← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 33

Sashe 23

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ne ba na gaskiya ba. Da zarar an haɗaku zaman aure hirar mintina goma ma sai an wayi gari ba zai iya ware wa cikin lokacinsa ya yi da ke ba, a yanzu kuma ya yi miki sabo da doguwar hirar da idan baki ji daga gare shi ba zaki kidime ki kasa sukuni. Me za'a yi da soyayya irin taki ne Bilki?" Da nasan gaskiya ta faɗa sai na kasa amsa mata domin ba ni da bakin yi mata musu ko raddi dan idan ta kaikaice ta fara cashe mini sai ta sanya ni kuka na gaske. Sannan zata juya ta yi kwanciyarta, cikin nutsuwa zan ga tana sauke numfashi tabbacin barci mai cike da nutsuwa take yi. Da ƙyar na yi barci ina ta saƙesaƙe ko jinya ce ta kwantar da shi tunda a kullum sai ya ce mini ba zai iya barci bai ji muryata ba. Shiyasa ma baya ƙirana sai ya yi sallar Isha domin da zarar mun gama waya barci yake yi muryatace abu na ƙarshe da yake ji a ko wanne dare. Ina idar da sallar asuba na sake ƙiran layinsa amma shiru kake ji a kashe take. Na shiga damuwa duk yadda nake son komawa barci ranar ban samu sukunin komawa ba. Sai da muka karya muka yi sashen Momi hannuna ɗauke da ledar alawa da biskit masu tsada cikin wanda Sahal yake kawo mini na ɗiba na zuba a leda da yawa da mufin na bawa baban Bilkisu ya kaiwa Hafcy. Muka tarar shi kadai yana karyawa kuma ya yi haramar komawa. Muka gaishe shi ya amsa tare da faɗin "Na shiga gaida Mami da Baba ƙarami baku tashi ba". Abida ce ta amsa da ce wa "ki ce ban tashi ba kawai, amma ita bakam ta yi bata cikin hayyacinta saurayinta ya yi mata fushi tun daren jiya ta rasa walwala da kuzari ". Ga mamakina sai na ga ya ɓata rai, bacin ran da ya bayyana har a fuskarsa. Da farko tamkar zai share sai kuma ya kasa hadiyewa ya ce "Har haka kika bari ya mamaye ki ne Bilki? Ni ba dan kar na zama babban kwabo ba da sai na ce miki kin fishi ƙarfi da karsashi, gabadaya fa siffar mata gare shi wannan yaron, dan dai kina sonsa ne, autar momi ta yi gaskiya zubin makirai ne da shi, kin kasa ganewa, bansan me yasa ba zaki gane gaskiyar lamari ba, yanzu saboda Allah Maigado menene aibun auren mai mata ne?" Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Amma saboda yadda Abida ta kasa ta tsare tana kallonmu nasan ba iya kallon kawai take yi ba, har da nazari. Domin kamewa ta yi tana kallonmu cikin tsananin nutsuwa. Dan haka cikin rawar murya haɗi da kuka na ce "To shine ya tunkare ni da sunan soyayya ban da shi babu wani, sannan mai matar ai bai zo ba, bare ace na jingina masa aibu." Bansan ya aka yi ba Abida ta yi fit ta ce "Sau dubu nawa zasu zo? Yaya Faruku fa?" Takaicinta ya shake ni, na rushe da kuka sosai na ce "Da yaushe ya taba tare ni da sunan soyayya ta gaskiya ba ta wasa ba?" Kafin ta amsa mini Baban Bilkisu ya ce "Kin fita gaskiya. Faruku bai zo da gaske ba, amma akwai wadanda suke son ki da gaske kina tankwabarwa, abokin nan nawa da gaske yake yi, bayan shi akwai wani da zaki amince ya tabbatar mini ko yaushe a shirye yake domin kin yi masa irin sosai ɗin nan". Abida ta numfasa ta ce "oh Yaya Asad! Ya yi biris da ita domin sosai ya ɗaure fuska dan haka dole ta kame bakinta ta tsuke. Ya numfasa ya ce " share hawaye ki ki daina kuka kin ji, ba wacce aka yiwa auren dole a gidan nan, matukar ina raye kema ba za'a yi miki ba, ina miki fatan alheri tsakaninki da yaron". Daga haka ya mike ya zura hannu a aljihunsa ya ciro ƙudi ya damƙawa Abida ya ce "ke da ita, ku sayi abin da kuke so idan zaku koma makaranta." A sanyaye ta yi masa godiya. Ni kuwa na kasa yin godiyar. Ya ce "To mu je ku raka ni mu yi sallama da su Baba." Na miƙe na zare abin hannuna wanda na stones ne, na sake zaro ribbon din kaina na jefa a ledar alawaer na ce "ga shi ka kaiwa Hafcy, ka faɗa mata I realy miss her silly questions." Ya murmusa ya ce "Kullum sai ta yi hirarki, kullum sai ta ce "Anty Maigado zata. Ga shi Maigado ba mai fahimta ba ce". Zuciyar tawa ta sake karaya,.nauyi mai yawa ya kama ni. Na saci kallon Abida na ga itama kallona take da dukkan nutsuwarta. Haka muka bi bayansa ba tare da mun iya tofawa ba. Ya yi sallama da kowa, iyayenmu suka bishi da sanya albarka tare da nema masa tsarewar Ubangiji akan dukkan lamarinsa. Har waje muka bishi ni da Abida. Bana manta kallon da ya kafe ni da shi, amma bai ce ƙala ba, illah faɗin "ku kula da kanku Allah ya sake haɗamu da alheri." Abida ta rike hannunsa ta ce"Ka kula da kanka yaya! Su Baba na buƙatarka, matarka da ƴaƴanka na buƙatarka, muma muna sonka, kada ka saka damuwa mai yawa akan lamarin wanda baya bukatarka ko ba shi da asara idan ka haɗu da jinya ". Ya zuba mata ido irin sosai tare da ruƙo dukkan hannuwanta murya cike da rauni ya ce "Zan kiyaye autar momi! Sai dai bana son ki zama mai son kai, ko tursasawa ga rayuwar wani ta hanyar kyara da ƙaranta mu'amala. Kina da hazaƙa, kina da saurin fahimtar al'amurra. Na roki kada ki yi ƙullaci ko kushe wanda Maigado take so " Ta amsa da ce wa "To" a takaice. Jikina ya sake sanyi sosai domin na gaskata sona yake yi. Sai dai tabbas bai yi mini ba, duk yadda yake a tsaye kuma ƙarfaffa. Amma bana son auren zumunci, bana son auren mai mata bana son baƙin namiji. Ya shiga motar da ta zo daukarsa suka tafi. Abida ta yi gaba ta bar ni da sanyin jiki. Da ƙyar na ja ƙafafuwana na bi bayanta. Shariyar Abida da rashin samun wayar Sahal suka yi mini rubdugu. Yini guda ina ɗaki sai juyi nake yi na rasa sukuni a jika da zuciyata. Da na idar da sallar la'asar na dauki wayar na sake ƙiran layinsa a karo na barkatai. Cikin sa'a ta shiga, gaba-daya na ji wani irin salama ta shige ni. Sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba. Na sauke ina sake gaskata lallai akwai matsala. Sai dai tunanina bai haƙaito mini menene dalilin faruwar haka ba. Ina ta kokawa da zuciyata akan kada na sake ƙiransa. Ba zato sautin da na sanya masa na real love by massari ta hau tashi. Kamar zan share amma na kasa sharewar. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
Chapter 23 · 0% Book details