Sashe 14
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Dan Allah Ki zo mi saka order din ciccibin garari ko kazar sababi Ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
Yaya Asad ya ce "Ni ne zan kai ku? Shekara da shekaru wa yake kai ku?"
Ni dai da ba wani sakewa da shi na yi ba, ban ce kanzil ba. Yaya Faruku ya ce "Baba ne ya ce "Ba zai ba ni motarsa na tuka ba, wacce kuma aka yi nufin kaisu a ciki ta k'i tashi.
Shine ya ce kai kad'ai zai iya bawa motarsa. Sai kuma Allah ya kawo ka babu zato ba sai ka kai su ba ".
Nan da nan ya ce hakkun ya aki Umar. To marabci wadannan da na zo da su."
Cikin girmamawa ya karbi mukkullin mota a hannun Baba babba. Shi da Yaya Faruku suka kwashe kayanmu suka dawo da shi motar da za'a yi tafiyar da ita bayan ya dakatar da tawagarsa da suka yi nufin kwashewa tare da ce wa "Wannan hidimar ta mahaifina ne dan haka ni yafi cancantar na yi da kaina".
Ni na shiga gaban motar a dalilin yadda nasan Abida owners coner ne wajen zamanta tana matukar son ta zauna a wannan gefen ana janta, ita kuma ta hakimce bayan ta sanya glass ta hau duba mujallar Tambari ta ado da kwalliya ko littafin Hausa.
Ni mamakin yadda take daukar ta d'aya nake yi. Domin yana wahalar gaske ka ga Abida ta yi karatun da ya shafi na boko, matukar zaka ganta a nutse tana karatun cikin nutsuwa to kuwa littafan Hausa ne ko mujallar ado da kwalliya ko kuma na girke girke.
Amma karatun boko a gajarce take yinsa. Daga k'arshe sai na gano tana cikin jerin dalibai da ake kira student with high I.Q. Tana da tsanin hazakar da ta kerewa dukkan y'aya' matan gidanmu. A maza kuwa da Yaya Asad da Ansar k'anina zasu fafata.
Ni kam average ce, ba ni da hazaka sai naci, nacin ma na dole ne, domin hidima iri d'aya ake yi mana, amma kullum ta kawo sakamako mafi daraja wato 1st position, ni kuma na dinga kawo babu yabo, babu fallasa. Kishin haka ya saka nake nacin karatu tare da bita har na samu nake kawo sakamako mai kyau domin bana wuce tsakanin 5-9.
A duk sadda zamu tafi a hanya sosai muke hira da Yaya Faruku ya yi ta zolayarmu tare da sakamu dariya ta hanyayoyi da dama har ya ribacemu mu manta fargabar komawa makaranta.
Amma a wannan tafiyar tsit kake ji hatta Abida da ba wani shayinsa take ji ba, baka jin bakinta, a karshe ma sai ta ciro da littafin Tsuntsu duka Tsuntsune na marigayi Malam Abubakar Imam ta hau nazarinsa, domin ta ce ba karatu take yi kawai a littafin ba, har da nazarin yadda zata samu azanci.
Mun fara nisa amma gabadaya a takure nake zaune. Wani irin abu ya mamaye ni na rashin sabo da zullumi, na dinga jin tamkar na ce ya dakata na koma baya.
Na dinga mutsu mutsun rashin sukuni.
Ya kalle ni ta madubi ya ce "Ina fatan yadda kika zama tsaleliyar budurwa no more cin tasono".
Na yi k'asa da kaina cikin jin kunya k'warai da gaske.
Abida ta yi gajeriyar dariya ta ce "Ta daina cinsa amma kasan farce take ci duk girman nan nata ".
Ya ce ",Wonderful! From Shan majina, to cin tasono, to cin farce, sannu mai sabbin update". Abida ta fashe da dariyar iyashege tare da ce wa "Bak'in ciki kamar na sume idan muna tafe tana fama cusa yatsu a baki, gabad'aya sola ya danne zahirin sunanta. Ya murmusa ya ce "Wai ke autar Momi waye babba a tsakaninku ne? Na ga fa kin rainata da yawa".
Ta ce "Ai ita ce gabad'aya wata iri ce, ba wadanda yasan wacece Bilki sai Allah sai ni".
Ya share Abida ya juyo gare ni tare da ce wa "To ki bude kunnen ki da kyau. Ba hadisi ba ne, amma maganar masu Ilimin rayuwa da hikima ne, ta yadda idan suka yi magana ko hasashe sau tari yana zama wajabat. Cin farce mafi yawa ance yana dauwamar da mai yinsa cikin kunci da talauci. Kina son daga gidan arziki ki fad'a na talauci ne?"
