Sashe 13
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NA *MAMAN AFRAH* FCW Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. From the writer of RAYUWAR MARYAMU GIDAN MIJINA SANADIN KISHIYA AR YARINTA ANWATA paid AN UBANCI And now BEELAL *This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* Page 1 Cikin matu ar razana direban ya juyo ya kalli Alhaji Husaini lokacin da ya kashe motar ma gaba aya, ya kasa gane laifin da ya yi dan haka sai ya auka Alhajin na son a tsayar da motar ne duk da birkin da ya taka ya kusa haifar da mummunar ha ari tsakanin motar da Alhajin ke ciki da wacce ke bin bayansu dan da ma motocin guda uku ne. "Tuba nake Alhaji Allah huci zuciyarki" Direban ya fa a muryarsa har rawa take. Ba tare da Alhajin ya ko da kallonsa bane, dan har lokacin idanunsa ma na kafe a kan Beelal da bai ma san me yake faruwa ba.Daga cikin motar da ke bayan ne ofar ta bu e mutane guda biyu suka fito sanye da ba en kaya da alama bodyguard in Alhajin ne, cikin sauri suka araso wajen motar Alhajin su duka biyun suka kama ofar bayan d Alhajin ke ciki suka bu e duka ofofin dan sai an bu e duka ofofin biyu sai ya za i ta wacce ofa zai fita. Kamar jira yake ya watso afafunsa waje wani kakkaura mutum ne ba i amma ba sosai ba yana da tsayi sosai, sanye yake da farar shadda mai babbar riga kan babu hula dan ya cireta ya ajiye a cikin motar, hannunsa aure da wani tsadadden agogo. Yadda ya fito a fusace ya fito tamkar kumurcin maciji , sai ka auka a filin dambe yake ko na ya i, inda Beelal yake ya nufa da sauri kamar zai tuntsura, sai a lokacin gaba aya wanda ke motocin da kuma bodyguard in nasa da suka bu e masa ofar suka lura da yaron da ke dur ushe a bakin ofar da yake sun zo wurin kawai horn za su yi a bu e musu get in, gaba ayan su idanu suka zaro dan kowa ya lura d nakasar da ke tare da yaron Beelal kuwa ganin mutumin nan ya tunkaro shi, da kuma yadda ya ga fuskarsa babu alamar rahma cikin tsoro da firgici ya mi e tsaye ya tsaya a kan kafarsa duk da irin nakasa da kuma antar yaron hakan bai s Alhajin ya ji cewar zai fasa abin da ya yi niyya ba. Zuwansa ke da wuya ya aga hannu ya wanke fuskar Beelal da tagwayen maruka hagu da dama, wanda hakan ya sanya yaron gigicewa dan sai ya kasa gane laifin da ya yiwa mutumin dan ko ka an ma bai san cewa mai gidan da yake tsaye a ofar gidan bane bare ya san laifin da ya masa, bare ma gigicewar da ya yi ta sanya ya kasa tuna komai bare har ya tuna masu gidan basa bu atar mai irin halittarsa ko makamancinta ya ra i ko da inda suke. Beelal dajikinsa gaba aya ya auki rawa lokaci guda ya fashe da kuka, idanunsa ya sauke a fuskar mutumin da ke auke da shekaru kimanin talatin da hu u zuwa da biyar, da ke kallonsa da wata irin fuska mai bayyanar da tsantsar tsana da kuma yamar wanda ake yiwa wannan kallon. "Uban wa ya kawo ka bara unguwar nan? Wane shege ne ma ya baka damar tsayawa a ofar gidana, ko da ubanka muka ha a muka siya? Jikin Beelal na karkarwa ya shiga jijjiga masa kai hawaye na zubo masa. "Wato bebe ne kai baka ma magana, nakasar taka ma ta yi yawa ba afa aya ba hannu aya bakin ka ya sha kwana, sannan bebe ne kai?" Alhajin ya fa a yana zazzare masa idanu. "I...i...ina...magana...mma...n "Dalla rufewa mutane baki kai yanzu nan har wata magana kake ai da man ma bebe ne dan wannan maganar taka da ita da babu duk aya" Ya katse Beelal in cikin aga murya. Wannan tsawar da Alhajin ya yi ita ta ankarar da Mai tsaron ofa zuwan Alhajin da kuma aya daga cikin masu aikin gidan da ke zaune a bakin get in daga ciki. A ki ime Mai tsaron ofa ya mi e tsaye yana rarraba idanu, ayan ma tsayen ya mi e ya ce "Wallahi Alhaji ne wannan ta amma na tausayawa ko ma waye ya samu haka mai rabasu sai Allah" Mai tsaron ofa kwa da tunaninsa ya bashi cewa Alhaji ya ga Beelal kuma ya tabbata da shi yake wannan maganar sai ya tsinci kan sa cikin tashin hankali dan ya tabbatar yana cikin gagarumar matsala ba ma shi ba har Hajiya La ifa da anwarta da kuma Nasira duk suna ruwa matsawar yaron ya shaida masa mamarsa na cikin gidan. "Ni dai na yi nan kar a rutsa da ni, kai kuma da yake aikin ka ne sai ka rungumi addara dan ka san cewa zai yi laifinka ne dan yau ma fitarka sai Allah" Ya fa a yana juyawa ya bar wajen har da ha awa da an gudu-gudu. