← Book details Beelal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 25

Sashe 5

Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aran wayarta ne ya dawo da ita daga zaucewa da fa ar magangaun da take, tana dubawa ta ga sunan mai tsaron ofa aro - aro kamar yadda ta rubuta.Tsabar ru ewa ma sai ta kasa aga wayar har kiran ya katse, yana katsewa wani ya sake shigowa aran da wayar take yi ha e suke da bugun da zuciyarta ke yi.Haka dai ta yi ta maza ta aga wayar ta kara a kunne hannunta har karkarwa yake jikinta sanyi alau. "Hajiya suna nan fa a tsaye kuma da na ji kiran ya katse na auka ma za ki sake kira" Ya ce cikin girmamawa. "Mai...mai tsaron ofa ka taimaka min kar kowa ya gan su, ina zuwa akwai abin da zan yi" Ta fa a kamar za ta fashe da kuka kai da jin muryarta ka san tana cikin damuwa fargaba ha e da tashin hankali. Jin muryarta ka ai ya sanya jikin Fatima yin sanyi tabbas ko da ace ba ta ga Yayarta ba jin muryarta ka ai ta san tana cikin wani hali, a halin yanzu ji take kamar ta kama Beelal su koma inda suka fito, sai dai ba halin yin hakan domin ko ku in motar komawar basu da shi. "To Hajiya in sha Allah babu wanda zai gan su, daga waje ma suke ko cikin get in ban shigo da su ba" Ya fa a yana waiwaya bayansa yana arewa gidan kallo dan tabbatar da babu wanda ya taho ko kuma wanda ya hango su. "Yawwa ina zuwa bari zan kira ka" Ta fa a a hankali kamar mai ra a -ra a ta yanke kiran tana kalle -kalle a falon nata dan gaskata babu wanda yake jin ta, duk da ta san ita ka ai ce. Hajiya La ifa na kashe wayar ta tafi da sauri ta bu e labulen window ta le asa da yake a sama take sai ta shiga arewa ko ina na gidan kallo.Babu kowa domin kowa yana can part insa kuma kowacce an aikinta na angarenta dan haka sai da ta tabbatar babu kowa ta saki labulen sannan ta dawo cikin falon nata.Cikin sauri ta sakko falon asa babu kowa a falon sai aran AC da TV suna ta aiki dama Nasira ta bari tana canja labulayen falon.Wayar Nasira ta shiga kira ringing in wayar na bugawa da bugun da zuciyarta ke yi, bugu aya biyu a na uku ta aga. "Assalamu alaikum Hajiya barka da warhaka"Nasira ta fa a cikin girmamawa. "Nasira ki bu e kunnenki ki ji abin da zan fa a miki Hajiya ta fa a a maimakon amsuwar sallamar, dan ita burinta kawai ta san yadda za a yi da su Fatima ba tare da wani ya gan su ba dan ko ka an ma ba ta fatan hakan. "Ina jinki Hajiya" "Ki akko kayanki na aiki set aya ki saka a cikin leda ki zo angarena yanzu -yanzu" Cewar Hajiya La ifa har lokacin a firgice take dan ta san matsawar labarin nan ya kai kunnen sirikarta to babu tantama wata ila ma a yau in nan a warware igiyoyin aurenta. "Hajiya kayan aikina kuma?" Nasira ta tambaya cike da mamaki, dan a iya saninta dai Hajiya bata ta a bu atar hakan ba. "Haba Nasira haka na fa a kamar yadda kika ji, ki yi sauri ki zo yanzu kuma kar ki bari kowa ya gani" "Toh Hajiya gani nan zuwa" Cewar Nasira ba dan ta gamsu da abin da uwar akin nata ta fa a ba, dan gaba aya mamaki ya gama cika mata rai da zuciya. Cikin sauri Hajiya La ifa ta katse wayar tana sauke aramar ajiyar zuciya, dan tana ganin ta an fara samun mafita duk da ba a kai ga inda gizo ke sa ar ba. Nasira kuwa ganin Hajiya ta katse kiran ta saka wayar a cikin aljihun rigarta ta aiki dan uniform ne da su gaba aya an aikin sai dai kowace matar gidan an aikinta da ban sannan kalar uniform an aikinta da ban, kayan an aikin Hajiya La ifa blue ne riga da wando sai dai rigar har gwiwa ake musu da aljihuna a jikinta sai an karamin hijabi iya kafa a amma hijabin ja ne. Lokar kayanta ta bu e ta akko uniform in, dan uniform in aikin yawa garesu ana kuma sassake musu haka ta akko a wanke tas a goge dan Hajiya La ifa ba ta son azanta kwata-kwata hakan ya sanya suke gyara kayansu tas gwanin sha'awa.A leda ta sanya ta fito daga akin, ma'aikatan ne gasu nan kowa yana abin da ke gabansa wasu wanki suke wasu kuma suna can angaren uwar akinsu suna hidima. "Nasira ina zuwa haka ke da kika shigo yanzu, ko baki gama aikin ba?" Wata budurwa da ke shanya kayanta ta jefo mata tambayar. "Eh akwai abin da zan yi ne ina zuwa" Ta fa a tare da saurin juyawa ta tafi ba tare da ta ji mai