← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 33

Sashe 32

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Idan kuma kuttun mijine ya mintsine ki, ki sake kallona mana, kin san dai a yanayin da na shiga ba aikin k'arfi da sana'ar da ban yi yana karbe kudin ba. Komai ni ce a auren nan. Haihuwa uku bai taba siya mini ko da tsumman goyo ba. Hakan bai ishe shi ba, ya saka kafa ya gudu ya bar ni da su. Tsananin babu ya sanya ciwon yunwa ya kashe su daya bayan daya. Hakan kuma bai saka na fadi na mutu ba tunda da sauran kwanana a gaba. Shin yanzu bai wuce mini ba?"
Ta tambaya cikin karyewar murya tunda kuka take yi irin na sharbe.
Na rike hannunta sosai murya na rawa na ce ",Ina son na ga Abida, ina son na ganni gaban Baba babba. Ina son na fadawa Yaya Faruk halin da nake ciki. Ina son na ga Yaya Hamida a gidan nan"
Kuka ya sake kwace mini mai gunji sosai.
Ta ce "ki yi waya da Faruku. Baba babba kuwa kina iya zuwa idan kin nutsu. Ganin Abida ne sai dai ki yi hakuri domin nasan irin ganin da kike son ki yi mata, domin har yanzu lokacin da zaki ganta, irin ganin da kike so bai yi ba tukun.
Yaya Hamida kuwa duk tsawon lokaci zaki ganta a inda kike matukar Ubangiji ya sanya tasiri a cikin jini . Ki yi hakuri, sake hakuri, Allah yana tare da masu hakuri."
Hawaye jage jage a idona na ce "Na gode sosai Alti. Ina matukar jin dadin zamanki tare da ni. Kina debe mini kewar Abida da Yaya Munira "
Ta goge kwallar idonta ta ce "Ni ce da godiya, Ubangiji ya jibanci lamuranki."
Murya babu amo na ce"Ameen ".
Da ta ga na nutsu kadan sai ta yi amafani da fikon da ta yi mini ta ce "Tashi ki watsa ruwa, ki yi sallar azahar, kin ga har uku na shirin yi".
Ban musa ba, ban kuma amsa ba, na mike na durfafi bayi dan yin abin da ta ce din.
Wankan na yi, sannan na doro alwallah. Na idar da salla kenan ta shigo mini da plate dauke da faten dankalin turawa da ya ji alaiyahu da bushassen kifi.
Na karba tare da godiya.
Ta ce "Ki ci mahmah sai ki fito falo, zaman ke kadai na haddasa miki tunaninka masu kassara kwakwalwa."
Na ce "To Alti, zan fito".
Ta fita tana fadin "Bari na je na yi sallah, ke kam kin hada da laasar."
Ta ja kofar ta rufe.
Sannu a hankali nake cin abincin duk yadda bana jin dadin jikina da zuciyata haka na tura shi dan dai na sanarwa Alti nutsuwa. Domin idan ta ganni a irin wannan yanayin gabadaya rasa walwala take yi, ta damu da ni matuka gaya. Tana matukar kwantar mini da hankali, na aminta da ita irin sosai din nan.
Na cinye na bude ruwan robar da ta ajiye mini na sha. Na yi gyara na furta "Alhamdulillah! A fili.
Na yi shiru zuciyata sai sake sake take yi. Mafi girman abin da take sakawa kuwa shine me yasa Baban Amrah baya tausayina, baya nuna damuwa da lamarina tamkar yadda Alti take yi ne?"
Kaina ya kulle na kasa hasaso dalilansa na yin hakan. Daidai da Amrah idan ta ganni cikin rashin sukuni ko firgici ta iya harhada kalmomin da zata yi mini magana da su dan na samu sassauci, amma shi kam sai ya yi tamkar bai game ba, ko kuma ta hau fadan na cika makala abu a raina tamkar dai ni kadai ce mai damuwa.
Amma na fara gasgata Basma da ta ce na daina burge shi ne.
Na sake tuna Abida da ta taba ce mini ya yi miki yaro Bilki! Lokaci zai zo da zai daina ganin komai a tare da ke domin a lokacin kin masa tsufa sa'annin yayan cikinku zai dinga hari. Ba kuma zaki iya yin komai ba a lokacin domin ya riga da ya gigita miki kuruciyarki.
Cikin jarumta na danne hawayen da yake neman sake ballewa.
Murya na rawa na furta "Ki bani dama mana Abida."
Gabadaya zuciyata ta yi mini nauyi ainun. Kishi da kewar ahalina suka taru suka sababa mini irin al'amari a zuciyata mai matukar nauyi na gaske.
Gabadaya na rasa inda zan tsoma raina na ji sassaucin halin da nake ciki.
Wayata ta yi haske, na mika hannu na ga sako ne daga banki suke sanar da ni an cire dubu sittin da takwas ta hanyar amfani da katin (A.T.M)
Mamaki mai tsananin gaske ya rufe ni domin yau ba'afi kwanaki uku ba ya cire kudade masu nauyi.
Na sake dubawa na ga super market ne suka cire kudin.
Na shanye mamakina watakila kayan amfanin gida ya siyo ko kuma dan kayan kwalam zai siyo mini tunda ya sani idan na shiga irin wannan yanayi bana iya cin abinci mai nauyi.
Na yi sukuri ina tuno sadda Basma ta fahimci ATM dina na account din da albashina ke shiga na hannunsa. Hakan kuma baya hana wani lokacin ya karbi A.T.M din business account dina.
Cikin fishi ta ce "Ba fa zaki kubuta daga abin da kike tsoro daga gare shi ba. Duk sadaukarwarki gare shi ba zai sanya shi ya zalunci kansa ko ya tauyewa zuciyarsa abin da take so ba. Ina jiye miki ranar da zaki fahimci ainihin karatun da nake miki bita a kansa. Ina fatan ki fahimta da wuri ba sai lokacin da komai ya k'ure ba".
Na numfasa duk da ina cikin fishi amma a kasan raina still ga ni nake yi, menene aibu idan mace ta taimaki miji, ta kuma rufa masa asiri, menene jin dadin arziki idan har iyalinka basu wadata ba?

