Sashe 18
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sanɗa da hila S.Mashi ya shiga jikina. Domin wata irin kalar soyayya yake gwada mini mai tsayawa a rai yana kirana sama da sau biyar a , kullum kuma sai ya zo ya ganni, al'amarin da nake mamakinsa, ina yawan tambayar kaina shi bai tafi gida ba ne ko kuwa?
Ashe a Zaria yake zaune gidan Baffansa wan mahaifinsa wanda prof ne a jami'ar. Haka nan a cikin quarter's din makarantar suke zaune.
Sanadina ya sanya bai tattara ya tafi gida Katsina ba tunda ya kammala
Asalin su Sahal ƴan asalin ƙaramar hukumar Mashi ne.
Mafi yawa zuri'arsu ƴan boko ne wayayyu, sun kuma watsu a sassan arewacin ƙasar. Wasu na Kano, wasu na Kaduna, wasunsu na Katsina da Zaria, wasu kuwa na Abuja da cikin Mashi.
Sannan mafi rinjaye su farare ne ƙal masu zubin sadaka yalla, domin duk fadin Mashi da kewaye idan ka ce gidan jajaye yaro da babba yasan gidan ake nufi.. An tabbatar asalin tushensu na Agadaz ta ƙasar Nijr. Kakannnsu daga can suka fito, kowa kuma yasan alaƙar mutanen jihar Katsina da Nijer.
Mahaifinsa na cikin waɗanda suke zaune a Katsina.
Tun Abida na kushe da nuna adawarta akan S.Mashi har ta haƙura ta zuba minu ido a dalilin watarana da ta ganmu tare a Libry muna hira.
Ta kasa kawaicin ɗauke kai ta iso gabanmu ta ce "Wai ko yaushe kuna tare kenan?
Ya zo da safe, ya zo da rana, ya zo da yamma, yanzunma da daddaren sai kun haɗu?
Amma ai kinsan ba'a barinmu hirar dare a gida ko?"
Na kasa ce mata komai domin gaskiyar magana ta faɗa mini.
Ta numfsa ta ce "Sahalu ta kasa faɗa maka dokokin da aka sanya mana kafin a barmu mu zo makarantar nan. Dan haka zan faɗa maka domin ni ɗin jakadiyar iyayenmu ce. Tsakanina da Allah kana ɗagawa Bilki hankali. A yanzu ne ta shiga aji biyu. Tunda ka shigo rayuwarmu gabaɗaya ka ɗauke mata hankali daga karatun da ta baro gida dominsa, alhalin kai ka kammala naka tare da Yayarmu da muke makwabtaka da ita wajen haihuwa. Kada ka kuma zuwa wajenta a ranakun litinin zuwa juma'a, sannan haramun ne zuwanka a irin wannan lokacin. Bayan haka mu dokace ta dole sai mutum ya bayyana gaban dattijaanmu ya gabatar da kansa tare da neman izinin magana da ƴarsu".
Cikin takaicin yadda take nacin jingina masa fikon da ya yi mana bai kai ya kawo ba, ya ce "Na ji Abida a kuma cikin satin nan zan je Funtua na nemo iznin, na gode da tunatarwa".
Daga haka ya miƙe ya tafi babu sallama. Ta zauna kusa da ni bayan ta ja ƙaramin tsaki. Tunda ta zauna ba abin da take yi sai yaɓa mini baƙaƙen kalmomi. A matuƙar tunzure take faɗin kin faɗo da yawa. "Ina rantse miki Bilki da wannan sololayin gara miki auren Yaya Faruku mai mata da yara, gara miki yaya Asad duk da yadda ya baki tazarar shekaru masu nauyi. Yaya Usman ya yi ta nuna miki soyayyar da babu algus kina tankwabewa sai kuma ki buge a auren wannan abin? Wai ko dai kina da raunin fahimtar abu mafi kwanciyar hankali da dacewa ne?
Ki ture waɗannan da suke cikinmu guda ni da su, wataƙila zuciyarki ta kisima miki ina da son kai, me yasa kika ƙi bawa tarin masoyanki dama sai Sahalu da idan ya kai shekarun ganiyarsa zai ga tsufanki?"
