Sashe 8
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi a saitin wurin da ta fito, ta babbake dan kar a hango Fatima dan har rigar Fatima ta an le o sai dai fatan kar Hajiya ko an rakiyarta ta su gani.Wurwurga ido ta shiga yi kana ganinta ka san bata da gaskiya da ma an magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. "Keee Nasira! Shin wai dodanniya kika aukeni da duk lokacin da za mu ha a hanya da ke sai kin uya ko kuma kike sinne kai, kai wani lokacin ma ina tahowa kike sauya hanya ko kin auka ba na sane da ke yanzu ma na hango shigarki ma oyarki wato ga aljana kin gani" Wata bayyananiyar ajiyar zuciya Nasira ta sauke, wacce da Hajiya ta lura sai ta yi zaton al awarin yanka Nasira aka yi aka fasa saboda irin ajiyar zuciyar da ta sauke mai arfi. Idanu Nasira ta rufe tare da ware su cikin sauri tana ta ari harha a kalmomin da za ta yiwa Hajiyar bayani, dan ba aramin da i ta ji ba jin Hajiya lokacin shigarta cikin flower ta ganta, bata hangosu suna tahowa ba, Allah ne ya rufi idanunta ba ta hango Fatima ba. "Ba da ke nake magana ba" Cewar Hajiyar cikin acin rai. "A'a ba haka bane Hajiya dan Allah ki yi ha uri, kawai dai ina ratse miki hanya ne dan baki girma da kuma matsayi, saboda rumfa sha shirgi kike, sannan kuma sawun giwa ya taka na ra umi ba na so mu ke ha a hanya da ke dan ba girma da matsayinki bane ha a hanya da mu iyan talakawa wanda muke samun mafaka daga arzi i da aukakar da Allah ya muku" Cewar Nasira cikin girmamawa. Wani murmushi ne ya bi ta kan acin ran da ke kwance a kan fuskar Hajiyar har ha oran makarta guda biyu da ke jikin manyan ha oranta na gabasuka bayyana, wani da i ne ya ziyarci ran Nasira dan ta lura ha arta ta cimma ruwa da ma babu abin da Hajiya Mariya ke so sama da a ko a ta a wasa ta tamkar wu a a wurin washi. "Allah sarki ar nan ai ban san haka bane, jeki abinki ai da ma bin na gaba bin Allah"Ta fa a tare da juya wa ta kalli an aikin nan nata guda biyu ta ce "To iyayen gulma da tsigudidi da baku san girmama na gaba ba saboda tarbiya bata isheku ba kuka tsatstsareni da ido" Saurin sadda kan su asa suka yi dan sun san yanzun nan ran su in ya yi dubu zai aci in ma ba a raba su da aikin su ba saboda korar ma'aikaci a gidan ba abu bane mai wahala. "Godiya nake Hajiya Allah ara girma" Nasira ta fa a tana juyawa ta an fara tafiya domin barin wurin dan bin umarnin Hajiya Mariya, ganin idanunt basa wurin da Fatima ke oye bare ta ankara da rigar Fatima da ta an fito. Gaba ta yi cikin izza da ta ama suka nufi angaren Hajiya Nuratu.Nasira ganin sun sha kwana ta dawo ta ce Fatima ta fito su tafi.Sai da suka shige get angaren Hajiya La ifa sannan suka tsaya suna maida numfashi tamkar wanda suka yi tseran gudu. "Mu yi sauri mu tafi cikin gidan Hajiya kar wata daga cikin an aikin angarenta su gan mu kin san kowa yana iya yin komai a kan ku i, bar ganin an aikin angaren Hajiya La ifa ne a ciki wallahi muddin suka gan mu sai sun fa a saboda irin tarin alherin da aka yi al awari za a baowa wanda ya kawo cewa wani ba o ya shigo gidan nan.Dan duk wanda kika gani a cikin gdn nan to mutanen gidan ne ko kuma masu yiwa mutanen gidan hidima amma bayan su ba a so kowane bare ya shigo cikin gidan nan" "Saboda me??? Kuma menene dalilin su na yin hakan?" Fatima ta jefawa Nasira tambayar dan bata so t nunawa Nasira cewar ta san dalilin yin hakan duk da ba komai t sani ba dan ta lura abin yanzu ya zarce wanda ta sani. "Ba mu da wani lokaci mu tafi kawai, za ki ji dukkan komai daga bakin ar uwarki" Nasira ta fa a tana kama hannun Fatima suka nufi cikin sashen Hajiya La ifa. Beelal tun da aka rufe get in nan yaron ya tsaya abin tausayi, sai waige-waige yake dan Mai tsaron ofa ko ta kan sa bai bi ba saboda yana tsoro sannan yana jiran kiran Hajiya La ifa ta bada umarnin yadda za a yi da yaron. A gefe aya ma dai babbar rashin nutsuwar da ke tattare da shi rashin sanin su Nasira sun tsallake rijiya da baya ko kuma shin afka ciki. Tagumi Beelal in ya zabga da hannunsa mai lafiyar yana ta tunanin halin da Mamarsa take ciki duk da yaro ne amma ya san dai Mamarsa na cikin wani hali dan yana jin irin wayar da ake bugowa Mai tsaron ofa da yadda ya ga duk hankalin