Na girgiza kai da sauri.
Ya ce "To ki daina cire farce da baki."
Da hanzari na ce "Tom".
Abida ta ce "Allah yasa dan ya riga ya zame mata addiction".
Yaya Asad ya ce "Zata daina mana Abida".
Yadda ya yi maganar sai na ga kamar ba azababben nan da yake kidima ni ba.
Na saci kallonsa na ga still yana nan a mai siffar k'arfi, bai yarda ya tara teb'a ba. Ko a yanzu yafi matarsa kuruciya, haka nan sai ka dauka bai yi aure ba, duk da shekarar da muke shiga sakandire ya yi auren ga shi yanzu idan mun dawo mun kammala.
Ya waiwayo ya ce "Wai ke kallon me kike ta bina da shine haka? Tun dazu nake jin kallon ki a jikina, kada ki bari fa na juya na d'ora miki duniya".
Abida ta kyalkyale da dariya mai yawa.
Yayin da na yi muk'us a dalilin babu sakewa a tsakaninmu.
Sai da ta yi dariyar da ta ishe ta sannan ta ce"Kasan kullum idan muka je sashen samari bata yarda ta wuce ta kusa da duniyar, kuma bata gajiya da fad'in duniyar Yaya Asad bana son ki".
Shima ya yi dariya amma ba mai yawa ba sannan ya guntse fuska ya ce "Oh ba kya son duniyata? To ki tabbatar idan ba ki daina cire farce da baki ba, kina tare da ita. Kun cike jamb ne?"
Murya babu amo na ce"Eh".
"Wanne course kika cike?"
A hankali na ce "Computer science "
Ya ce"da kyau".
Ya mayar da hankali kan tukinsa ba tare da ya sake fad'in komai ba.
Abida ta ce "Yanzu kai ma babban Yaya haka zaka mini? Ai dai ni ce y'ar dakinka, amma ka tambaye ta akan karatunta ni baka tambaye ni ba, alhalin haka Yaya Faruku yake nuna mana banbanci, na yi ta cika bakin dan nawa yayan ya yi nisa ne, shine daga zuwanka zata k'wace mini kai?"
Ya bugi sitiyari bayan ya yi murmushi mai sauti ya ce "Wa zai shiga tsakaninmu, ai nasan ke guru ce, na kuma dad'e da sanin burinki, ki zama likita, ashe kuwa ba sai na tambaye ki ba, ita kuma na tambaya ne dan ta d'an saki jiki da ni, ba ki ga yadda ta takure ba ne?"
Ta numfasa ta ce "Na fahimta yanzu, amma da na ji haushi domin na kai kololuwar gajiya da yadda ake k'unsa mini takaici akan Bilki, da yadda ake yabon ta fini nutsuwa."
Ya yi dariya tare da ce wa "Autar Momi ke ma ki zama marar hayaniya irin ta mana, kinsan nutsuwa a wajen mace adone na mussaman da yake kawata ta fiye da adon da ake yiwa fuska".
Ta yi fit ta ce "A a Yaya bar ni na dinga k'watar kaina a wajen jama'a ita ma shiru shirun nata na nunkufurci ne, ni tunda muka je Katsina ta nemi rikicewa akan wani solalayi mai zubin makirai na tsorata da ita na fahimci ta wuce tunanina."
Da mamaki ya ce "Maigado wannan kike nufi?"
Da kazangi ta ce "Bilkin da take gefenka dai."
Ya numfasa ya rasa abin fad'i. Can ya sake numfasawa ya ce "Wonder shall never end! To kuma ta fasa da Faruku ne?"
Abida ta ce "Ai tunda ya yi aure ta ce "Ta fasa fas dama kuruciya ce".
Ya kallo ni kad'an ya mayar da fuskarsa a kallon gabansa.
Ya ce "Maigado wai kin fasa da Faruku da gaske?"
Da yake ni ban iya karya ba, ko zagaye zagaye ba.
Sai kawai na daga kai tabbacin eh.
Ya ce "Ikon Allah ban yi zaton akwai lokacin da zaki ce soyayyar da kika wanzu kina yi masa zata zama ta kuruciya ce ba. Lallai yau na sake fahimtar al'amarin mata da kuma kuruciya babban al'amari ne da ba zaka ganesu ta dad'in rai ba."