da lafiya, sai dai kuma jinyar bata hanata cin abinci da wanka da kuma nazari a mujalloli da littafai daban daban.
Ganin hakan da masu gidan suka yi ya sanya suka raɗawa ɗiyarsu Bilkisu. Ranar da ya faɗa mana sunan diyar kenan Abida wiwi ta rushe masa da kuka hannuwa a ka, tana ce wa "Yaya Asad haka zaka yi mini, lillahi wa Rusulihi ai kowa yasan ba shiri kake yi da ita ba. Ni ce taka ita kuma ta yaya Faruku sai kuma ka tashi kasa sunanta alhalin ni yafi cancanta ka saka. Wanne iri kunyata ni ka yi haka?"
Da rarrashi ya ce "Kwantar da hankalinki autar momi! Ba matar Usman an ce ta kusa haihuwa ba, to ki ji a ranki matuƙar mace ta haifa to sunanta Maryam-Abida."
Ta sassauta kukan ta ce "Ni dai na fi so kai ka yi mini".
Ya ce "zan yi miki matukar ina raye. Sannan zan saka miki ma a gidan Usman a kusa, sai dai idan ba mace aka haifa ba.
Ta sassauta kukan, duk da so ta yi a canjawa yariyar ta amsa Abida. Yayin da Yaya Munirah ta saki gauron numfashi ta ce "Allah ya bani haƙuri!
Ya yi gajeriyar dariya tare da faɗin "Ke ai yayarsu ce Munee".
A kuɗin da ya bani na ƙirgi dubu ashirin na bashi na ce ya siyo ragon suna, sauran ya yi hidimar sunan Bilkisu. A lokacin ragon dubu goma na bada labari ne.
Ya karba da murmushi ya ce "Lallai kin iya karrama takwara sarauniyar shaibah!
Na sake ɗaukan dubu biyar na kaiwa Anti Maryam na ce idan ta fita ta siyowa little Bily ɗankunnen gold.
Chapter 20 · 0% Book details