Sashe 23
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi saboda yadda ya ha e mata biyu kukan zuci da kuma na zahiri duka biyu abin ke yiwa zuciyarta ga Fatima ga kuma Beelal da a ce tana da dama da anci a gidan n an da kuwa sun dawo hannunta da zama ko dan su samu kulawa su zama basu rasa komai ba ko dan ta zamewa Fatima bango abin jingina ko dan Fatima take ji a ranta cewa bata yi maraici ba, gwara ta zauna da ita a kan zaman auren da take wanda da shi da babu kusan aya ne dan ba a ce aya b saboda shi aire ginshi i ne kuma garkuwa ne ga a mace, aure yana aga darajar mace sama da duk yadda wanda ke da aure zai yi tunani amma wanda bai da aure ya kan gane hakan saboda abubuwan da zai ga ya rasa idan bashi da auren. Fatima kuwa daga baccin wasa da ta rufe idonta baccin ya yi awon gaba da ita, saboda gajiya ga kuma wunin fargabar da zuciyoyinsu suka wuni a ciki. Haka Hajiya La ifa ta aida kanta ta kwanta a kan katifar amma kuma sai ta ji ba za ta iya kwanciya ba ita ka ai tana ganin an uwanta haka ta tashi ta koma kam gadon ta gyarawa Beelala kwanciyarsa ta kwanta suka sanyashi a tsakiya haka ta kwanta tana sa e -sa e har bacci ya yi awon gaba da ita. Haka suka kwana biyu kamar yadda suka zo su yi da yake gidan gaba aya a ru e yake da haihuwar da aka yi sai ya zamana babu wani wanda zai kawo cewar ma a kwai wasu a cikin gidan haka suka yi kwana biyun cikin soyayya da kulawar junansu Hajiya La ifa tana ji a ranta ina ma kar su tafi su barta domin u ka ai ne sanyin idaniyarta su ka ai take kalla ta ji da i marar misaltuwa a ranta. Amma babu yadda za ta yi haka za ta ha ura su koma gida. A dai dai lokacin da ake wani taron a lokacin da kowa yana angaren Hajiya Mariya a can take taro ita da Alhaji dan haka kowa na gidan yana can bayan Hajiya La ifa sun yi sallama da Fatima har da kukansu na rabuwa da juna, Beelal ma sosai ya ameta yana kuka wai ba ya son su tafi su barta, yana ta mata magiya tana zuwa suna ganinta, haka dai ta amsawa yaron cikin jin tausayinsu duk a ta san yanzu komai zai yi sau i tun da Hajiya Nuratu ta haihu dole za a rage dokar hana fita. Waya sabuwa Hajiya La ifa ta baiwa Fatima da kuma kayan Beelal na an ball da abubuwan wasa da piano na na yara da ta baiwa direbanta sa o ya siyo mata a oye sai ku e masu yawa da za su sayi kayan abinci da kuma abubuwan bu ata. Mukullin get in da ta kar a a hannun Mai tsaron ofa wanda yake datse ofa idan za a yi taro shi ya bata a oye domin su samu su fice ba tare da kowa ya sani ba, suna yin sallama ta kama hanyar angaren Hajiya Mariya ta barsu a angarenta za su fita sai Nasira ta samesu a bakin get in dan idan a ka ga Hajiya La ifa ta fito za a zargi wani abu idan kuma Nasira ce ba lallai a kawo komai ba, dan haka Fatima Beelal in ta goya a bayanta ta ri e musu akwatin kayansu da Hajiya La ifa ta basu suka saka kayansu a ciki har da turamen atamfofin Fatima haka ta auka suka baro part in cikin sauri dan gudun wani ya gan su duk da dai da wuya dan kowa yana wajen taron a haka ta araso get in tana ta hucin tafiya da kuma nauyin akwatin hannunta ga kuma goyon Beelal da take auke da shi. Suna zuwa kawai sai ganin Nasira ta yi ta fito daga ma oyarta dan izinin fitowa fitsari ta nema ta fito wannan kasadar. Bu e get in ta yi sa mukullin suka fita tana aga musu hannu, da sauri ta mayar ta rufe ta juya abinta, haka ta koma angaren Hajiya Mariya ba tare da kowa ya ganta ba, ta koma mazauninta ta zauna, da aka gama fa auli da ba'adin aka sallami kowa ya kama gabansa, a haka ta yi dibara ra baiwa Mai tsaron ofa mukullin ba tare da kowa ya gane hakan ba. Haka suka koma angaren Hajiya La ifa ita da Hajiya La ifar cike da kewar Beelal da Fatima suna musu fatan sauka lafiya. *Fatima* Suna fitowa daga gidan ta yi hamdala da wannan tsallaje rijiyar da baya da suka yi, sakko Beelal ta yi daga bayanta, ta kama hnnunsa tana ri e da akwatin a haka suka an fara tafiya kafin suka samu napep suka hau ya kaisu tasha suka hau mota, motar na cika suka kama hanyar Kazaure. Suna sauka a Kazaure Fatima ta musu siyayar kayan abinci da duk wani abu da za