← Book details Beelal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zauna ka na ta kuka" "Ma...ma, naaaa...ji...maganarki...amma fa...yau ma Malam ma ...korata ya yi...da zan karanto masa karatu, wai...ba ya son, in,innaa" Ya fa a har lokacin kan nasa na kan gwiwarsa kuma bai fasa kukan ba duk da yana in,innaa amma hakan bai hana Fatima gane mai yake fa a ba, kuma har cikin rai da zuciyarta ta ji haushin abin da Malamin ya masa duk da ba yau ne aka fara ba amma dai abin ya sosa ranta sosai dama kowace uwa ba ta son damuwar an ta bare kuma a mai nakasa dan mace ko anta goma idan dai guda aya yana da nakasa ko yaya ne ko da kuwa wata jinya ce Allah ya jarabci an da ita kamar sikila ko aljannu ko dai wata tawaya a jikinsa to uwar an nan ta kan ji ta fi aunarsa.Duk cikin anta ta kuma fi tausayinsa sama da sauran iyan nata... MMN AFRAH *BILAL* NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ba Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. Page 3 Cikin raunin zuciya da sagewar afa jin furucin Beelal, na sanya hannu na tashe shi tsaye, tsayawa ya yi amma har lokacin hawaye na zuba a idanunsa da alama ma idanun a kumbure suke saboda kukan da ya yi.Rungume Beelal in na yi a gefen hannun damana, hagun in sai na rungume Hameeda aran sheshshekar kukan da suke na ta a min zuciya ji nake kamar in maida damuwar tasu cikin raina duk da na san yadda nake ji a raina ya linka yadda suke ji.Sai dai babu wani abu da zan iya yi a kai wanda ya wuce in lallashe su in basu ha uri tare da addu'ar Allah ya kawo mana arshen wannan hali da muke ciki da kuma alubalen rayuwa da muke fuskanta tun da dukkan tsanani yana tare sa sau i babu wani dawwamammen abu da i ko wuya, duk masu wucewa ne.Haka na ja su muka shiga cikin gidan dan na san Hameeda ma babu inda za ta tafi har sai ta ga Beelal ya daina kukan dan duk lokacin da yake cikin unci haka take kasancewa tare da mu har sai ta ga walwalarsa, al'amuran yarinyar tamkar wata babba haka take yin abubuwa ga sanin ya kamata. Muna shiga cikin gidan na zaunar da su a kan tabarma na shiga lallashin su har sai da na ga sun saki ransu sannan na tafi domin in iza wutar da na ora abincin. "Mama kin ga fa har takalminsa ya tsinke da an makarantar suka biyomu" Muryar Hameeda ta katse min hura wutar da nake, ko ma in ce ta dawo da ni daga tunanin da na lula dan a zahiri ina hura wutar ne amma zuciyata tana can wani waje da ban, dan kuwa na tafi tunanin maha in abincin da zan basu, domin kuwa ko igon mai bani da shi a gidan bare yaji gishiri kawai nake da shi.Tsaye na mi e daga sunkuyen da na yi ina fifita wutar da mafici na kama ugu tare sa sauke wata ajiyar zuciya na ce. "Babu komai Hameeda zan san yadda za a yi" "Za ki siya masa sabo" Ta ara jefo min tambaya. "Idan Allah ya hore min zan siya masa idan kuma ban samu ku i ba zan baiwa mai gyaran takalmi ya gyara masa" Na ce ina maida kallona kan Beelal da ya yi tagumi da hannun hagun insa dan shi ne mai lafiyar, yana bin mu da ido. "Ma...ma ki ba da ...aaaa ...gyara min na san baaaa...ki...da ku...ku i" Ya arashe maganar cikin sanyin murya. Shiru na yi ina jin tausayin Beelal na tsarga min saboda yaron akwai hankali idan ya yi wata maganar ma ba za ka ta a tunanin yaro ne mai arancin shekaru ya yi ba. "Kawai ka bari idan ta samu ku in ta... "Assalamu alaikum" Sallamar Umma Hafisa wato Ummar Hameeda ta katse maganar da Hameedar ke yi. 'Wa alaikumus salam" Na amsa ina iro murmushin ya "To sarkin surutu kina nan kina ta zuba ko?' Ta fa a lokacin da ta araso tsakar gidan. "Umma ba fa zuba nake ba magana nake yi" Hameeda ta fa a tana washe ha ora. "To na ji dai, Beelal kuka ka yi ne?" Ta tambaya tana kafe Beelal in da ido fuskarta na nuna alamun damuwa. "Kuka muka yi an makaranta ne suka biyo mu kin san kullum fa sai sun biyomu suna tsokanarsa"Cewar Hameeda tana kallon Ummarta. "To zabiya ke na tambaya?" Ummar ta fa a tana harararta.Ni dai murmushi na yi na akko kujerar ar tsugunno na ajiye mata na ce "Ummar Hameeda ga kujera, kuma dai kin san idan kika tambayi Beelal abu tamkar kin tambayi Hameeda ne dan kuwa kin san ba a raba hanta da jini" "Ai na sani Hameeda da Beelal sai Allah,amma kin santa fa