← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

✍️
[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

5

*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750

Yini guda muna ta namu kasafin a dakinmu, sai da muka sallaaci la'asar sannan muka dunguma sashenmu suka gaida Mami muka cigaba da yin shiriritarmu. Sai da magariba suka tafi. Yaya Munira tana ta jaddada mini na taho mu kwana tare sai gobe mu zo nan mu kwana.
Bayan sun tafi Mami ta zuba mini ido cikin takaici ta ce "Sokokuwar banza sai yanzu kika ga damar zuwa mini? Tun azahar kuka dawo amma kika kasa zuwa sai dazun nan! Munira tun safe ta zo gidan bata zo ta gaishe ni ba. Abida kam ai ko motar bata gama tsayawa ba ta yi wajen uwarta, amma ke da yake baki bani muhimmanci a duniyar ki ba, ai kin bisu kin tayasu adana uwarsu. Ke kam kin yi asarar hali gabadaya, sunan Saratu kika fi dacewa ki amsa ba mai gadon zinare ba."
A tausashe na furta "Ki yi hak'uri Mami".
Tsaki kawai ta yi, ta shige dakinta.
A wannan ranar a sashenmu na kwana domin fargaba nake yi na ce zan tafi wajensu Yaya Munira.
Da daddare Yaya Sulaiman da su Ansar hadi da autarmu duk muna falo tare da Mami sai fad'a mana rikicin da take yi da yan'uwanta, tare da ankarar da mu y'an uwanta sun wareta ne dan mijinta ya zarta nasu. Sannan dangin Babanmu kuwa suna fifita Momi a kanta dan suna ganin Baba babba ne don 1.
Alhalin arzikin tare da mijinta ne.
Ni dai ban tofa ba, ina safare ina jin babu dad'i, domin kaf dinmu bamu son yan'uwanta a dalilin yawan laifinsu da take furzarwa a gabanmu babu sassauci. Sannan dangin Babanmu ma a hagunce muke kallonsu muna ganin sun fi son Momi da y'aya'nta.
Ansar da yafi kowa bin ra'ayinta ya ce "Rabu da y'an kusun uwa Mami! Shiyasa gabad'aya bana musu gaisuwar arziki daga dangin na ki har na su Baban, gabad'ayansu na washe su, me zan yi da wanda zai musgunawa uwata?"
Ta muskuta tana jin dad'in yadda yake taya ta son komai tamkar dai mace.
Ta numfasa ta ce "Da wayonka ka taso ka ga yadda nake tiritiri da y'an uwana menene bana d'ora maka ka kai musu, duk zanin da na cire idan zan bayar su zan bawa amma tsabar hassada basa yarda su fad'i alherina, komai zan basu a raine ne, kowacce ta zuba mini ido, ina auren mai wadata alhalin asirin ciki sai hanji. Komai d'an-uwa ya yi babakere a kai, me za'a yi da kasafin gidan nan ne?"
Suka had'a baki wajen fad'in "Ai Baba k'arami ne ya sarayar da y'ancinsa gabad'aya fa ya koma tamkar yaron Baba babba ne ba wai d'anuwa ba. Kuma abin kaicon dukiyar tasu ce gabad'aya, watak'ila ma ta Baba k'aramin ta fi rinjaye, ya kasa tsayawa waje d'aya, yau na Katsina gobe na Funtua. Idan ya zo garin ma idan kana son ka samu hankalinsa ainun sai dai ka bishi Ladi farms yana can yana k'arar da lokacinsa cikin dabbobi".
Na saki gauron numfashi tare da kame bakina duk kuwa ina da kalamai fal a zuciyata.
Nan da nan Mami ta hauro ta dinga surfa mini sababi tana furzar da kalamai masu ciwo.
"Shashar banza mai za'a yi da zuciya irin ta ki. Munafukar wofi, to duk iyashege irin na ki, ni ce dai kanki ya dawa, domin ni din da ba kya so, ni ce na kawo ki duniyar."
Murya babu amo na ce "Ta ya ya zan k'i ne Mami? Na roke ki yi hak'uri."