kowa a tashe amma Mamarsa an tafi da ita. Yana nan tsaye sai ya hango wani kare ya fito daga cikin wani get da ke gaba da gidan da suka zo.Ganin karen ba irin da jajayen idanu hakan ya sanya Beelal jin wani mugun tsoron karen gashi unguwar ta masu hannu da shuni ce babu kowa a layin kowa yana cikin gida, idanun Beelal ne suka kawo ruwa ganin karen kamar ma wurinsa ya nufo ga wata sar a a afar karen da gani a aure yake ya cire aurin ya kamo gabansa.Kafin karen ya araso Beelal ya fara waiwayen wurin da zai shiga ya oye saboda kar karen ya cutar da shi dan babu afar da zai ceci kan sa wajen gudu saboda yadda afar guda aya take kamar a shanye sannan kuma a lan washe. Ganin babu wurin da zai fake hakan ya sanya ya matsa jikin get in gidan da suka zo ya shiga bubbugawa dan ko Mai tsaron ofa zai kawo masa auki ya taimaka masa, bugun yake da hannun hagun insa mai lafiyar dan ayan na daman shi ma a lan washen yake. Mai tsaron ofa kwa yana jin bugun ofar kuma ya san Beelal ne ke bugawa, amma bai yi wani yin urin bu ewa ba, saboda bai san ya mai zai cewa yaron ba kuma yana gudun tonuwar asiri kar wani ya ga yaro a zargeshi da wani abu dan shi wallahi bai shirya rasa aikinsa ba wanda yake taimakonsa wurin taimakon iyaye da iyalansa.Dan haka mirsisi ya yi tusar ango amma a ransa tausayin yaron ne fal. "A...a...bu... e...min...ga ...ga... ka...ka...re nannnn" Ya fa a da fashewa da wani kukan mai ban tausayi. Jin kalamansa ya sanya Mai tsaro ofa nufo ofar da niyyar taimaka masa amma kuma sai ya hango aya daga cikin ma'aikatan gidan ya nufo wurinsa hakan ya sanya ya dakata, amma a ransa ji yake kamar ya bu e ya akko yaron ko ma mai zai faru ya faru. Beelal kwa da ke ta bugun ofa jin ba a bu e ba ya ce "Wayyo Allah na" Cikin in'innarsa. Cikin ikon Allah sai ya hango wasu samari guda biyu sun fito daga gidan da karen ya fito sun taho a guje, karen kuwa hangosu da ya yi sai ya fasa nufar wurin Beelal ya mi e kwalyar layin a guje, samarin suka mara masa baya.Dur ushewa Beelal ya yi a wurin yana maida numfashi har lokacin tsoro ne fal a cikin ransa dan ya mugun tsani kare. Yana a hakan ya hango samarin nan sun dawo da karen nan sun kamo shi, suna zuwa za su wuce sai idanunsu ya sauka a kan Beelal wanda ficewarsu azu basu lura da shi ba saboda hankalinsu na a kan karen nan. "Kai ji wani yaro kyakkyawa da shi" ayan wanda ke ri e da sar ar da ke aure a wuyan karen ya fa "Kai wannan yaro kamar ba a Nigeri'a ba" Cewar aya, yana juyawa ya sanya bakinsa a kunnen ayan ya masa ra "Baabaa yaron nan fa mu tafi fa shi akinmu da gani zai yi da in harka ka dai gan shi arami babu zancen tonon asiri" "Kuma fa wallahi ka kawo shawara, da ganinsa bashi da galihu, mu kuma da ma irinsu muke so wanda iyayensu ke wasarere da su" ayan ya fa a yana yala dariyar mugunta. " Eh ai in har iyaye basa kulawa da yaransu to fa gayu ba za su yi asa a gwiwa ba wajen kai musu farmaki wala mace ko namiji, dan mu ba fya ananan yaran ba, ba kuma lalata a mazan ba" Cewar ayan lokacin sun araso wurin Beelal da ke dur ushe, yana ara tattakura ganin sun dawo da karen da ya firgitashi azu. "Ikon Allah Baabaa ai nakasashshe ne" aya ya fa a yana walalo idanu waje. "Dalla can kai fa gara ne, to ai ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba" Dariya suka yi su duka sai ayan ya ce an yaro ya sunanka, kuma mai kake a nan baka san masu gidan nan su suka aurewa jahilci tsantsa ba, basa son masu nakasa su ra e su ba amma ka zo ka zauna musu a ofar gida" "Zo mu je gidan mu ka zauna mu baka biskit da alewa har da madara" Cewar wanda aka kira da suna Baabaa. "Mamana ta fa a min kar in bi mutumin da ban sani ba, kuma kar wanda ya bani abu na kar a, kuma ko waye ya ce in bu e wandona ma kar na bu e kuma in fa a mata duk wanda ya yi hakan" Beelal ya fa a cikin in'innarsa yana kallon su. " Kai! Ka ga uwa mai tunani ko? Wato duk da ta barka wasarere ashe ta bar maka makaman da za ka ya i masu hali irin namu" Cewer ayan yana kallon aya. "Gaskiya na sarawa matar nan ko da ba warin kaifin ba, wato dai tana fa awa yaronta idan masu satar yara za su yaudaresa da alewa da biskit kar ya kar a, ka san wasu yaran idan aka ce mu je cikin gidan can in