Sashe 10
Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saurayine ya bata lambarsa akan ta nemi shi, shine ni kuma na yaga takardar kin ji sanadin kukan da take yi. Yaya Salaha ta yi jim domin bata tab'a zaton yadda nake very silent har zan fad'a tarkon soyayya tashi guda haka ba. Mussaman da ni ko karance karance bana yi. Abida ce kullum cikin fakar idonta take tana debo littafan Hausa a dakinta tana raba dare wajen karatun. Ta numfasa ta ce "Share hawayenki, Bilkisu, rabu da Abida.". Abida ta yi maza ta ce "Idan an k'addara mijinki ne zaku sake haduwa, amma ni ban miki sha'awarsa ba zubin majununai ne da shi". Yaya Salaha ta d'auki salati tana ce wa "Oh ni y'asu ke Abida wacce irin yarinya ce tun baki tafasa ba zaki kone? Har kinsan kalolin mazaje? Har kina iya banbance na gari da kuma majununi?" Ta yi dariya ta ce "Allah kuwa Yaya ina ganinsa na ji bai mini ba, da ace d'ayan da ya nuna yana sona ne yake sonta da ba zan yaga takardar ba, domin ya yi, kyaunsa kad'an ne, sannan mai wararren kai ne, haka nan bak'i ne. Amma Sallau yake ko wa? Fari ne tamkar tsada, ga kuma alamun izza tare da shi. Sam sam zuciyar Bilki bata dace da wannan ba, domin artabun da zata yi da y'an mata ba kad'an ba ne". Mamakin Abida ya sake daskarar da Yaya a tsaye. Ta ce "Ke mai ya hana ki so wanda ya nuna yana son na ki tunda kin tabbatar shi ba munafiki ne ba?" Ta yi dariya ta ce "Ban shirya aure kusa ba, dan haka bazan bada k'ofar da za'a zo gidanmu da sunan ana sona ba, hakanan ba zan yi gangancin fara soyayya a yanzu ba.". Yaya Salaha ta gwale ta da fad'in " To uwar iya. Idan ke baki shirya aure yanzu ba, kada ki sake toshewa Bilki hanyar samun samari. Ina ce bana zaku kammala sakandire, idan ta samu tsayyaye wanda ya shirya ita aurenta zata yi ba zata zauna ta tsufa da sunan karatu ba. Allah bar shi sai ta cigaba da karatunta a dakinta." Ta ce "To shike nan ba zan sake ba, ta kallo ni ta ce "Sorry Bilki solar soyayya". Yaya Salaha ta ce "Allah ya shirye ki kawai Abida." Ta matso kusa da gadon da nake kwance ta ce "Yi hak'uri kin ji Bilkisu. Tashi ki yi alwallah an fara kiran sallah. Sai kuma kunya ta rufe ni haka siddan. Na kasa koda motsi, yayin da ta juya ta tafi a dalilin ringin din da wayarta ke yi daga falo. Abida ta saki gauron numfashi ta ce "Bilhillazi shiyasa jinimu bai jitu ba, yanzu yadda kike sokokuwar nan ashe abin da yake zuciyarki azim ne, ke ce da kuka akan wanda yau d'aya tak kika d'ora idonki a kansa?" A sanyaye na ce "Kin ga Abida bana shiga shirginki irin haka, kin fitinane gaskiya, ina ce kin yaga takardar kin jefar? Na ro'ke ki, ki shafa mini lafiya pls and pls". Bata kula ni ba, ta dauko littafin HAMIDA na Maryam Kabir Mashi ta hau dubawa sai kuma ta kallo ni ta ce "Sai na ga kamar S.S Mashi ya rubuta ko?" Ban kulata ba na mike na shige bayi domin na sani idan ba wuri na bata ba, tana iya sake sa ni sabon kuka. Ilai kuwa da na fito daga bayi ta bini da ido ta ce "Da kika share ni kanki kika yiwa asara. Niyya na yi a turo mini lambar Anty Maryam Mashi tunda marubuciya ce na sayi shafi d'aya a cikin littafinta na gaba da zai fito kasuwa a yi miki cikiyar S.S Mashi. Nasan da wuri za'a samo shi tunda garinsu d'aya. Watak'ila ma wata cikin danginsu ta ga cikiyar tunda mata mun raja'a a karatun littafi". Na ja dogon tsaki na tada salla na kyale ta. Ita kuwa ta fashe da dariya mai hade da ihu ainun tare da ce wa ",Oh ashe sola macijin sari ka nok'e ce, ana miki kallon salaha nutsatssiya ashe abin da yake ranki kabiran ne. Bilhillazi gwara ni sau milyan da nake fito da zahirina a fili. Haba ai kina cutata Wallahi. Ana ta miki kallon hankali, ni kuma ana mini kallon buzu buzu saboda kawai ban iya nunkufurci irin na ki ba. Komai na ki kunbiya kunbiya, ni ban da gayunki da tsananin son turarenki ban ga me kike yi mai kyau ba ". Har na idar da sallah bata daina zungure zunguren magana ba, har da fad'in tafi kowa shan wahalar rayuwa a gidanmu tunda ni da muka taso tare zuciyata mai fad'i ce, ana mini kallon tausayin ta matsa mini ashe ingiza mai kantu nake yi mata a wajen jama'a, na