← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 33

Sashe 27

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

*Lafazi writer's*

13
Message Amreesh spices & more on WhatsApp. https://wa.me/message/Y7KSRJ7PDQSCC1

*Fatan alheri ga*
*Haj Dr Safiya Saulawa*
*Haj Zahra Shehu*.

Sai da aka yi sallar isha sannan Baban zaria da matarsa da ake kira da Mama suka kai ni gidana da babu nisa tsakaninmu da su. Unguwar kusa ne kwarai da jamiaar.
A gidan muka tarar da shi tare da amininsa Lawal.
Addua sosai Baba ya yi mana tare da jaddawa Sahal girman hakkina da yake kansa.
Haka nima ya ta nanata mini na kulla abota da hakuri da kuma juriya, sanna na gane biyayyar da aka kallafa mini na yi masa umarnine daga Ubangiji. Dan haka duk abin da zan yi masa na hidima na yi min Allah dan kuwa shi ya shirya tsarin aure da kansa. Mama ta shigar da ni cikin dakina ta zaunar da ni akan gadona tana ta yi mini fatan Ubangiji yasa na zama tsohuwar gidan.
Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a sabon gidana da zan fara sabuwar rayuwa a cikinsa.
Jin ana kiran sallar magahariba ya sanya suka tafi, su Sahal suka rakasu wajen mota suna ta godiya da ban gajiya gasu Baba, sai da motarsu ta bace musu. Basu shigo ciki ba suka wuce masallaci dan sauke farali.
Bayan an idar suka shigo da ledoji da alamu sun siya tun dazu a mota suka barsu.
A guggurje ya yi barkwancinsa tare da ajiye mini bandir din yan 200 wai kudin siyen baki.
Ya yi mini sallama ya wuce, dan hanyar Katsina zai kama a daren nan.
Da kazangi ya dawo ya zauna daf da ni ya rungume ni yana shakar kamshina. Gabadaya na takura, bansan meyasa ban ji tsumin da na ji a lokacin da Yaya Faruk ya rungume ni ba a yanzu.
Tabbas jikina ya shiga bakon yanayi da bai saba ba, ban sani ba ko tsananin alhinin rabuwa da ahalina tare da fargabar yadda zan shiga cikin sabon ahali ne oho.
Cikin nutsuwa ya ware mayafin da na lulluba da shi. Ya mikar da ni ya ce "Zo mu je falo mu ci abinci. "
Tsire ne mai kyau sai yogurt da kuma ruwan roba masu sanyi.
Duk yadda nake jin yunwa ban iya cin naman ba, sai yogurt din na sha, shima ba wani mai yawa ba.
Bai wani sake ba, sai da ya dawo daga sallar isha.
Ya sake janmu sallar nafila ya yi mana adduar zaman lafiya da albarkar rayuwaa.
Da rawar Jiki ya mannu da ni ya ce "Yau ranace ta mussaman a tarihin rayuwarmu gabadaya. Ina fatan Ubangiji ya sanya albarka a dukkan zaman da zamu yi."
Murya babu amo na ce ",ameen".
Duk yadda nake jin bakunta ta kewaye ni sai da ya hilace ni ya dangana ni da lafiyayyen gadonmu da ya sha shimfida ta alfarma.
Cikin gaggawa yake yin komai, gabadaya ya dinga sarrafa ni, ya jima yana shafata tare da kissing dina. Bai samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar ya isa inda ya dade yana fatan ya isa. Bai wani jima ainun ba. Yayin da ni ban wani gane komai ba sai radadi.
Na kalle shi yana ta numfarfashi, daga haka barci ya yi awon gaba da shi. Na jima ina ta sake saken zuci ban kuma isa na hakaito mai nake sake sake a akansa ba.
Na duba wayata na ga shadayan dare. Na mike na shiga bayi dan yin wanka. Domin Mami ta ce mini kada na bari na dinga barci da janaba in ba dole ko lalura ba.
Na gasa kaina sannan na yi wanka. Har na kammala na shirya bai motsa ba. Na lallaba na kwanta a gefensa.
A haka nima barci ya yi awon gaba da ni.
Bamu makara sallar asuba ba, sai dai da muka koma din sai wajen goma muka farka a dalilin dukkanmu mun tara gajiya, na fito daga wanka ina shiryawa cikin nutsuwa, shi kuma yana daga kwance yana kallona cikin murmushi.
Daidai lokacin kuma ya fita ya karbo abin karin kumallo da aka aiko mana daga gidansu.
Funkaso ne da kunun gyada. An zuba cikin kyawawan kwanuka.