Daidai wannan gabar ma sai da na kasa riƙe hawayena. Hakikanin gaskiya Abida ta soni ta yi dukkan iyawarta ta yakice mini shi a rayuwata amma ina?
Domin ya iya shirya zakakkun kalmomi, ya iya ririta zuciyar mace, bugu da ƙari kyakkyawan ne na gaske, irin wanda nake so.
Jin na yi shiru ta tunzura ainun ta ce "kyawunsa ne yake rudarki, amma da ace kin kula da kyau da kin gane ba shi da kyau, domin dukkan kyawunsa irin wanda yafi zama abun burgewa ne idan mace ke da shi. Fari dogo, mai kyawun fuska. Sai dai a lankwashe yake tunda bashi da siffofin karfafan maza, na rantse miki ba zai iya yin gwagwarmayar rayuwa ba, ina jiye miki gararin rayuwa! Ni fa ko ina da rai ba zan baki kafada ki yi kukan kuttun Sahalu ba. Domin na faɗa miki tun tafiya bata yi nisa ba, amma dan jaraba kin kasa fahimtar manufata.
Haka kawai na fara mata kuka ina faɗin "Ki yiwa Allah ba dan ni ba ki daina jingina masa yarinta akan idonsa, baya so, baya jin daɗin al'amarin. Dan Allah Abida kada ki sake kore mini shi ".
Na ƙarasa cikin kuka na sosai. Tsawon lokaci ina mata kuka yayin da ita kuma ta kasa ko da kwakkaran motsi. Can ta numfasa ta ce "Wato duk abubuwan da na faɗa ke ko saurarensu baki yi ba, balle na saka ran zaki fahimce ni?"
Ta fesar da iskar baki tare da ce wa "Well! Idan Allah ya ya yarda ba zan kuma jingina masa ƙuryciya akan idonsa ba, amma ki sani har duniya ta naɗe a idona yaro ne ƙanƙani da bai fi ki aike shi a matsayin ƙanin mijinki ba. Amma tunda bansan gaibu ba, bansan dalilin da yasa aka jefa miki sonsa ko na ce kika jefawa zuciyar ki ba, na ajiye makamaina, amma ki sani babu ke babu kawo mini matsalolinsa, ke bama za ki ga fuskar tunkarata da kalubalen Sahalu ba. Domin Allah ne shaidar yadda nake jinki a zuciyata da kuma yadda nake guje miki artabu anan gaba. Babu damuwa na daina adawa da soyayyarki da shi tunda kina cikin jerin mutane masu son mutum a kallon farko ba tare da nazari ko tsinkayen halayyarsu ba. Fatan alheri amma ki sani matuƙar kuka cigaba da hirar dare zan bugawa Baba babba waya na faɗa masa kin yi bara'a da kyawawan turbobin da suka ɗora ahalinsu a kai. Sannan tabbas idan mun koma zan siyar musu jarida mafi tsada domin kuwa zan fayyace musu gaskiya da gaskiya cewar aure kike so dan haka su aurar da ke, sai ki kammala karatun a dakinki domin ni ba zaki dinga sanya ni cikin zullumi da fargaba ba, alhalin karatuna na matuƙar buƙatar nutsuwa."
Na yi shiru tare da goge hawayena domin na yi matuƙar samun nutsuwar zata daina gwanya masa, sannan ban ji damuwa ba dan ta ce zata faɗa a mini aure.
Ta yi ƙwafa tare da ce wa "Kina da kayan kuttu sola!
Daga haka ta buɗe tafkeken littafin gabanta wanda modern Biology ne ta hau bita cikin nutsuwa.
Yayin da ni kuma na bude littafin()sai dai bana fahimtar komai. Gabaɗaya nutsuwa ta yi mini tutsu, ba dan komai ba sai dan Ubangiji ya sanya albarka a harshe Abida a gaban iyayenmu, idan ta yi shaidar abu gabaɗaya suna raja'a domin ita ɗin bata iya ƙarya ba, a tsaye take tamkar nonon maza akan komai, idan ta ce zata yi abu ko zata faɗa to tana nufin har zuciyarta hakane. Bayan haka na hango da gaske take da ta ce tana cikin zullumi akan yadda na daukaki Sahal. Gabaɗaya rauni ya kamata a dalilin kukan da na yi mata.