su bu ata har takalmi na soso ta siyawa Beelal dan dama daga can a kayan da aka siya masa har da takalman kwalliya kala biyu. Dan haka sai da ta siyawa Hameeda ma na kwalliya kala aya da na soso guda aya sannan ta yi tsaraba, dan bata samu damar siyowa a Kano ba saboda gani take kamar wani zai je ya fa a cewa sun je gidan Hajiya La ifa Alhajin ya sa a biyo su. Napep ta samu ya kwaso musu kayansu ya akko su zuwa auyensu, a dai dai ofar gidan ya tsaya ya fito yana fiddo musu da kayayyakin daga can bayan napep in da aka sanya su da kuma na kan mazaunin kaya ne da ba ka an ba. Beelal da ke sanye da wando da riga masu kyau ga takalmin kwalliya sai washe baki yake ana fito musu da kayan yana murna yana jin farinciki a ransa su ma sun yi kayan abinci ba za su ke zama da yunwa ba. i ta akko ta sallami mai napep in, a haka yara suka zagayesu amma ganin Beelal in cikin shiga me kyau ya sanya yaran tsayawa suna kallonsu da a mamaki dan ba Beelal ka ai ba hatta Fatima kaya ne masu kyau sababbi a jikinta, hakan ya sanya ma basu tsonani Beelal kamar yadda suka saba ba. Fatima juyawa ta yi da niyyar ta je ta bu e gidan dan ta shiga da kayan amma me kawai sai ta ga ofar gidan a bu e tana shirin fa awa Beelal sai zuwa Hameeda a guje ya dakatar da ita dan Hameeda ta samu labarin dawowarsu. Tana zuwa suka rungume juna Hameeda da Beelal suna ta murna. "Beelal Babanka ya dawo jiya" Cewar Hameeda da bakinta ya i rufuwa ganin Beelal. Gaban Fatima ne ya bada wani rass, jin abin da Hameeda ta fa a, tana shirin furta wani abu aikuwa sai ga Idrisu ya fito daga gidan, ganinsu ya sanya ya ha e rai kamar wanda ya ga ma iyansa wani kallo yake jifansu da shi wanda ya sanya Beelal sunkuyar da kai dan ba ya son kallon fuskar mahaifin nasa saboda yadda yake masa wani mugun kallo me cike da tsantsar tsana. "Baban Beelal ashe ka dawo" Fatima ta fa a cikin ari- ari muryarta har rawa take. "Ya za a yi ki san na dawo kwa tun da kin tafi yawon barba a kina can kina yawon bariki, to aikuwa bariki ta miki kyau tun da gaki da kaya ni i-ni i, kuma kar ki sake kirana da Baban Beelal ki bar ha ani da wannan nakasashshen kirani da sunan na Idrisu hakan ya fi min" Ya fa a cikin kaushin murya yana hararta. "Haba ka bar fa ar haka nan fa titi ne, ko ma me za ka fa a ka bari mu shiga gida, kuma Beelal ai bashi da wani mahaifi sama da kai" Ta fa a tana kallon Beelal da ke zubar da hawaye har lokacin kansa a sunkuye Hameeda ma ta yi shiru ranra a ace tana ri e da hannun Beelal. "Ke har wata kima ce da ke wacce za ta sanya a miki magana a ke antaccen wuri? Ai ko a kasuwa a bainar jama'a zan iya fa a miki abin da raina yake so" Ganin abin nashi zai wuce gona da iri sai ta auki kayan Hameeda ma ta taya ta Beeelal kuma ya auki abin da zai iya suka kwashe duka kayan Idrisu kuwa tuni ya kama gabansa ya shiga gari. Kayan ta fitar ta baiwa Hameeda nata da kuma na Ummarta suka tafi da Beelal su kai mata duk da ta san za a samu yara a hanya su zolayi Beelal amma dole ta aika su gidan su Hameeda dan ta san Idrisu zai dawo ya yi rashin mutuncinsa a gidan. Cikin ar murna Beelal in ya bi Hameeda suka tafi duk da tun lokacin da Babansa ya ce a daina ce masa Baban Beelal ta lura duk jikin yaron ya yi sanyi duk da ba yau ya fara ji da ganin hakan ba in ban da yarinta ma in sabo ne ai da ya saba. Tun da ya dawo gidan yake sababi yana cewa ta tafi yawon karuwanci dan ta ga baya gari, haka ta shiga bashi ha uri tana nuna masa wajen ar uwarta Fatima ta je saboda ta da e bata zo ba kuma gashi basu da abin da za su ci. "Yo ban da aurin tsantsa a ce wai kin tafi wajen ar uwarki neman abinci, bayan ga jari nan Allah ya baki, wannan an naki nakashashshe ai shi ne jarinki, dan idan kika aukeshi kuka shiga cikin gari da ma auyukan da ke ma otaka da mu sosai za ku samo sadaka, dan ata lokaci ma kike da kuke turasa wata makaranta amma ai babu abin da Beelal ya dace a yi da shi sama da neman ta annabi (Bara, sadaka). Tun da ya fara magana idanun Fatima ke tsiyayar hawaye, yana maganar yana cika baki da lomar abincin da ta dafa wanda suka dawo da shi dan shi ko tsinke