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yau mun ka e har ganyemu" Cewar Mai tsaron ofa yana saurin sanya hannunsa a cikin aljihu ya rarumo wayarsa.Waige -waige ya fara ganin ba kowa cikin azama ya zari buta ya nufi ban akinsa da ke kusa da akinsa, yana shiga ya kamo sunan Hajiya La ifa ya danna mata kira. Hajiya La ifa da ganin su Fatima ya sanya ta jin wani mugun da i ganin sun tsallake rijiya da baya, cikin sauri da murnar ganin junansu da ba za ta misaltu ba suka nufi junansu suka rungume junansu cikin farinciki. Nasira sosai ta cika da farinciki ganinsu suna murna tamkar yau suka fara ganin junansu.Ana cikin haka ne sai wayar Hajiya La ifa ta shiga neman agaji, amma sun kasa sakin juna bare har ta auki wayar da ake mata har dai kiran ya katse ba tare da ta auka ba. "Haba Hajiya muna cikin matsala fa ki auka mana" Mai tsaron ofa ya fa a kamar zai kurma ihu tare da sake danna mata wani kiran. Hajiya kwa jin kiran ya sake shigowa ta zame Fatima daga jikinta suka arasa kan center table inda wayar ke ajiye amma har lokacin hannayensu sar e da na juna, tana aukan wayar idanunta suka sauka a kan sunan Mai tsaron ofa. Sai lokacin ma ta tuna cewar sun bar Beelal a bakin ofa dan duk murna ta so matar da ita hakan. Da sauka ta danna ok tare da kai wayar kunneta. "Hajiya akwai matsala fa" Mai tsaron ofa ya fa a hankali tashe. "Matsala kuma mai tsaron ofa, matsalar me?" Cewar Hajiya La ifa cikin rawar murya dan yadda ta ji muryar Mai tsaron ofa ta tabbata gagarumar matsala ce, Fatima kwa Nasira idanu suka zaro suka zubawa Hajiya cikin son jin abin da ke faruwa. "Hajiya Alhaji ne ya dawo kuma ya ga Beelal a ofar gidan" "Alhaji ya dawo ya ga Beelal fa ka ce" Ta tambaya hankali tashe. Cikin sauri Fatima ta warce hannunta daga hannun Hajiya La ifa ta juya da gudu za ta fice, cikin zafin nama Nasira ta ri ota. "Ina za ki je?" Nasira ta fa a tana ameta ganin sai arin wace kan ta take. "Ki barni in tafi dan Allah, ko ma me zai faru ya faru dan wallahi ba zan jure ganin ana a wani hali ba kuma ba zan lamunci a wula anta min shi ba, domin ni ina son shi a haka kuma har arshen numfashina ba zan gaji da godewa ubangijina ba da ya bani kyautarsa, dan miliyoyin mutane neman haihuwar suke basu samu ba amma ni ya za eni kin ga kuwa ba zan butulce masa ba" Ta fa a hawaye na allewa daga idanunta tamkar an kunna famfo. "Wallahi ruwan da za ki allo ya fi wanda ya alle yanzu sannan za ki sanyamu a cikin wata matsala ki bari mu shawo kan komai a sannu" Cewar Nasira cikin kwantar da murya. Hajiya kuwa, Mai tsaron ofa ne ya cigaba da rattaba mata bayani, suna cikin magana ya ji an saki wani uban horn a jere- a jere kafin Hajiya ta arasa maganar da ta akko har ya yanke kiran. Sakin wayar ta yi ta nufo wurin su Nasira suka shiga lallashin Fatima, suna kuma addu'ar Allah ya rufi asirinsu. Mai tsaron ofa kwa yana kashe wayar sai ya yi saurin mayar da ita aljihu, jin gumi na kwaranyo masa daga fuska sai ya godewa Allah domin hakan ma cikin abin da ya ke tunanin shiryawa domin shirin ko ta kwana tsakaninsa da abin da ya tunkaroshi, addu'a d fatan da yake shi ne kar Beelal ya ji a masa aiki. Sai da ya ji ya an finciki aramar ofar get in da wani uban arfi tamkar za a alleta alamar wani zai shigo kenan dan a tabbatar da dalilinsa na rashin bu e get a kan kari. A hankali ya auki butarsa da ya shigo da ita ya tsiyayar da ruwan ciki tas, ri ota ya yi da hannun dama hannun hagun in ya ri e bango ya fara tafi a du e dan ko mi ewa bai yi ba. A hakan ya fito daga bayin yana bin bango ga wani uban gumi da ya ji ashi jargaf, idanunsa ne suka sauka a kan wasu afafu wanda hutu ya zauna a jikin fatarsu, suna sanye cikin takalmi mai matsiyacin kyau. Yana daga du en ya ago iya idanunsa yake bin jikin mutumin da kallo dan tabbatar da zargin da zuciyarsa ta fa a masa, tun daga kafa ar mutumin wakwarsa ta gaskata masa wanda yake gani a gabansa ba sa o ba. Cikin dauriya ya arasa da idanunsa fuskar mutumin zuciyarsa ce ta yi wani irin hautsinawa d mugun arfi ganin fuskar da ya yi ya ara ru ashi, domin kuwa ba a