← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 33

Sashe 25

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na saki ajiyar zuciya mai nauyi ina cigaba da leken yadda ake ta daura tampol tare da shimfida tabarmai . Tsawon lokaci ina tsaye ina kallo tare da cankecanken me za'a yi haka a gidan na hidima bamu sani ba?
Na tabbatar da mutuwa ce ba zan ga ana yin aikin cikin walwala da nutsuwa ba.
Nan da nan aka kammala shimfida aka shiga ajiye kulolin abinci kalakala tare da lemounan kwalba na maltina da su coke.
Na sake shiga mamaki, sai na yi tamkar na tashi Abida sai na fasa domin tashinta a barci bata dauke shi da sauki ba. Yana cikin zunubin da idan aka yi mata sai an biya ta da wani abu, ko ku yi ta buga dabi.
Kafin ka ce kwabo kuma sai shigowa ake yi ana ta zama, na gane wasu da yawa abokan Yaya Faruk ne. Yayin da ban gane wasu da yawa ba.
Ina tsaye ina kallon ikon Allah kawai sai na ga Yaya Faruk ya shigo ya zauna cikin alhini, sai mika masa hannu ake yi ana yi masa jaje tare da fatan Allah yasa hakanne alheri.
Kaina ya sake kullewa, a fili na furta "Menene yake faruwa ne?"
Gabadaya wajen sai hada hada suke suna cin abinci ana ta hira yayin da Yaya Faruk ya tagumi cikin takurarren yanayi.
Can Kuma na ji ya hau fadin "Ba fa hira da nishadi na kiraku mu yi ba. Na gayyatoku ne ku taya ni alhinin rasa sarauniyar shaiba".
Suka dauki hayaniya kowa na fadin "Rashin rabo ya sanya bai fahimci Dingishin kwado da wuri ba.
Ni kuwa gabadaya na ji jiwa na katantawa da ni, kaina ya kulle dakin ya shiga juya mini tamkar an mayar da kasan ya koma sama.
Hawaye ya balle mini. Wani irin abu ya sake tokare mini a kirjina. Hakan ya saka damuwar da nake ciki ta rubanya tsananta. Bansan ya aka yi ba na ware baki na fashe da matsanancin kuka, hawaye da majina suka dinga sintiri a fuskata.
A kidime Abida ta tashi ta zauna a tsakiyar gadonta.
Murya a dashe kuma a firgice ta ce "Me ya faru, mutuwa aka rafkane Bilki? Hayaniya nake ji sosai".
Ta duro a gigice dan taga abin da yake wanzuwa har ya sani kuka sosai.
Bata ga komai ba, illah Yaya Faruk da jamaarsa suna ta cin abinci da alamu walima ake yi duk da shi din bata ganshi da kuzari ba.
Ta saki labulen yayin da ni kuma na yi kasa na zauna dabas a kasan tayal ina cigaba da kokawa ainun.
Ta yi shiru amma gabadaya jikinta ya saki. Ta zauna kusa da ni a tausashe tamkar ba Abida ba ta ce "Na hada ki da darajar ma'aiki ki fada mini me ya sanya ki kuka irin haka? Ta ruko hannuna na dama ta dora a saitin inda zuciyarta take. Wani irin bugu take yi fiye da kima. Ta zuba mini idanuwanta da barci da firgici suka jirgitasu. Na yi kasa da kaina ina gunjin kuka. Ta rike hannuna sosai tabbacin hakuri take ba ni duk da bata furta hakan da baki ba.
Da rawar murya na ce "Yaya Faruk ne Abida! Na furta hakan cikin rushewa da kuka fiye da wanda nake yi.
Ta zabura ta fita ko mayafi bata saka kan doguwar rigar barcinta cotton ba.
Da Yaya Sulaiman ta yi kicibis.
Ya shigo diban ruwan da lemo a fridge din momi.
A matukar razane ta ce "Me yake faruwa ne a gidan nan Yaya Sulaiman? Ina Yaya Faruku?"
Ya amsa da ce wa "Ga shi can ana masa jajjabin an kasa shi a soyayyarsa da Bilki!
Tausayinsa ya tsirgawa Abida ta sani yana son Bilki, ta kuma sani tunda ya gane Yaya Asad shima an jarrabe shi akan sonta shiyasa ya shiriritar da maganar tun kafin su fahimci Yaya Asad na sonta shi ya fahimci hakan.
Gabadaya dukkansu uku tausayinsu take ji, amma a yau na Yaya Faruk yafi tsananta.
Bilki kuwa haushin yadda ta rufe ido ta kasa zaben mutum guda a cikin yayyen nasu ya dakushe tausayinta.
Ta koma ta zauna a bakin gado tana hurar da iskar damuwa. Kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce "Bilkisu ki rufe mini baki, tun ban miki sanadin da zaki yi kuka fiye da hakan ba. Wanne irin kasafi ne haka? Menene zaki yi kuka akan Yaya Faruk alhalin ba dole aka yi miki kika zabi waninsa kika bar shi ba.
Ko makaho ya zauna da ke da Faruku sai ya gane yana tsananin sonki, amma kika runtse idanuwanki kika bar shi. Yanzu kuma ki ce zaki yi kuka dan yana bayyanawa duniya alhinin asarar rashinki da ya yi!
A matukar kufule take wannan maganar.
Tashin hankali ya yi mini kawanya. Zullumi da fargaba suka saka na yi zurzuru cikin lokaci kalilan. Na rarrafa na isa gaban gadon da take zaune na durkushe gabanta na ruko dukkan hannuwanta biyu, murya na rawa na ce "Abida ki yi mini adalci, ki ji tausayina ko iya na yau ne a rayuwata.
Na rasa gane me nake ciki, kaina na shirin fashewa, zuciyata na shirin tarwatsewa Wallahi ina jina cikin bala'in da ya yi mini dauri tamkar huhun goro!
Ta sassauta amma bata furta komai ba.
Na ce "Ki yi alkalanci na gaskiya Abida kin sani ina sonki, kin sani da ke nake son na yi sharing damuwata anan duniya dan Allah kada ki rufe mini wannan damar a wannan tsukun da nake ciki na cankacakare"

