← Book details Beelal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. *This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* *END OF BUK 1* Page 2 Gaba aya haka suka fito suka barbazu a bayan gidan ko ta ina sun kewaye, sai dubawa suke lungu da sa una na angaren Hajiya Nuratu. Fatima da tun lokacin da abin da ta taka saboda tsawon windown da yake daga asa akwai zurfi sosai take le awa ya zame ya yi ara, hakan ba aramin sanyawa ya yi hankalinta ya tashi ba, hakan ya sanya cikin zafin nama ta fara neman inda za ta uya waige-waige ta shiga yi hankali tashe dan maganar Alhaji ta sanya ta ji dama bata ma fito ba kamar yadda yayarta ta fa a mata amma ta tsallake maganar tata ta fito. Ganin in bat samu mafaka ba za su cim mata hakan ya sa ta hango wani tsohon tanki na ruwa da ke can bayan gidan wandaba a amfani da shi cikin hanzari ta auke murfin da yake yana da babbar ofa haka ta ajiye murfinta ta shige cikin tankin. gabanta na mugun fa uwa tana ta jin wucewar masu nemanta suna ta zuwa da dawo wa tatw da duba ko wane lugu da sa o na wurin amma cikin iko da hikima ta ubangiji babu wanda ya lura cewa wani zai shiga cikin tankin ya uya, dan su duk zatonsu ma arawo ne. Sai da ta ji sawu ya auke bata jin ko motsin mutum aya sannan ne fa ta lalla a ta fito gabanta na dukan uku-uku tana addu'a da fatan Allah sa dai kar asirinta ya tonu ko dan yayarra ma da bata ji ba bata gani ba. Wani uban zagaye ta yi kafin ta samu zuwa part in Yayar tata tana shiga kuwa ta haye sama ta je ta kwanta a kusa da Beelal tana sauke numfashi har lokacin gabanta fa uaa yake dan abu ne ya faru wanda bata ta a zaton faruwarsa ba. angaren Hajiya Nuratu* Gaba aya ma'aikatan gidan sun kara e gidan amma babu alamar wani ya shigo ma dan get in ma kamarbyadda mai tsaron ofa ya sanya atoton kwa o ya gar ame a haka aka samu get in babu da aka yi amfani da shi aka le o falo masifa sosai Alhaji ke yi yana basu san aikinsu ba, gaba aya sun yi tsit suna sauraronsa kamar su ne suka yi laifin a haka dai aka sallami kowa daga taron aka yi al awarin kyaututtuka masu tsoka da za a rabawa ma'aikatan gidan. Sallamar gaba aya ma'aikatan aka yi aka bar me gidan da matan gidan nan ma dai ya yi garga i da babban murya a kan kowacce ta kiyaye da dokokin gidansa kar a samu wata ta karya doka, sai ya ce zuwa wani lokaci zai iya barinsu su fita tun da matarsa ta haihu sai kuma zuwa gaba idan wata ta samu cikin ya tsufa dole dokar za ta ora daga inda aka tsaya. Haka dai kowacce ta tashi ta koma angarenta aka bar me jego da wacce ta kar i haihuwa da masu mata hidima na angarenta dan sai zuwa gobe ne ma za a bar iyayenta da wanda shi me gidan ya ga ya kamata ya barshi daga ckn an uwan su zo su ga me jegon da abin da aka haifa. HAJIYA LA Tun da aka ce an ji aran wani a bayan window hankalinta ya yi mugun tashi saboda ta san anwarta da taurin kai ta san duk iya garga in da ta mata ka an da aikinta ta fito, hakan ya sanya tun da aka fita duba waye ya le o gaba aya ta rasa nutsuwarta gabanta ke ta faman lugude tana addu'a a ranta Allah ya sa ba Fatima ba ce duk da zai yi wuya in ba ita in bace. Haka ta zauna cikin fargaba tana ta addu'a a ranta a kan Allah ya rufi idanunsu kar su ga wanda suke nema in har Fatima ce. Bata samu nutsuwa ba har sai da ta ga sun dawo sun ce basu ga kowa ba, sosai ta yi farinciki duk da ta san zai yi wuya su ga in har Fatima ce zai yi wuya su ganta saboda shegen wayo dole ta san za ta yi duk iya yinta domin ganin ta uya ko ta gudu ba tare da sun ganta ba. A hanya ma tana so su yi maganar da Nasira amma hakan ya gagara saboda tare da ma'ailatan angarenta suka taho dan haka babu dama sai ha ura ta yi da yin maganar. Sai da suka zo dai dai ofar da za ra sada su da angarenta ta sallamesu gabaki ayansu sai kuma ta ce Nasira ta biyo ta za ta sanyata wani aiki haka suka mata sallama kowa ya kama gabansa ita kuma da Nasira suka shiga angarenta, suna shigowa falo cikin tashin hankali ta fara magana. "Nasira baki