i ba tambayeki ba ce.Yanzu ma na ji shiru-shiru shi ne na biyo sawu dan na san tana nan, matu ar dai ba gani ta yi ya daina kuka ba na san ba yarda za ta yi ta taho gida ba"Ta ce tana zaunawa a kan kujerar da na ajiye mata. "Wallahi kam ai tsakaninsu sai Allah"Na fa a ina kallon yaran. "Fatima dan Allah ki ci gaba da ha uri kamar yadda na sanki komai mai wucewa ne wataran sai labari, labarin ma wata rana ba a ji ba" "Babu komai na auki hakan a matsayin addarata" "Yawwa Fatima haka ake son bawa ya kasance mai yarda da addara mai kyau ko sa anin hakan, idan da rai da lafiya wataran sai hakan ya zama tarihi" "To Ummar Hameeda na gode" Hannun ta da ke cikin hijabi ta fiddo, ta mi o min ba ar leda. "Ga wannan ka an ne ba yawa" Hannu biyu na sanya na kar a idanuna na cikowa da walla. "Na... Hannun da ta aga min ne ya dakatar da ni daga maganar da nake shirin yi, dan babu abin da Ummar Hameeda ta tsana irin ta baka abu ka mata godiya. "Tashi ke mu tafi har an fito daga masallaci" "Ki barta mana idan ta ci abincin sai ta taho"Na fa a ina kallon Ummar Hameeda da har ta mi e tsaye. "Ni dai a gida zan ci, Ya Beelal sai na biyo maka islamiya" Hameeda ta fa a tana mi ewa tsaye ta sanya takalmanta. "Tooo...Ha...ha ...meeda" Ya ce har yana runtse ido saboda in, innar da ta sar eshi. " Maman Beelal mun tafi sai zuwa jimawa" "To Ummar Hameeda mu jima da yawa" Suna fita na yi saurin bu e ledar man gya a ne rabin kwalba, da jan yaji dakakke a wata ar roba, sai dakakken arago a farar leda a ulle da kuma garin kwaki.Wata ajiyar zuciya na sauke mai arfi na ajiye ledar tare da aga hannaye na sama na godewa Allah d wannan kyauta da ya mini tabbas ubangiji mai ji ne kuma masanin komai yana tare da bawansa a koyaushe. "Ma...ma me...me..nene?" Beelal ya fa a yana washe baki. Wani da i ne na ji ya baibayeni ganin murmushi a fuskar yarona tabbas babu abin da ya fi ka ga anka cikin farinciki. "Gari ne da yaji da kuma mai har da arago" Na fa a cikin farinciki. "U...U...Umma tana son ...Mu, amma... Baa...Baa ba ya zuwa wurin mu bare ya kawo mana abinci." Cewar Beelal yana kallona. Jikina ne ya yi sanyi da jin furucinsa, yaro ma kenan ya san mai kulawa da shi, idona ne ya kawo walla, amma sai na yi saurin mayarwa dan ba na son na yi wani abu da yaron zai fahimci wani abu saboda yana da kyau uwa take oye damuwarta ga anta, tare da kawar da duk wani abu marar kyau daga zuciyar yaran dan gudun kar su sanya hakan a ransu musamman dangane da mahaifinsu gudan kar su girma da abun ya ransu.Wani murmushin ya e na maye gurbin damuwar da ta so bayyana a fuskata na arasa kan tabarmar da yake zaune na zauna tare da dafa kafa arsa na ce "Eh Ummar Hameeda na son mu haka Babanka ma yana son mu, kuma rashin zuwansa ai hakan ba yana nufin ba ya son mu bane aiyuka ne suke masa yawa amma zai dawo kwanan nan" "Amma ai ya da e bai zo ba kuma ko ya zo ba ya kawo mana komai, ba ya siyo min alewa ko abin wasa kuma ba ya so in ke zuwa kusa da shi korata yake, ya ce tafi ka bani wuri ni ba na gane maganarka kuma ba na so kake zuwa kusa da ni" Ya fa a cikin in,innaa idanunsa na cikowa da wallar. Daker na danne hawaye da ke barazanar zubowa daga idanuna, wani tausayin yaron ya rufeni ashe komai yana walwarsa dama yara basu da mantuwa yanzu rabon Babansa da garin nan kusan shekara biyu amma bai manta abin da yake masa ba amma dole a matsayina na uwa in yi abin da zan kawar masa da abim daga ransa.Dariya na yi har ha orana suka bayyana, Beelal kawai tsayawa ya yi yana kallona na ce "Kaima dai Beelal da wani abu kake, ashe baka san wasa ba, ai Babanka wasa yake maka amma ya fi aunarka fiye da kowa, kuma kaya da ba ya siyo maka ku i ne babu a hannunsa shi ya sa" Shiru ya an yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce. "Amma ina ganin ku i a hannunsa kuma... "Ya isa haka bana son jin komai, tashi mu je na maka alwala na cire maka kayan makarantar sai a sanya wasu ka yi sallah kafin nan na ha a abincin" Ta fa a dan kawar da zancen saboda ita tana fashin sallah. MMN AFRAH *BEELAL* NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. Page 5 Misalin arfe biyu na dare ne zaune take a kan katifa, ta
Chapter 2 · 0% Book details