Kaitsaye dakin ya shigo da kwandon. Ya zuba mini ido ina sanye cikin guda daga cikin kyawawan material din Malaysia, mai kalar siminti da yarfin kwanduwar kwai.
*Contact umm Nihla for all your *Malaysian fabrics.
*Malaysian Batik and more*
*All are unique and classy*
*Available wholesale and retail*
.......
Ya ce "Billy kin kara kyau sosai
Na murmusa cikin kunya na ce "Na gode ".
Ya wuce bayi yana ce wa "bari nima na yi wanka kada tazarar da kika yi mini a kyau ya sake tsananta."
Na murmusa ba tare da na ce kanzil ba.
Bai wani jima ba,¹0 pop-up ya fito daure da tawul na yi maza na dauke kaina. Bai ce komai ba ya fice zuwa daya dakin da yake a matsayin nasa.
Na hanzarta canja zanin gadon da duk ya baci da jinin budurci na canja wani. Na shiga bandaki na kama duk inda ya baci na wanke, na yarfe sannan na ninke na baza shi akan kyauren bandakin.
Ya shigo sanye cikin yadi mai taushi shudi kalar sararin Subhana(sky blue).
Sosai ya yi kyau zuciyata ta doka da tsananin gaske, take raunin da soyayyarsa ta yi a dalilin Yaya Faruk ya kau, mai kyaune irin wanda nake so duk da dai siriri ne irin sosai din nan, na tabbatar sirintarsa tana karawa tsayinsa kaimi. Sabuwar soyayyarsa ta sake yun mmkuro mini tana sake bin dukkan sassan jikina tana mamaya da k'arfin gaske.
Idona ya kada kwallar shauki ta cikasu taf.
Da hanzari ya iso inda nake. Ya ce "sannu da aikin lada Bily. Allah ya yi miki albarka! Mu je mu karya yunwa nake ji sosai."
Gabadayanmu kamshi muke yi. A plate daya ya zuba mana abincin. Ya turo mini kofin shayi gabana tare da ce wa "zuba sugar da su madara yadda zasu yi miki".
Ban ce komai ba, domin kaina a kasa yake, kunya da bakunta ke dawainiya da ni gabadaya.
Cikin nutsuwa da walwala muka karya duk da ni kunya ta yi mini dabaibayi.
Bai fita ba sai da aka yi sallar azahar. Ya yi tafi masallaci ya ce zai shige gida ya gaidasu Baba.
Na idar da tawa sallar. Na dauko wayata da take kashe tun daren jiya.
Na kunna, na jinkirta ta daidiata.
Mami na fara kira, ta amsa da walwalar da take alamta mini ta yi kewata sosai.
Har na ji dadin yadda ta mu'amalance ni. Ta dinga fadin nasan kina da hakuri da shanye damuwa, ki yi kokarin ninka hakurinki Bilki, hakurin nan dai shine aure, shine ma rayuwa gabadaya. Murya babu amo na ce "To Mami na gode Allah ya kara miki lafiya da hakuri. Ta amsa da fadin "ameen, amma ai ni bana hakurin da zan cutu, a sha'anin aure ne kawai nake dukkan hakuri domin zawarci bashi da dadi Bilkisu!
Ko a gaban uwarka da ubanka zaka yi shi kuwa bare ni marainiya ce, tun ba'a aurar da ni ba na rasa uwarta, mahaifina kuwa ban yi haihuwar fari ba na rasa shi. Ga shi ni din an jarrabe da wata irin nannauyar jarabawa.mai matukar nauyi. Y'anuwana suna cikin magautana."
Na nisa na ce "Mami sunnar rayuwace ai, ba ke kadai bace kike da k'alubale da y'anuwanki ba, mutane da yawa ne, kawai ke dan kina yawan furzarwar ne, ba kya iya barin al'amarinsu a ranki ko dan a samu saukin gaba da b'acin rai. Manyan bayin Allah sun fuskanci kiyayya a wajen danginsu, haka Annabawan Allah. Idan kuma Allah ya rufa maka asiri Mami ba wani mahalukin da zai tona maka. Sai dai ya tonawa kansa.
Na numfasa na ce "Allah ya jiqan magabatanki, Allah ya saukaka miki dukkan kasafinki Mami ".
Ta amsa da"ameen ameen a sanyaye."
Karon farko da na yi mata jirwayen hakuri akan shaaninta da danginta bai zame mini sanadin bacin rai ba.
Na kashe wayar na kira su baba daya bayan daya.
Su kam dukkansu albarka da addua suke yi mini. Suna sake jaddada mini basa jin dar a kaina ba zan kunyatasu ba.
Abida na kira daga karshe, muka sha hira, tana ta tsokana tana cewa "Na ajiye mata kazar amarci a fridge tunda satin sama zata dawo makaranta.
Chapter 27 · 0% Book details