← Book details Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 33

Sashe 17

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ya haɗiye bacin ransa ya ce "Amma ina ganin ke zan baki shekaru shida zuwa bakwai."
Ta ƙyalkyale da dariya ta ce"Ka girme ni tabbas amma da shekaru uku da watanni, ita kuwa Bilki babu watanin ma".
Daga haka kuma ta silale ta yi tafiyarta.
Takaicinta ya shaƙe shi a dalilin ya gano bata maraba da soyayyarsa da ƴar'uwarta shiyasa ta shigo da wannan rainin hankalin.
Ni kuwa gabaɗaya na kasa magana domin ina tsoron jidalin Abida idan mun koma hostel.
Amma gabaɗaya na ji babu daɗi yadda take yi masa iyashege mai cin rai. Gefe guda ina cikin zullumin kada ta kore mini shi, ni kam ko na girme masa ina sonsa a haka bare sarkin kankanba ta ce ya ba ni shekaru uku.
A matuƙar sanyaye ya ce "Dan Allah saka mini lambarki"
Tare da miƙo mini wayar hannunsa.
Na karba na sanya masa.
Na fara tafiya ya biyo ni yana faɗin "Yayanki ne ya kammala ko Yayarki?"
Cikin nutsuwa na ce Yayata ce"
"Wanne course ta karanta?"
Ya tambaya a gajarce.
"Law". Da matuƙar mamaki ya ce "Ya sunanta?"
"Munirah Musa Funtua".
Na furta cike da alfahari, domin sunanta ya yi fice a department din art and social secience gabaɗaya.
Da mamaki yake girgiza kansa yana faɗin "Munee sister ɗinki ce?"
Na ɗaga masa kai tabbacin eh.
Ya ce "Munee gifted ce ƙwarai da gaske."
Kafin na amsa masa sai gata, sanye cikin irin rigarsa. Ta ce S. Mashi kai kaɗai a nan?"
Tare nake da Bilkisu ƙanwarki, nifa na ga mata Munee".
Ta yi dariya tare da ce wa "Idan tana sonka ai shike nan".
"Idan bata sona ba zaki taya ni kamfen ba Munirah?"
Kai tsaye ta ce "Ni da ba ni zan zauna mata ba, kaga bai kamata kuma na tirsasa mata ba".
Ya ce "Hakane". Tare da sakin ajiyar zuciya.
Tare da yaya Munira suka shige cikin taron da alamu wani abu zasu yi.
Yayin da ni da Anisa muka koma cikin ahalinmu.
Sai yamma lis suka ɗauki hanyar komawa gida Funtua.
Yayin da Abida ta kaikaice take faɗin yau zuciyar sola sai Allah ta ga masoyinta.
Ban yarda na buɗe baki na tanka mata ba.
Amma matuƙar zamu zauna daga ni sai ita, zata kaikaice ta ce "Bilki yanzu sai ki amince da yaron nan? Na rantse miki fa da kad'an zai girmi yaya Munirah. Ya miki yaro da yawa, ga shi sololayi zubin makirai, kin ga Bilki ina raba ki da kisan mummuƙen namiji".
Ranar da ta fara faɗa mini wannan maganar na yi dariya ƙwarai da aniya domin yadda ta yi maganar tamkar wacce tasan kuttun ya'ya maza. Shi yasa a kullum ina tuna Abida sama da sau goma a rana. Domin komai ta faɗa mini a hankali nake ganinsu a cikin rayuwata, suna tabbata. Na numfasa na fashe da kuka ainun, sosai na yi kuka. Kukan da na tabbatar ba zan daina yinsa ba ila yau mil ƙiyamati sannan na cigaba da hakaito rayuwarmu tamkar a majigi.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

08

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*
Chapter 17 · 0% Book details