Tunda ga wannan rana Abida bata sake tisa ni gaba tana kushe Sahal ba, sai dai kuma bata ba ni ƙofar da zamu dinga maganarsa ba, nima kuma ganin yadda ta kame daga yawan takura ni, sai na warware na daina takura kaina na rungumi karatu domin dama faragabar kada ta kore mini shi ta hanyar yi masa isgili ne yake kiɗima ni. Amma a yanzu na wartsake tunda na sani ita ɗin bata faɗar magana da zummar waƙe.
Nutsuwar da na shiga da kuma takaita zuwan Sahal sai ya samar mana da daidaito a tsakaninmu.
Ta daina musguna mini, ni kuma na mayar da hankali wajen karatuna.
A haka muka zana jarabawar zangon ƙarshe. Muka tafi hutu gida, wanda dogon hutu ne na watanni kusan uku.
A ranar da muka isa gida Abida bata bari mun kwana ba ta zayyanewa Baba babba halin da nake ciki, a kuma gabana da muka je gaishe shi.
Ya nunfasa ya ce "Alamun al'amarin daga Allah ne tunda wanccan karon kin toshe hanyar da zasu haɗu amma cikin ikon Allah sai ya sake haɗasu. Dan haka ki taya ƴar-uwarki da addu'a kawai, sau tari muna ƙin abu sai abu ya zamo alheri, abinda muka raja'a akansa kuma sai ya shayar da mu mamaki."
Wata irin salama ta shige ni, domin na yi zaton Baba zai ce sai mun kammala karatu ko kuma na zaba aure ko karatu.
Cikin taushi ya cigaba da ce wa "Ai ya turo ƙanin mahaifinsa ya nema masa iznin magana da ita, mun kuma amince. Tare muka yi Barewa College da iyayensa. Ni ajinmu ɗaya da wan baban nasa, mahaifinsa kuwa ajinsu ɗaya da Baba ƙarami. Mutanen kirki ne zuri'arsu basu da aibun da za'a guji haɗa iri dasu. Namiji ai baya kaɗan Abidan Baba. Ta ya Bilkisu son abin da take so."
Kunya ta kama ni, na yi ƙasa da kaina ina jin farin ciki na ratsa ni.
A sanyaye Abida ta ce "Shike nan Allah ya tabbatar da alheri."
"Ameen ameen Abida! Ke ma Allah ya fito miki da naki mijin duk sai na haɗa na aurar da ku rana ɗaya".
Da azama ta ce "Na roke ka Baba ka bar maganar nan haka. Bilki ta samu miji, ta kuma amince a yi mata aure. Ni kuma ban samu ba, ko na samu ma sai na kammala karatuna, dan Allah kada maganar nan ta yi tasiri a zuciyarka, ita dai da ta ga zata iya to a yi mata auren ta, Allah ya bata sa'a".
A sanyaye ya ce "Ameen".
Daga haka ya sallame mu.
Duk wanda ya zo gidan sai ta bashi labarin halin da ake ciki.
Yaya Faruku kuwa da ta bashi labarin ya zuba mini ido ya ce "Da gaske dai kin fasa yi da ni ko Bilki? Anya alkawari ya ce haka?"
Na yi murmushi tare da sunkuyar da kaina ƙasa.
Yaya Munirah kuwa addu'ar fatan alheri ta yi ta kame bakinta daga tofa komai. Amma kuma bata armasa al'amarin duk da ta san Sahal sosai tunda shima law din ya karanta.
Satinmu biyu da yin hutu yaya Asad ya turo da direba ya kwashemu zuwa Anambara dukkanmu uku. A wannan lokacin matarsa na da tsohon ciki. Mace mai kirki da haba haba da mutane. A wannan lokacin haihuwarta hudu duk mata zata yi ta biyar sai ta daya ta raayi bara.