Gabadaya suka yi mini ca suna kaico da ni, a lokacin kuma na fara fahimtar dukkan y'anuwana suna matukar jin zafina a dalilin nafi shaƙuwa da yaran Baba Babba a kansu, duk da basu tab'a tunkarata kai tsaye ba. Amma maganganun da suke amayarwa tare da yi mini kaico ya sanya na fahimci dukkansu masu wahalallen ra'ayine, basa raina abin yin sarhutu.
Hatta su Ansar da suke kannena sai da suka saka baki wajen caccakata.
Babban abin da yake ba ni mamaki idan an had'u basa nuna adawarsu da iyalin Baba babba, hatta Mami idan suna tare da momi da yaranta sai ka rantse babu komai a ranta na gilli saboda tsananin yadda ta iya hadiye komai.
Idan na zauna ni kad'ai ina nazartar yadda al'amarin yake gudana sai kaina ya yi mini nauyi ainun. Tare da hasashen ko Momi da yaranta ma suna adawa da yadda Baba babba yake wahala da mu babu banbanci da iyalinsa?
Wannan tunanin na matukar caja mini kai, domin ni a lokacin ban yi zaton za'a iya mua'amala da fuska biyu ba.
Kullum kwanan duniya wannan tunanin na dabiar ahalina ya haifar mini wani irin tunani dangane da mutane, a hakan na samo sha'awar son nakaltar halayyar danadam. Sai dai ban samu damar hakan ba, a dalilin zuciyata a sake take. Sai nake yiwa mutane hukunci da yadda nake. Bana zargi, bana munanan zato.
Da naga tunanin halayyar momi da yan'uwana zai gigita ni, sai kawai na daina matsawa kaina, bana tunawa sai idan ina gabanta, sa'a d'aya ma bata nunawa a waje ,sai imu imu. Sai dai kuma hakan ya janyo kulli da yawa a zukantanmu. Misali mafi yawa muna yiwa kowa kallon munafukanmu ne. Ma'ana a bazance muke kallon danginsu Baba, tare da zargin sunfi son su Abida.
Haka dangin mami. Tsakanina da Allah ni bana wannan akidar haka ma Yaya Sulaiman yana da sassauci, to amma Shi wani irin mutum ne da Magana ma bai cika yi ba matukar bata shafe shi ba, dan haka Duk abubuwma da Mami take fada ko take yi, a dunkule zai ce "Yi hakuri, Ki cire komai a ranki,, Allah ya Baki Ni, ba abin da ba Zan yi miki ba na jin dadi".
Ga shi a wajenta ba ni da kwarjini ko kad'an. Haka nan yan'uwana basa yarda su yi maganar sirri matukar ina wajen, sun riga sun yi amanna nafi son Momi akan Mami na kuma fi kaunarsu Yaya Munira akansu, wanda ba haka ba ne duk yadda nake son y'aya'n Baba babba dai bai kai y'aya'n da mahaifiyata ta haifa ba, hakanan ba zai yiwu na so uwar wasu sama da tawa uwar ko hauka take yi kuwa.
Haka dai na lallaba kwanakin hutunmu suka k'are.
Ranar da zamu koma makaranta an kammala shiri tsab har mun shiga mota mun zauna, sharrin karfe juyin duniya mota ta tashi amma ta ki.
A lokacin motocin gidan hudu ne, ta Baba babba d'aya, ta Baba k'arami d'aya sai guda biyu ta amfanin gida. D'aya ta amfanin gidan ta yi faci, wacce kuma aka shirya a kaimu a ciki ta k'i tashi.nBaba babba da yake tsaye ya ce "Sai a nemo bakanike dan kuwa ta'azziya zan je Maska."
Abida ta ce "Gaskiya Baba motarka ce baka son bamu, tunda motar nan ta iso kake kaffa kaffa da ita. A lokacin mota kirar 190 ta hamshakan Alhazai ce.
Ya ce "Da ace yayanku na gari da sai na bashi motata ya kaiku domin na gamsu da tukinsa. Amma babu yadda za'a yi Faruku ya ja mini mota".
Yaya Faruku ya bata fuska ya ce "Baba kana bada ni a gaban Abida, domin Bilkisu a nutse take."

*MalaysianFabrics*
*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*
*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*
*7020695644.*
Chapter 11 · 0% Book details