barta tana ta bankaura tare da harigido, yau Allah ya bayyana mata gaskiyar lamari. Tsananin tisa ni a gaba da Abida ta yi akan maganar S.S. Mashi ya sanya na ware na daina tunaninsa akan dole. Har zuciyarta kuma na fahimci bai yi mata ba da gaske. Bamu koma Funtua ba sai ana saura kwanaki biyar hutunmu ya k'are. Muna sauka a mota da Baba babba muka fara yin tozali. Sanye yake cikin farar jallabiya fara kal haka hular kansa ma fara ce irin ta larabawa. Idonsa sanye da farin gilashi. A tsaye yake cak, duk da ya tsufa amma yana nan da k'arfinsa garau dan kuwa da mai ra'ayin aure ne sai ya auro yarinya k'ankanuwa tunda da kudinsa. Ban ankara ba na ga Abida ta fetsa ta isa gare shi. Shi kuwa ya mik'a mata dukkan hannunwasa yana fad'in lale da Abida k'anwar Bilkisu." Ta kame baki ta ce "Ai Baba na zo maka da sabuwar jarida mai dad'i nawa zaka siye ta?" Ya murmusa ya ce "Na siye ta da d'awisu" Daidai lokacin na kariso na tsugunna ina gaishe shi, ya miko mini hannunsa guda na rik'e nima. "Cikin kanzagi ta ce "To Bilki dai ta yi kasuwa ta samo wani irin mutum da kiris ya rage ya shiga sahun zabiya ta makance a kansa, gara tun wuri ka sani babu ajandar karatu a wajen ta." Tana rufe baki ta falfala a guje ta yi cikin gida. Yayin da na yi k'asa da kaina ina jin kunya da nauyi suna mini kawanya. Ya sassauta murya ya ce "Mai gadon zinare da gaske kanwar ki take yi ko kuwa shegantakarta ce?" Murya babu amo na ce "Yaya Salaha ce ta aike mu gidan inlaws dinta, sai suka tare mu a k'ofar gidan, d'aya ya ce ni, d'ayan kuma ya ce ita." Ya murmusa ya ce "Ashe har da ita ma ta yi kasuwar?" Na sake sunkuyar da kaina kasa ban amsa ba. Ya ce "To sai kuka yi ya ya?" A hankali na ce "Ita ta ce ba zasu shirya ba domin karatu zata yi mai yawa. Ni dai ban yi magana ba, amma ya ce na ba shi lambar wayata, na ce ba ni da waya, shine ya rubuta mini tasa." Ya numfasa ya ce"idan kin nutsu ki kawo mini lambar ". Murya babu amo na ce "Abida ta yaga tun a ranar". Da azama ya ce "Saboda me?" "Ta ce siffar munafiki ne da shi, sannan tunda fari ne bai yi ba". Dariya ta sosia ta kama Baba ya ce "Allah ka shirya Abida." Ya ce "Ki yi hak'uri, idan daga Allah ne zai kawo dalilin da zai sake had'aku. Sannan duk wanda ya nuna yana sonku lallai lallai ku turo shi gidanku ya nemi izinin magana da ku. Tashi ki shiga, ki fad'a mata kuma bata ci kyautar d'awisu ba". Na yi murmushi na ce "To ni kuma da na fad'i gaskiyar magana fa Baba?" Ya ce "Kin ci kyautar talo talo sai ki soya ki tafi da abinki makaranta." Da murna na ke yin godiya. Sannan na isa cikin gidan. Bangarensu Abida na fara isa, abin farinciki na tarar da Yaya Munira ta zo hutun mid semester. Da gudu na rungume ta ina jin farinciki har cikin zuciyata. Na sake ta muka zauna muna gaisawa sosai. Abida ta fito daga bayi tana fad'in Yaya Munira na siyarwa Baba jaridata ta yau, amma me za ki ba ni na fesa miki?" Cikin sace iska Yaya Munira ta ce "Rik'e abar ki dan kuwa ba ni da abin bayarwa." Domin al'adar Abida matukar ta baka labari sai ka biyata, shiyasa tafi kowa y'an canji ko abin dad'i. Yayyenmu maza Abida guntsi fesa suke ce mata, kuma ko a kwalarta, haka nan idan ta fad'a maka abin da baka sani ba, baka biya ba, to ta ringa yi maka bak'in naci ke nan, ko ta dauke wani abu naka mai muhimmanci, shiyasa Yaya Munira bata yarda ta sayi jaridarta, dan kuwa k'arshe sai dai Momi ta biya ko Baba ya biyata da kaza ko tattabaru. Shiyasa ita kad'ai ce mai dakin kiwo a gidanmu. Daga can bayan gidajenmu aka yi mata dakunan kiwon tattabaru da na dabbobi. Wato Abida kes ce babba. Kowa kuma ya sani ta shiga ran Baba babba ainun, duk da yana iyakacin k'ok'arinsa wajen dannewa baya ware ta ya fifita ta. Amma matukar ta murde akan ta siyarwa wane ko wance jarida ba'a biyata ba, to fa dole Baba ya bata auren tattabaru, ko kuma ta tubure sai tunkiya shiyasa ta had'a nata garken. Ban da haka ko labarin littafi bata yinsa a banza siya ake yi. Ta kan ce ba zai yiwu ta zauna ta bata lokaci ta yi karatu ba, sannan ace ta bada labari a bagas ba. Ba ta yi arahar hakan ba kuma zata zama haka ba.