← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 33

Sashe 6

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fara kuka sosai. Ta gangara gefe ta ce "Bude baki ki mini magana Bilki. Kin sani bazan yad'a sirrinki ba, na damu da ke tamkar ko ma fiye da kaina. Kalle ni, ni ce ta ki BBM ".
Hawaye na zuba murya na rawa na kalle ta na ce "Baban Amrah ne, soyayya yake yi da k'ananun yan mata wadanda basu bawa Amra shekaru biyu ba!
Kuka mai nauyin gaske ya kece mini.
Amma ita bata ka'du ba. Sai ma ce wa ta yi "soyayyar da yake yi da y'an mata ya kamata ki saka a ranki, ko kuwa kamata ya yi ki gane irin kuskuren da kika rayu a kai, ki yi d'amarar gyarawa?
Bilki ba fa zan rufe ki ba, domin ni da ke bamu hadu dan munafunci ba. Dan haka bazan yaudare ki ba, tamkar yadda bazan yaudari kaina ba.
A halin yanzu mijinki zai bukaci yarinya k'arama. Domin shi a yanzu yake kan ganiyarsa. Kinsan kuma na tab'a fad'a miki da jimawa har muka samu sabani akan hakan.
Ni yanzu ba soyayyar da yake ba ne cikas ba. Yadda kike ragaita a hannunsa ne tashin hankalina. Bilki kina da zafafa soyayya. Anya kina yawan tuna hadisin Annabi da ya ce mu takaita soyayya da k'iyayya domin komai na iya juyawa. Ma'ana masoyi kan rikide ya koma makiyi. Haka nan makiyi kan rikide ya koma masoyi.
Menene something precious a tare da Baban Amrah da kika zama haka ne?"
Na kalle ta ina son na fahimce ta da kyau. So take na kashe aurena ko kuwa? Duk abin da nake yi ina da damar da zan yi ne. Allah ya yassare mini. Na yi k'asa da kaina domin na hakkake ba ingiza mai kantu zata yi mini akan halin da nake ciki ba. Tun fil-azal take adawa da yadda nake gudanar da rayuwar aurena.
Ta rayu tana kaicon yadda komai ya cukurkude mini.
Na nisa na ce "Ba yadda kike zato ba ne. Kin ringa kin sani ban dauki abin duniya da muhimmanci ba. Dan haka duk abin da nake yi a gidana ban tab'a jin kaicon yinsa ba. Na fi son soyayya fiye da kudi. Na fi son a ririta ni, fiye da a ajiye mini komai babu kulawa. Na fi bukatar kulawar miji sama da na tara abubuwan kyalekyale."
Ta numfasa ta ce "Yanzu fad'a mini kin samu yadda kike so din ne? Kusan asara biyu kika yi Bilki. Ke baki yi tattali kin mori karatunki da aikinki da kike yi babu hutu ba. Sannan kuma baki samu yadda kike so a wajen mijin da kika d'ora dukkan fatanki a kansa ba. Tun farko na fad'a miki kada ki bada k'ofar da zaku yi joint pocket. Amma kika k'i."
Cikin kuka na ce "Yanzu "Maman Abdul ina da kudi sai na bar mijina yana ragaita? Ina da hali sai na bari mu zauna da yunwa! Ina da dama sai na bari mu zauna a gidan haya, ko kuwa na zuba ido a dinga ganin y'aya'na kamar almajirai saboda rashin sutura da kyakkwar makaranta?"
Idonta ya ciko da k'walla. Ta yi dabarar daukesu ta ce "Ba ina nufin haka ba. So nake ki gane ba kowa ne yasan alheri ba. Yanzu fad'a mini da kika yi hakan kin samu abin da kike so? Har yau baki samu ba. Ni da na bar mijina da hidimar gidansa na fiki samun kulawa, na fiki nutsuwa, na kuma fiki gamsuwa da kokarin miji. Ban tab'a yarda na yi abin da nasan ba hakkina ba ne. Na yarda zan yiwa kaina irin suturar da ta dace da ni ko da shi ba zai mini ba. Zan siyawa y'aya'na suturar da nake son ganinsu a ciki, mussaman idan zan je taro da su.
Haka nan idan ta tura ta kai bango zan shiga cikin tallafin karatunsu domin idan na ginasu kaina na yiwa sabida na yi amanna y'aya' mallaki uwa ne. Ko ina nake a duniya zasu nemi ne ba kuma zasu canja ni da wata ba. Sai kuwa magani idan ba ni da lafiya ko su. Sai kuma na tabbatar miji ba shi da sukunin yin wannan hidimar. Idan kika cire wadannan ba abin da zan yarda na daukewa miji, komin kashin abin da yake da shi sai ya kawo ya bamu tunda shari'a ma bata dauke masa ba."