*Muna siyar da gold daidai da Farashin kasuwa*
*Muna siyan Wanda yake da receipt daidai da Farashin kasuwa*.
*Ina matan da suke son siyan gold amma Basu san kansa ba, suke gudun a cucesu?*
*To kakarmu ta yanke sakandon kuwa zamu siyo muku Babu cuta babu cutarwa daidai da Farashin kasuwa, abin jin dad'i Allah ne wakilinku*.
*Ku tuntube ni a wannan lambar wandada suka shirya siya da gaske*
*08032773332*

Na kalli agogo na ga biyar tana shirin yi, daidai lokacin kuma su Farha zasu tashi a islmiyya ita da Yaya. Gabadaya na zama weak Dan haka haka na kwalawa Alawiyya kira.
Ta shigo a hanzarce ta tsuguna.
Na ce "Dauko mini jakar hannuna, ta mike da azama ta dauko akan madubi.
Na zuge na cire yan dari biyar biyu na ce "Ki je ki taho da su Farha ba zan iya tuki ba".
Ta karba tana ce wa "To mahma sannu Allah ya sauwake."
Bata jima da fita ba, Amrah ta shigo bakinta dauke da sallama, tana sanye cikin uniform, ga jakar makaranta a kafadarta, tabbacin yanzu ta shigo. Da kulawa ta gurfana a gabana ta saka hannu tana taba jikina.
"Sannu mamah na ji babu fever". Ta fada cike da kulawa.
Na murmusa kadan duk da idanuwana sun yi kozai kozai na ce "Da sauki sosai Amrah. Ina Dady?"
Ta ce "ya ce na taho aiki ya rike shi"
Na ce "Tom ki je ki samu wani abu ki ci, nasan kun yi sallah".
Ta mike ta ce "Bari na fara yin wanka."
Na bita da ido ina sake shaidar tsananin kamannin da take yi da Sahal. Hatta tsayinsa duk ta kwaso, tana aji hudu a sakandire yanzu.
Na yunkura na mike cikin k'arfin zuciya na fara zagaya dakina ina ta kokawa da sashin zuciyata da yake kalubalantar Babanta akan da Hawwa ya fita ya kashe mata kudin da suke nawa ne. Kudin da ba'a b'agas nake samunsa ba, sai na shafe kwanaki ashirin da biyar ina sammakon barin gidana duk sanyi, duk zafi ko damina, haka nan yini nake ina fama da alli da biro hadi da marking bayan bata lokaci wajen yin nazari tare da bitar yadda zan dinga koyarwa cikin hikima ta yadda dalibaina zasu fahimci darasin da kyau. Ba dan komai ba sai dan na tabbatar albashina halal ne. Sai ga shi duk wannan fadi tashin ina yi ne, wata tana ci a b'agas cikin dabara da hila.
"Tirkashi." Kalmar ta subuce mini ba tare da na shirya hakan ta faru ba.
Chapter 32 · 0% Book details