zargi wani abu ba game da aran da aka ce an ji na wani? " "Babu zargin da na yi Hajiya menene ya faru?" "Na shiga imuwa wallahi dan na san Fatima za ta iya fitowa kin san wallahi da sun ganta sai an mata lilis a gidan nan dan babu abin da zai sa su ylaleta sannan ma duk su Hajiya da sauran abokan zamana sun san Fatima ni wallahi damuwar da na shiga ma ba ta tonuwar asirin ganin Fatima a gida nan bace, damuwata kar idan suka ganta kafin su kawo ta ma wurin Alhajin su mata dukan da za ta shiga wani hali" "Dan Allah Hajiya ki bar wannan maganar ke da muka bar Fatima a nan sannan kuma kin fa a mata kar wanda ya fito, kuma ita ma ta san matsalar gidan nn ai ba za ta fito ba" "Baki san halinta bane dole na san za ta iya cewa Beelal ya zauna ta je wani wuri ta dawo, za dai ta masa wayo dan ta je ta ga ko za a ci zarafina kuma da ace ta tarar da abin da take zargi na san sai ta fito daga ma oyarta ta bi min ha in mutuncina da aka ci sai dai ko me zai faru ya faru" "Gaskiya ba lallai ita bace kin san fa bada alar gidan nan, yanzu haka aya daga cikin matan gidan ce ta shigo da wasu a oye su ma suka je su baiwa idonsu nama su ga waf kar a yi ba su" "Ni dai yanzu mu je mu gani ko ta samu ta dawo ko kuma tana can wani wajen ta oya tana tsoron fitowa a gan ta dole in san abin yi " Hajiya ta fa a tana hawa saman Nasira ta take mata baya. Suna shiga suka a falon saman shiru babu kowa alamar ma basa falon sosai Hajiya La ifa ta tsorata dan ta auka ma Fatima da Beelal ne suka fita a tare kuma basu dawo ba, cikin sauri ta nufi akunan ta fara dubawa duk inda ta bu e sai ta ga wayam, duk ta rikice ita ma Nasirar ta tsorata amma suna bu akin da ke can gaba sai suka ga Fatima da Beelal a kwance a kan gado suna ta bacci abinsu. "Kin gani ko Hajiya dama na fa a miki cewar suna nan gashi dai kin gani da idonki sai zuciyarki ta yi sanyi" Cewar Nasira tana ar dariya. Wata nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana sakin murmushin farinciki ta ce "Kai me za a yi da tashin hankali da fargaba duk sai ka rasa nutsuwarka"Ta fa a tana samun wuri ta zauna. "Hakane kam tashin hankali ina ya ga da i yanzu zai sa ka ji komai ya kwance maka" Fatima da duk tana jin abin da suke cewa dama tun da ta jiyo motsinsu ta rufe idonta. Haka dai suka an jajanta Nasira ta yiwa Hajiyar sallama ta tafi angarensu. Haka Hajiya La ifa ta yi shirin kwanciya ta zo ta shimfi a katifa a akin ta zauna a ka tana ta kallon ar uwarta fa Beelal tana jin irin yadda son su da tausayinsu ke ratsa dukkan jiki da jijiyoyinta, tabbas maraici ba aramin abu bane da a ce iyeyensu suna raye da komai ya zo musu da sau i to amma Allah ba ya barin wani dan wani ya ji da i gashi mutuwa ta musu yankan auna ta auke iyayensu da kuma Kakarsu wacce ita ka aice wacce ta rage musu, yanzu kuma su ka ai suka ragewa kawunansu, gashi kuma addara wacce ke riga fata ta shiga tsakaninsu na rashin dace da abokan zama nagari dama haka ne rayuwar a mace gajera ce shi yasa ake so ta inganta ta, ta kuma tattalata ta kare mutuncinta arshe dai abu aya ne zai kasance jin da in rayuwarta shi ne dace da samun miji nagari nagartacce wanda zai kiyaye ha inta da na ansa wannan shi ne ka ai zai sanya ta rayu cikin farinciki sa anin hakan kuma rayuwa ce marar galihu da nagarta ha e da inganci Allah kiyaye. Haka ta zauna tana ta kallonsu tana sa a abubuwa da dama ta so a ce ita da ar uwarta sun yi dace da samun abokan zama nagari, sai dai kash hakan bai samu ba. Ita anwar tata miji babu halin kirki babu kulawa kai shi babu nasa da yawanta, ita kuma ga dai komai na more rayuwa amma kuma sai ta ha u da jahilin miji da kuma jahilar sirika zaman gidan wani irin zama wanda ba a san ha in da za a kiyye ba na aure na baiwa mace kylawa da soyayya, sai dai a bata ci da sha a bata komai ga ku i nan babu shamaki amma kuma abubuwan da aka rasa sun fi ku in muhimmanci nesa ba kusa ba. Kuka take yi ba mai sauti ba amma zafinsa ya fi ma a ce mai sautin take
Chapter 22 · 0% Book details