← Book details Beelal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 25

Sashe 14

Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kan fuskar kowa ya sauke idanunsa ba sai a kan Alhaji Husaini idanunsa ne suka firfito a take kuma jikinsa ya fara karkarwa hakan ya sanya butar hannunsa fa uwa... MMN AFRAH... *BILAL* NA MAMAN AFRAH FCW Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. *This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* Book 1 Page1 Alhaji Husaini ne ka kafe shi da idanunsa da suka ka a suka masa wani irin ja saboda tsabar acin rai. "Wallahi tallahi Alhaji ban ji zuwanku ba ina bayi cikina ne ya aci to dai dai na tsugunna sai na ji wani aran horn tamkar saukar aradu hakan ya tabbatar min ofa na min kiran gaggawa na zo na bu e, to wallahi gudawar da ta taho min ma ri eta na yi na taso ko yanzu ji nake kamar na sakeshi a wando" Cewar Mai tsaron ofa yana mammatse afa shi ala dole gudawa yake matsewa a ransa kuma yana ta faman jan istigfarin rantsuwar da ya yi. Shiru Alhajin ya yi yana are masa kallo yana son tabbatar da gaskiyarsa, ganin uban gumin da ke keto masa kamar yana she a masa ruwa sai ya ji ya kar i uzurinsa. "Ba ta zancen ofa nake ba, wannan na maka uzuri ka sna da zancen bu ofa ne sai ko wani daga cikin bodyguard su shigo su dubo ka. Tun da ka ganni ka san ka yi babban lefi. "Tuba nake yalla "Ba zancen tuba ake ba, dan za ka san ba yanzu ne za ka nemi yafiya ba sai na sanar da kai cewa daga yau ka bar aiki, idan har na tabbatar da abin da nake zargi" Cewar Alhaji cikin acin rai da aga murya. Idanu Mai tsaron ofa ya shiga ciccirawa tare da ha iye wani yawu, dan ya san dai arshen maganar dan zancen gizo bai wuce na i. Dan ya san a kan Beelal zai masa tambaya, shi kuma wannan dalilin ne ya sanya ya yi aryar shiga bayi gudawa. Yanzu idan yaron nan ya ce ya san da zamansa a ofar nan shi kenan kashinsa ya bushe, kuma asirin Hajiya ma zai tono dan dole yaron zai fa i Mamarsa a gidan, kai ya san ma har abin da ba a tambayeshi ba sai ya fa a ya san halin yara da fa i ba a tambayeka ba. "Me yasa ka bar min nakasashshen yaro a ofar gidana?" Muryar Alhajin ya katse masa tunani. "Uhm, na'am, yaro me nakasa kuma Alhaji ban san ba ma da zuwansa ko da unguwar nan bare kuma ofar gidan nan, ina can bayi ina fama" Ya fa a yana an ciccije le e tare da ara du awa kamar wani tsoho mai usumbi, kana ganinsa ka san akwai alamar tambaya a kan sa saboda gaba aya alamomin rashin gaskiya sun bayyana a tare da shi. Idanu Alhajin ya tsayar a kan sa yana mazarinsa, hakan ya sanya Mai tsaron ofa ya sunkuyar da kan sa asa dan matsawar yana kallon fuskar Alhajin zai iya yin komai da zai gano shi, saboda gaba aya ba a nutse yake ba dan ya san matsawar gaskiya ta yi halinsa ba wai aikinsa zai rasa ba har lafiyarsa sai ya rasa, dan sai Alhajin ya sanya an masa dukan mutuwa na etara dokarsa kafin ya koreshi. Dan ya sha jin labarin abin da ke sanya a kori Masu gadin kenan bai wuce a bar ba o ya shiga ba ko kuma nakasashshe ya shiga gidan ko ya tsaya a ofar gidan matsawar aka bincika aka gano gaskiya to kai kuwa ka ka e har ganyenka. Dan ko mai gadin da aka kora aka kawo wannan mai tsaron ofar an ce wani gurgune ya zo barw w keke bara, wannan ne dalilin da ya sanya aka masa dukam da aka sauya masa kamanni tare da masa korar kare. Wannan jahilci da rashin imani har ina. "Mu je wajen in tabbatar da abin da kake fa a, dan ba na bu atar ya shigo min gida" Ya ara katsewa Mai tsaro ofa tunani. "to, to, Alhaji" Ya fa a tare da ajiye butar hannunsa ya bi bayan Alhajin. Tafiyar dai ya cigaba da yi a du e, yana raya wa a ransa da zai samu dama yana fita da na kare zai ara dai ya san dai babu yadda za a yi ya ku uta daga wannan GWARAMAR "Littafin ummu sadiq" Gwara dai ya tsira da rai da lafiyarsa a kan ya rasa aiki kuma ya rasa lafiya. Da hannu biyu ya dafa ofar lokacin da zai fito, yana fitowa idanunsa suka fara sauka a kan ti a-ti an bodyguards in Alhaji suna tsaye fuskar nan kamar an aiko musu mutuwa, ga wani uban ba en gilashi tamkar wasu makafii, duk sun ame umarni kawai suke jira a basu su aiwatar, cikin Mai tsaron ofa ne ya bada wani ululu sai ya ji