Ta nisa ta cigaba da ce wa "Mafi yawa fa mazan yau da zarar suka ga kana tausaya musu kana sana'a kana hidima a gidan wai maimakon su karfafa ka, su yaba maka, sai su dinga sakar maka ragamar rik'e gidan a hankali. Kafin a ankara sai su bar maka kaso takwas na rik'e gidan gabadaya. Ranar da baka yi ba kuwa sai ya zama ka yi zunubin da zasu juya maka baya ko ma su sallame ka. Kuma akan idonka zasu yi aure su dinga yiwa d'ayar matar hidima da dukkan iyawarsu. Da zaka yi magana sai a taru ace kishi kake yi, da ai baka yi k'orafin ya barka da wahala ba sai yanzu.
Shi kuwa gogan ko d'ar ba zai ji ba zai ce "Ai ita yarinya ce, yaro kuwa bai san babu ba, ke ma lokacin da kike kamarta ai ba abin da bai miki ba. Dole ki hak'ura idan kina son zama da shi, rikicewarki kuwa na iya sawa ya sallama ki ya cigaba da zama da matarsa ba tare da tunanin kun tara yara ba."
Na kalle ta na ce "Na gane na kuma san gaskiya kike fad'a mini wacce babu son kai a cikinta."
Ta ruk'o hannuna ta ce "Ki fara nazarin yadda za ki gyara kuskurenki. A yanzu yana da halin da zai rik'e gidansa Bilkisu. Dan haka ki zame ki bar shi ya dauki nauyin da Allah da kansa ya wajaba masa. Idan ba shi da hanyar samun kudi ta yaya zai fara tunanin k'arin aure, ko kuwa itama ke zai aurowa ki cigaba da rik'e masa ita?"
Na kalle ta a matukar kidime na ce "Sai ka ce na zama sauna Basma?"
Da rauni ta ce "Ai kuwa shasha ma ya mayar da ke ba sauna ba Maman Amrah! Muka yi shiru a dalilin na kasa magana, gabadaya kaina ya kulle. Ina ta tunanin fad'i tashin da na dinga yi a baya amma gabadaya ban ga ribar hakan ba.
Na fesar da ajiyar zuciya na ce "Zan gyara abin da zan iya gyarawa Basma. Amma ba duka ba. Domin kinsan idan ina son abu to ina sonsa ne da dukkan zuciyata. Ba abin da zan mallaka da zan yi masa iyaka da shi. Allahu yana kallona yana kuma kallon zuciyata. Idan abin da nake yi saboda shi ne to da sannu zai kawo mini mafita, na yi imani zan ga alheri ko da kuwa ba nan duniya ba ne. Abu d'aya na kudire idan har ya yi aure a wannan halin da muke ciki to tabbas shine tikatin sakina. Domin hakan da zan yi shine cikakkiyar soyayya tunda zan tsallakar da shi fad'awa halaka ne. Baban Amrah ba zai iya ba, na yi imani ba zai iya ba. Zan yi kokarin na danne komai domin ina son shi, ina son na rayu da shi, ina tausayinsa da y'aya'nsa. Amma idan har ya zabi wata saboda ni, to zan kauce na bashi waje domin ba zan hana shi abin da Allah ya ba shi dama ba.
Da ace shi din jarumi ne, na tabbatar zai iya rik'e mata biyu cikin mutunci da adalci, da zan danne komai na jagoranci k'arin aurensa na bashi dukkan gudunmawar da ta dace tunda ga kan kudi har zuwa samar masa da kwanciyar hankali. Son da nake masa ba zai ba ni kuzarin da zan hana shi morewa rayuwarsa ba. To akasin da aka samu shi ba jarumin ba ne ta ko wacce fuska. Ni kuma bazan yarda na yi hakurin da babu lada sai cutarwa a cikinsa gabad'aya ba."
Wata irin salama da annuri ya sauka a dukkan jiki da fuskar Basma. Ta ce "Na ji dad'i Bilkisu! Na gode miki, na kuma fahimce ki a yau k'warai da gaske. Zan fara yi miki addu'ar Allah ya mayar da shi irin yadda muke son ganinsa, daga yau na daina fatan ki bar shi, zan kuma tsaya miki har ki tsallake dukkan kalubalen da kike fuskanta a rayuwarki".
Hawaye ya tsinke mini da rawar murya na ce "Na ji dad'i da kika fahimci sonsa kaddara ta ne ba wai ni ce na makale akan dole ba. Babu abu mai azabtarwa irin so. Mussaman son da ake yinsa babu dalili. Domin idan duniya zata hadu ana son fahimtar da kai had'arin da kake ciki ba zaka gane ba. Illah sake nausawa jeji tare da k'ullatar mutane da kuma ƙalubalantarsu.

*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntube ta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
#+2349162662750.

Surayya Halin yau
✍️
[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2347020695644
3
*MalaysianFabrics*
*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*
*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*
*7020695644.*
Chapter 6 · 0% Book details