← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin abin da yake debe mini kewa har da koyarwa da nake yi.
Yana cikin abin da yake samar mini da nutsuwa na manta damuwowin da nake kwana na yini a cikinsu.
Yau har yamma ina cikin makaranta dan haka na biya na dauko yara tunda suma sai after biyar suke tashi a ciki suke islamiya.
Tun kafin na yi horn maigadi y a bude mini katafaren gate din gidan namu.
Kafin na kammala tsayar da motar ya fito yana danne danne wayar da ya zame masa ka'ida da dabi'a.
Yadda yaran suke masa hugging suna fad'in "We are back Dady, sannu da gida".
Suka shige da gudu, nima haka ya karaso ya rungume ni tare da karbar jakar hannuna yana fad'in "Welcome dear".
Na amsa da murmushi da ce wa "Thank you!
Tare muka shiga cikin katafaren falon.
Kaitsaye dakina muka nufa. Ya shiga taya ni cire tufafin jikina.
Abin wuya ya cire mini. Ya zuge zif din doguwar rigar atamfar da take jikina. Wanda dinkin ya yi matukar zauna mini tamkar y'ar shekaru talatin.
Na yi saura daga ni sai bra da pant da siket.
A maimakon ya tsikari kirjina kamar yadda aladarsa take sai kawai ya koma gefen gadon ya kishingide tare da mayar da hankalinsa kan wayar da ta sake zame mini tashin hankali a rayuwar aurena.
Na sake yin jarumtar mazewa na shiga wanka.
Har na fito na shirya bai ankara ba, don kuwa ya riga da ya yi nisa a sabon shafin da ya bude.
Duk yadda na so na cigaba da jarumtar cigaba da kawar da kai akan lamarin wayarsa abin ya ci tura.
Dan haka na fara tunanin lokacin da zan shammace shi na dauka. Tabbas sai idan yana barci cikin dare. Domin yana cikin jerin mutane masu nauyin barci.
Haka duk tsananin rudani da tashin hankali baya hana shi barci.
Ba jimawa suka fice zuwa masallaci shi da Faruk.
Gabadayanmu da yara muna falo, maimakon ace muna hira cikin farin ciki da walwala.
Amma kowa da wayarsa a hannu yana nausawa cikin yanar gizo.
Ogan nafi zaton chart yake yi da wacce take birkita shi. Ni kuwa ina cikin group din mu na old girls muna tattauna yadda taron reunion din da zamu yi zai kasance.
Amrah kuwa bincike take yi tana aikin gida akan wani darasi da aka yi musu a makaranta aka kuma basu aikin gida a kai.
Yayin da Faruk yake yin game. Farha kuwa hankalinta na kan tafkekiyar allon talabijin din tana kallon katoon.
Na ajiye tawa wayar ina nazarinmu gabadaya. Jikina ya yi sanyi yadda waya take lashe mana dukkan lokutanmu. A shekarun baya a lokacin da yaranmu suke kananu sosai waya bata shiga jikinmu irin haka ba. Amma a yanzu mafi yawan mutanan wannan karnin sun fi girmama sha'anin waya fiye da komai.
Na saki ajiyar zuciya na ce "Daddy, Amrah, Faruk, Farha dinner is ready".
Na mik'e na nufi dining din. D'ayan bayan d'aya suka biyo ni har muka hallara.
Kowa da kansa ya yi serving kansa as usual.
Mun ringa mun saba da rashin magana idan ana cin abinci dan haka ba a jin komai sai karo tsakanin tangaran da tsokali.
Mun kammala aka fara kiran Isha. Dan haka muka hau haramar yin sallah, yayin da Daddy da Faruk suka sake ficewa zuwa masallaci kamar yadda suka saba.
**
Dare ya yi nisa. Na mirgina na tab'a shi na tabbatar ya yi nisa. Sai kawai na lallaba na zaro wayarsa da take karkashin filonsa.
Jikina na bari na fice zuwa falo bayan na mayar da tawa wayar gurbin da na zare tasa.
Na zauna a bakin kujera, na fara kokarin cire password din, na rubuta sunana da babban bak'i *BILKISU* amma bata bude mini ba. Na sake rubuta *Bili* nan ma bata bude ba.
Kaina ya kulle yaushe ya canja? Na tambayi kaina a rude.
Na yi jim ina nazarin me zan saka ta bude mini domin ina jin tsoron kada na cike adadin da zata ki buduwa gabadaya.
Da zullimi na rubuta *B Funtua* nan ma bai bude ba. Cikin sa'a na sake rubuta *Faruku Sm* sai ta budu.