Ta cigaba da yi mini zuru hakan da na gani na alamta mini hankalinta na kaina tare da abin da zan furta.
Hawaye na zuba na ce "Abida tsakaninki da Allah Yaya Faruk ya taba tsayawa kai da fata akan yana sona, so na gaske?"
Ban jira amsarta ba na ce "Na sani kun fi kusa da shi a kaina, amma ban zaci zaki yi mini irin wannan son kan ba Abida. Ya kike so na yi? So kike na ce wa baba babba Yaya Faruk nake so ya aura masa ni alhalin shi da yake namiji bai yi hakan ba? Bayan matarsa yana da halin ya auro uku ba ni kawai ba amma tsananin tsoronta, ya hana shi kuzari akan sha'anina. Amma ke da kika fahimce ni, irin fahimtar da babu wanda ya yi mini irinta sai kuma ki hau gaba da ni akan lamarin da bani da laifi a cikinsa ko kankani! Akan me zaki rufe mini kofofin tattauna halin da nake ciki Abida? Akan me zaki yi mini irin wannan alkalancin akan lamarina da ya Faruk?"
Na fada ina rushewa da matsanancin kuka domin tsakanina da Allah gabadaya na daburce na kidime ban san ina son yaya Faruk over ba sai a ranar.
Ta sassauta kwarai da gaske ta busar da iskar damuwa ta ce "Yaya Faruk mutum ne mai matukar karamci da sadaukarwa, yana sonki, yana da burin ya aure ki, so yake ki kammala sakandire sai ya bayyana ta yadda ba zaku dade kuna dating ba zaku yi aure. Kwatsam sai aka jarrabi yayansa da sonki, irin son da ya kasa boyuwa a kirjinsa da gangar jikinsa. Hakan da Yaya Faruk ya fahimta ya sanya ya zabi ya bar lamarinki a zuciyarsa gudun kada shaidan ya kawo musu yamutsi! Amma ke gabadaya kin tattara kin rufe kofar da Yaya Asad zai same ki, kin ga ai dole Yaya Faruk ya shimfida tabarmai a yi masa jajen asarar da suka taffka ta biyu babu "
Na kasa cewa komai sai kukan da na cigaba da yinsa ainun.
Murya ba amo Abida ta sake cewa "Dole na ji babu dadi akan sha'aninki mana.
Na yarda Yaya Faruk bai zo ya nuna kansa da gaske ba. Yaya Usman fa? Yaya Asad fa? Wanne irin hannunka mai sandane bai yi miki ba? Har mai suna ya yi miki alhalin bai sanya sunana ba, kinsan kuwa na fiki cancantar ya mini cibina ba dan cikinmu guda ba sai dan tun filazal ni ce tasa ke ta Yaya Faruk ."
Na zuba mata ido hawaye na cigaba da tsere akan fuskata.
Yayin da ta numfasa ta ce "Dan haka ki rufe mini baki da wannan kukan domin dai ke kika yiwa kanki zabin da kike ganin kin gamsu da shi. Ba kuma zai yiwu ki hana zuciyata taya y'anuwana yanuwana bakin cikin asarar rasa ki da suka yi ba, hakanan ba zaki iya cire mini takaicin yadda kika zabi zumuncinmu ya yi rauni ba.
Dan kuwa da wani cikinsu kika aura zan yi mu'amala mai k'arfi da gidanki fiye da ace bare kike aure".
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://www.instagram.com/deenah_cakes_and_more?igsh=c2lnZjk5Z3pjYjNw&utm_source=qr
*Deenah cakes and more -Kano*
*09038055790*
*IG @Deenah cakes and more*
*Snacks such as*
*Birthday cakes*
*Cupcakes
*Samosa*
*Springrolls*
Meatpie
*Frozen snacks*
*Event snacks*

*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

12
Chapter 25 · 0% Book details