← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 33

Sashe 21

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murna da godiyar da ta yi ya sanya na gane ta iya mu'amala da mutane. Na sani tafi ƙarfin abin, sannan na tabbatar ɗan kunnen gold za'a siyo a sanya mata, tunda dukkan ya'yan uku ko wacce zagayayyen ɗan kunnen gold ne a kunneta.
Da matuƙar murna ta ce"Ai kuwa gobe zan fita da kudin nan zan siyo mata Bilki".
Tana mini godiya, nima, ina yi mata godiyar, domin na tabbatar da bata yarda ba, ba zai soma saka ma sunan nawa ba.
Cikin dare Abida ta tashe ni. Ta zuba mini ido ta ce "Bilkisu a ina kika samu kudaden da kike ta wadaƙa da su haka ne?
Nima na zuba mata nawa idanuwan na ce "satowa na yi Abida" Na bata amsa a kufule domin na gaji da abubuwan da take yi mini, tunda aka ce sunana aka sawa jinjira. Bayan haka kuma, na fara ƙosawa da yadda take yawan haiƙe mini tamkar dai itace gaba da ni.
Ta jijjga kai ta ce "Na rantse zaki san kin mini gatse. Ai na riga na gane shima sonki yake yi, duk hirar da kuka yi rannan da daddare idona biyu bakam na yi, duk ɓare ɓaren da kika yi na girki, da yadda ya kaikaice yake faɗin abokinsa na sonki duk na ji, kin sani, nima na sani ba wanda ya aiko shi, kansa yake ƙwanƙwasawa ƙofa. Na rantse gari na wayewa zaku ga tsiya sai na tsarawa matarsa komai na ga yadda za'a yi ta cigaba da yarda da ke, shima kuma na ga ƙarshen juya mini baya. Muna komawa gida kuwa zan siyarwa Baba ƙarami da yaya Faruku wannan labarin domin shine shafin farko kuma mafi tsada a jaridata."
Jikina ya yi sanyi sosai. A raunane na ce "Kada ki yi mini haka Abida! Kin ga haka matar yaya Faruku ta tsane ni, ki taimake ni, mu bar garin nan lafiya, ina kuma roƙon ki kada ki saka baba ƙarami a maganar nan kinsan dai yarda zai yi, alhalin kuma na turawa baba babba wanda nake so."
Ta ja tsaki mai tsananin gaske ta yi kwanciyarta bayan ta juya mini baya. Hakan da ta yi mini tabbacin ne na ba zata sake yin magana ba, domin haka ka'idarta take matuƙar ta kwanta ta juya baya to ta gama.
Kan dole na kwanta nima. Amma na shafe awanni barci bai sure ni ba.
Washegari na dinga yi mata shisshigi da azarbabin ta kula ni, ita kuma tana yauki gami da cin magani tare da muzuran yau ƙwai zai fashe. Idan ta ce zata fasa ƙwai din nan sai na ji cikina ya yamutse.
Kai Abida ta mini iyashege iyaka. Ban da rashin wayona ai da na barta ta fasa ƙwan tunda dai da ɗan uwanta zai tashi, kuma ma ai bata da garantin son nawa yake yi. Amma gabaɗaya ta kiɗima ni. Ta firgita ni, ganin na matsu ta huce ya sanya ta ce sai dai na sayi gatsen da na yi mata.
Jiki na rawa na zaro dubu biyu na ajiye a gabanta. Ta dauka tana juya su.
Tsawon lokaci ina dakon mai zata ce, sai da gama ja mini rai sannan ta ce "saura wata dubun dan ba zai yiwu na sarayar da wannan labarin cin amanar a dubu biyu ba. Ki dinga soyayya da mijinta a cikin gidanta ita kuma ta dauki dukkan yarda ta zuba miki. Komai Bilki, Bilki dai, gara na taimake ta na faɗa mata yadda kuke son nukurkusa ta da baƙin ciki."
Ban ce komai ba, na sake zaro dari biyar biyu na ajiye mata. Ta haɗesu waje guda ta buɗe tsakiyar Mujallarta ta zubasu.
A tsume ta ce "Shike nan ba zan faɗa mata ba. Amma ki tabbatar idan kika janye biyayyar da kike yi mini zan faɗa ne kawai, ki cigaba da kawo mini abincina d'aki."
Dad'i ya ratsa ni na ce "To Abida ƙanwar Bilki na gode!
Daidai lokacin yaya Munirah ta fito daga banɗaki da yake cikin ɗakin.
Ta ja tsaki ta ce "Bilki ki rabu ita da mana sai wahalar da ke take ta yi, komai zata yi, ki barta ta yi ɗin ai dai ba za'a kashe ki ba, sai gana miki azaba take yi ke kuma kina ta bin kanta."
Da azama na ce "a a yaya Munirah ai mun ma saito ta."
Yayin da Abida ta ja tsaki ta ce "To ta zuga ki kwabarki ta yi ruwa.".

Bojuwa herbs*
*Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?*
*Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?*
*Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?*

*Muna dafa ciccibin da yake ciki da mace, yake kyautata matuncin mace komin tsufanta*
*Kazalika muna sayar da saiwowin dahuwar idan ke kike so ki dafa da kanki*
*Muna dafa kazar sababi gangariya,mai saukar da niima da kuma hade mace*
*Akwia kuma saiwowin dahuwar idan zaki dafa da kanki*.

*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida maijego*
*Bazawara package*

*Man ayun Chad da Marwa Wanda Babu algus, zumar silki kola*
*Hakkkn daka emergency na mussaman*

*Tightening set*

*Kudai ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin aminci da rahusa, bana siyar da abin da bashi da inganci*
*A Dade ana yi sai gaskiya*
*08032773332 what'sapp only*

✍️
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

10
*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750
Chapter 21 · 0% Book details