yana jin gudawar ma da gaske, dan ya san aka ha a shi da wa annan ka ai ya san sai dai Allah kiyaye, yo da ma ya lafiyar kura bare ta yi hauka. Kuma dai na shiga ban auka ba bata fidda arawo, bare kuma shi ya aukan ma. Fitowa ya arsa yi, yana kallon Beelal da ke dur ushe a asa yana ta kuka abin tausayi, ga jakar kayansu da dam e a hannunsa. Wani tausayin yaro ya tsarga masa domin tozali ya yi da sawun yatsun Alhaji a kumatun yaro da yake Beelal in fari ne sai sawun yatsun ya yi ja. Shi ma yana arasowa sai ya je kusa da Beelal in ya dur ushe ya tsaya a kan gwiwoyinsa. "Kai tun yaushe ka zo wurin nan bara?" Cewar Alhajin cikin aga murya. Kuka Beelal in ya sake fashewa da shi, cikin sheshshekar kuka ya ce "Ni...ni...ba...ba Almajiri ba...ne" Ya ce cikin in'inna. "Uban me kake min to a nan" "Mama ta nake jira" Ya ce cikin in'inna Cikin Mai tsaron ofa ne ya bada wani ululuuuu jin abinda Beelal in ya ce, dan ya san yanzu yaron zai fa i komai. Ina Mamar taka?" Cewar Alhajin dan so yake ya samo bakin zaren dan so yake sai ya san dalilin zaman yaron a ofar gidansa duk gidajen layin bai tsaya a ko ina ba sai a ofar gidansa idan ma ture aka masa sai ya gono da sanya hannun wa aka yi hakan. "Ta...ta..ta...na " Sai kuma walwarsa ta shiga tuno masa da maganar Mamarsa lokacin da za ta tafi cikin gidan. "Beelal duk wanda ya ce maka ina Mamarka kar ka ce ima cikin gidan nan, ka ce na tafi na nemo maka abinci" "Mama kin ce arya babu kyau" "Eh Beelal arya babu kyau, amma yanzu muna cikin damuwa, kuma Allah zai mana afuwar yin hakan saboda a dalilin wani hali da muka tsinci kan mu za mu yi, kamar dai tilas ce ta sanya yin, ka ga ko azumi idan aka tilastawa mutum ya karya to yana in za a masa wani abu da babu yadda zai yi ya waci kan sa, to yana karyawa amma kuma bai karye ba" "To Mama" irjin Mai tsaron ofa sai difdifdif yake jin Beelal ya akko hanyar bayar da asalin amsar da za ta fallasa asirin su. "Ana tambayarka tana ina" Cewer Alhajin a fusace ganin yaron na ata masa lokaci dan shi ba ya so ne ma a munfurceshi ne shi ya sa harka indai irin wannan ce ya fi so ya yi da kan sa saboda in yarda, amma da gida zai shige ya bar yaransa su zartar da hukunci dan ba gane maganar yaron ma yake ba dan ya lura yaron har wani rintse ido yake yana yafitawa in zai yi maganar saboda yadda in'innar ke ri e shi. "Ta tafi ta samo mini abinci" Ya fa a cikin in'innar. Ahhhh, Mai tsaron ofa ya sauke wata lukutar bayyananniyar ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna da as jin kwanyar yaron na aiki tu uru. "A ina za ta samo maka abincin?" Ni ma ban sani ba, amma ta tafi. Juyawa Alhajin ya yi ya kalli bodyguards insa, ya ce "Ku auke shi daga ofar gidan nan ku tabbatar kun yi nisa d umguwar nan sosai sai ku jefar da shi, Mamarsa ma da yake magana ba dawo wa za ta yi ba guduwa ta yi saboda ta gaji da wahala da shi ga kuma talauci" Ya fa a yana nufar motar da ya fito, haka suka bu ewa Alhajin ofar motarsa amma kafin ya shiga, sai da ya yiwa Mai tsaron ofa kashedi a kan ya sake sanya idanu sosai saboda ya gane babu saninsa Beelal in ke zaune a ofar gidansa dan ya gane cewa Mamarsa ya tafi nemo abinci ne shi ne ta barshi a wurin. Godiya sosai Mai tsaron ofa ya yi, duk da ya ji ba da i a kan abin da aka ce za a yiwa Beelal in da kuma tunanin halin da mahaifiyar yaron za ta shiga, idan ta ji wannan mummunan labari, gashi kuma tun azu yana jin wayarsa tana ta amsa kuwwa a aljihunsa kuma baya raba ayan biyu Hajiya La ifa ce ki kiransa. Alhajin na shiga mota suka rufe masa , Mai tsaron ofa ya shiga ya bu e musu get motocin biyu suka shiga cikin gida, ayar kwa a ciki suka sanya Beelal yana kuka suka tafi da shi, sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka tsaya suka fitar da shi daga motar suka tafi suka barshi a wajen yana ta kuka.Lokacin har an fara kiran sallar la'asar ma haka ya samu jikin wata bishiyar maina ya jingina yana ta kuka amma babu wanda ya kulashi kowa sha'anin gabansa yake. Haka suka koma suka sanar da Alhajin cewa sun cika umarninsa, da yake har ofar part insa motar ta kai shi amma kuma da ya fito sai ya tsaya har sai da aka sanar
Chapter 14 · 0% Book details