waccen in za ta ce ba. Tana fitowa daga angarensu na an aiki ta fara waige-waige da yake angarensu na an aikin a cikin angaren Hajiya La ifar yake sai dai daga can ciki yake, dan ta ji Hajiya ta ce kar ta bari kowa ya gani sai dai tana ta mamaki tare da jefawa kan ta tambayoyi barkatai, na abin da Hajiyar za ta yi da kayan, sanna n gaba aya ma a tsorace take kar dai Hajiyar sanya kayan za ta yi ta saci hanya ta fice daga gidan dan yanzu ta san basa fita kwata-kwata.Tana ta sa e-sa en nan har ta kai ga shiga part in Hajiya La ifar ta yi sa'a babu wanda ya gan ta kamar yadda uwar akin nata ta bu ata. Tana arin yin sallama Hajiya La ifa da ke bakin ofar a jikin labule ta sanya hannu ta kamo hannun Nasirar wanda hakan ba aramin tsorata Nasirar ya yi ba, amma ita Hajiyar ba ta lura ba saboda ita ma gaba aya a firgicen take. Tun da ta kama hannun Nasira ta ja ta iiii suka hau sama, ita dai Nasira ta tsorata da lamarin uwar akin nata amma babu yadda ta iya haka ta ke bin Hajiyar kamar ra umi da akala.Hajiya La ifa bata tsaya a falon saman ba sai da suka shiga aya daga cikin akunan da ke saman, sannan ta sanya mukulli ta kulle ofar sai da ta kai Nasira arshen uryar akin sannan t sakar mata hannu Nasira kwa sai zare ido take tamkar arayon da mai kaya ya kama shi da kayansa dumu-dumu. Hajiyar ma sai ifta ido take, sai da ta sauke wata ajiyar zuciya, ita ma Nasira ma ajiyar zuciyar ta sauke tamkar wanda ya etara katangar gidan yari da niyyar guduwa fursunoni basu ganshi ba, ya gudu.Jin aran ajiyar zuciyar da Nasira ta yi da kuma yadda take zare ido ya so ya baiwa Hajiyar dariya sai dai ba halin hakan domin kuwa tana cikin halin da dariya ba ta cancanci motsa ko da la anta ba. Bakinta take arin kaiwa kunnen Nasira domin mata ra a, amma me za ta gani Nasira ta bu e baki za ta zandama ihu dan duk a tsorace take kuma ganin Hajiyar na arin kai bakinta jikinta sai ta yi tunanin sumbatarta za ta yi, dan a take zuciyarta ta fa a mata ko dai Hajiyar ar lesbian ce duk da ta da e tana mata aiki kuma ta san ta mace mai kyan hali da abi'u masu kyau ga ibada sai dai a ganinta hakan ba zai hana shai an kai mata farmaki ba kuma ma dai an adam tara yake bai cika goma ba... MMN AFRAH *BEELAL* NA *MAMAN AFRAH* FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. Page 9 Hannu Hajiya La ifa ta sanya ta rufe wa Nasira baki tana kalle-kalle kamar dai wani zai ji ihun Nasirar duk da a sama suke a aki ofar ma a rufe da mukulli sannan a atshen akin amma dai saboda halin da take ciki mai cike da fargaba sai take ganin kamar wani zai ji su, domin an magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. "Nasira ihun meye hakan kike? Ke da nake son mu yi komai cikin sirri amma kina neman ki ji a mini aiki tun ba a je ko ina ba?" Cewar Hajiya La ifa tana yiwa Nasira kallon rashin fahimtar dalilin ihun nata har lokacin hannunta a bakin Nasira, so take sai Nasirar ta nutsu sannan ta bu e mata bakin dan ta ga gaba aya a firgice take gudun kar ta ara yin wani ihun. Idanu Nasira ta zaro zuciyarta na dukan uku-uku dan babu abin da ya aga mata hankali sama da cewar za su yi komai cikin sirri, to shin menene za su yi cikin sirri ? Da har ba a son kowa ya sani in ba munafurci ba har a cikin aki? Ta jefawa kan ta tambayar a zuciyarta. Wani gagarumin aiki zan sanya ki, idan kika yi babu kuskure mun tsira daga ni har ke idan kuma kika yi kuskure to daga ni har ke muna ruwa, domin kuwa ni na san zama na zai are a gidan nan idan hakan ta faru hatta ke ma za ki rasa aikin ki" Muryar Hajiya La ifa ta katse mata tunani. Kasa e Nasira ta yi tana kallon uwar akin nata kalamanta kuma na kaiwa da kawo wa a cikin walwarta. "So nake ki tafi can bakin get wurin Mai tsaron ofa akwai ba uwar da na yi, ki kai mata kayan aikin ki ta saka, sannan ku taho tare ki kawo min ita nan angaren ba tare da kowa ya gan ku ba" Ta fa a tana sakarwa Nasira bakinta da ta ri e mata tun lokacin da ta ya saki ihu. Jin Nasira da ganinta ne ya auke na wasu sakanni, hatta walwarta tsayawa ta yi cak da aiki, cikin an sakanni ta dawo daga duniyar ki imar da ta yi, irji ta dafe da hannu biyu tare da cewa.
Chapter 5 · 0% Book details