*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750

Zuciyata ta buga da sauri. Na lalubo manhajar Whatsapp dinsa nan ma na tarar ya sanya masa tsaro. Na sake rubuta wanda ta bude mini waya. Sai bai bude ba.
Na rasa yadda zan yi.
Kawai sai na rubuta lambar wayarsa. Ai kuwa ya bude.
Ban kunna data ba. Dan haka na fara duba last contact din da ya yi magana da su a wannan daren kafin ya kwanta.
Suna d'aya ne ya ja hankalina kuma shine na karshe da ya yi magana da shi .
Na maimaita sunan a hankali *Hawwah*.
Zuciyata ta sake tsananta bugu. Na bude na fara bibiyar hirarsu. Babu wani abu na assha, amma maganganun da suke tattaunawa suna alamta cewa sun dade a tare. Sun kuma fad'a cikin matsananciyar soyayya a tsakaninsu. Sannan na fahimci gabadaya kudadensa a kanta suke karewa ni kuma ya bar ni da hidimar rik'e masa gida da shi kansa.
Mafi kankantar kudin da yake tura mata da na shiga text messages din da banki suke yi masa dubu ashirin ne.
Na fahimci tun yanzu shi yake yi mata komai na rayuwa. Maganganun ta suka fahimtar da ni yarinya ce k'arama wacce da kad'an ta girmi Amrah.
Wata magana da ta ja hankalina da na ga ta ce masa yau na ga matarka bata da kuzari.
Ya bata amsa da fad'in bansan me ya same ta a tsukun nan ba.
Ita ba yarinya ba, ba zata fad'i damuwarta ba, sai ana bin kanta. Sai kace yarinya sa'arku. Irin wannan rarrashin an yi mata itama, yanzu kuwa naku ne yara da za'a lallaba ku, a tarairaye ku.
Ta turo nasa imoji na dariya da na nuna soyayya.
Gumi ya dinga yanko mini. Ashe ma dalibata ce?
Wanne irin tozarci bawan Allan nan ya shiryo mini ne?
Anya kuwa na cancanci haka daga wajensa?
Hawaye ya kwace mini. Zuciyata ta yi nauyi, na fara tunanin wai da me na tsira ne a cikin wannan auren?
Sadaukarwar da na yi masa me ce ce ribata?
Anya kuwa zan iya zaman kishi da wata macen a karkashin ikon Baban Amrah?
A fili na furta ba zan iya ba, shima kuwa ba zai iya ba.
Tabbas cikin biyu dole d'aya ta kasance. Ko dai idan ya gama daukin amarya ya dawo mini, ko kuma ni ya sallama ni ya cigaba da more kuruciyarta.
Amma na sani, shima ya sani ba zai iya gamsar da mace biyu ba a tsarin halittarsa. Sannan nauyin aljihunsa ba zai rik'e masa gida biyu ba.
Hakanan ba shi da jarumtar da zai yi adalci a tsakaninmu. Dole akwai wacce zata janye shi a tsakani. Na rasa yadda zan yi da azababben kishin da ya tokare ni. Na tuna duk fafutukar aikin da nake yi ban ajiye komai nawa ba. Tunda rik'e gidan ni ce. Ban tab'a raba aljihuna da nasa ba. Komai tare muke yi, asalima sai da aka kai jallin da baya yin komai a harkar hidimar gida. Ban tab'a gajiya ko nuna kasawa ba. A yanzu da nake ganin zan samu sassauci da HALACCI ashe shi idonsa na kan yara k'ananu kusan sa'annin y'ar cikinsa.
"Da me na tsira ke nan ni Bilkisu?"
Na furta cikin rawar murya irin ta kuka sosai.

*Pay via*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.

*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
*08032773332*
*09069067488*

*Surayya Dee*
✍️
[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *DINGISHIN KWADO*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS.M.I.NASHE)*

2
*Lafazi writer's*

*Wannan littafin na kudine pay 1k via 2384876855 Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
#09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram ga wadanda suka biya kudi n karatu*.
*Na gode muku Allah ya saka da alheri.*

*Contact me 08032773332* *what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.
Chapter 3 · 0% Book details