Sashe 10
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. *This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* Page 1 Waigawa Nasira ta yi hagu da dama ta ga babu kowa, shi ma mai tsaron ofar waige-waigen yake kamar yadda ita ma take yi.Sai da ta tabbatar ba kowa sannan ta ce. "Mai tsaron ofa Hajiya La ifa ce ta... "Yanzu ta kirani ta fa a min komai" Ya katse ta daga maganar da take son fa a masa. "Yawwa to ina ba uwar take?" Ta tambayeshi cikin ra a-ra a dan shi ka ai ta gan shi kuma ma duk fa babu kowa dole ta yi takatsan tsan saboda tsaro amma akwai tsoron ma. "Ki shiga cikin akina ga ta nan zuwa" Ya fa a yana kallon Nasira, cikin sauri ta yi wuf ta fa akin mai tsaron ofa da ke kusa da get in ba tare da kowa ya gan ta ba. ofar ya kama da hannunsa ya an bu ofar da yake mayar da ofar ya yi ya kara dan kar wani ya zo bazata ya gan su.Yana bu ewa ya le a kan sa sai da ya tabbatar babu kowa a wajen sannan ya ce "Fatima shigo ta zo" Ya fa a a hankalin. "To" Cewar Fatima dan gaba aya ma bata da nutsuwa a tsorace take. Ledar su ta akko tare da kama hannun Beelal ta ce mu je ko?" "Fatima ban da shi fa, ke ka ai za ki shigo" Cewar mai tsaron ofa. Idanu Fatima ta zaro jin furucin mai tsaron ofa ta ce "Kamar ya ban da shi?" "Haba Fatima ya kike ata lokaci akwai gagarumar matsala fa, tun da aka ce ki shigo shi ma ai za a shigo da shi" "A'a ba zan ta a tafiya ina bar shi a nan ba, idan wani abun ya faru da shi fa?" "Mai tsaron ofa wai ya na ji shiru, ka san fa ha arin da ke tattare da wannan kasadar da zan yi" Nasira ta fa a lokacin da ta le o daga akin jin shiru ba uwar ba ta shiga akin ba. " Tana zuwa " Cewar mai tsaron ofa, lokacin da ya juya yana kallon Nasira kafin daga bisani ya maida hankalinsa kan Fatima da ta i shigowa. "Babu abin da zai faru da shi ki taho kawai zan kula fa s... aran kiran da ya shigo wayar Mai tsaron ofa ne ya katse masa maganar.Ganin sunan Hajiya La ifa ya gani da sauri ya aga ya kara a kunnensa. "Mai tsaron ofa sun taho ne?"Cewar Hajiya La ifa. "Yanzu za su taho Hajiya sai dai wai ba za ta iya tafiya ta barshi ba" "Sa wayar a handsfree na mata magana" Da sauri ya sanya wayar a handsfree "Fatima ki yi ha uri ki taho shi ma za a san yadda za a yi a shigo da shi" Muryar Hajiya La ifa ta doki kunnen Fatima. "To Yaya" Cewar Fatima ba dan ta so ba. "Mama ki je ni ina nan, ni ma an ce za a shigo da ni" Beelal ya fa a cikin in,innarsa yana mai yin murmushi dan shi da i yake ji an ce za su shiga gidan. "To Beelal" Fatima ta fa a tana shafa kan sa, walla na cikowa da hawaye.Haka ta barshi tana ta wai wayensa har dai Mai tsaron ofa ya nuna mata akin da za ta shiga. Tana shiga Nasira ta mi a mata kayan dan har ta fitar da su daga leda gudun ata lokaci.Da mamaki Fatima take kallon kayan dan bata fahimta ba annan kayan su za ki saka domin yin adda kama" Cewar Nasira tana juya mata baya dan ta sanya kayan.Haka Fatima ta yi sauri ta sanya kayan, tsaf kayan suka zauna a jikinta dan dama ba iba gareta ba dan wani ma sai ya yi zaton ba ta da aure. Tana gama saka wa suka fito daga cikin akin, haka suka baro bakin get in suka kama hanya kowacce na addu'ar isar su lafiya. Fatima sai arewa gidan kallo take kamar ba shi ba, ga tarin motoci nan masu kyan gaske wasu kuma a lullu e suke.Mamaki take a rant a cewa duk tarin dukiyar gidan nan amma babu kwanciyar hankali a cikinsa, tabbas arzi i ba shi ne ban kwana da damuwa ko tashin hankali ba sau tari dai ka ga wanda bashi da cin yau bare na gobe ya fi wanda ke da tarin dukiya sa un kwanciyar hankali amma wasu sai suke ganin babu wanda ya kai mai ku in samun wa annan abubuwan.Tun da yana da dukiya ai babu wani abu da zai rasa. Sun an yi nisa da bakin get ka an sai kuwa suka ga shugaban masu ban ruwan flowers a gabansu kamar wanda aka jefo shi. "Nancy manyan asa fa gari baki aya" Ya fa a yana washe baki. "Akwai magana ne sauri nake, kai sai ka tare mutum kuma ni ina da abin yi ba yanzu muka gaisa ba"Ta fa a gabanta na fa uwa. "Kinsan ba na gajiya da kallonki, dama ina can zaune ina jiran dawowarki sai kuma na hango kin ru anya, ma'ana kun zama ku biyu ke da kika tafi ke ka ai" Ya ce yana ta arin ganin fuskar Fatima da ta janyo hijabin ya rufe fuskarta. "Wayyo Allah azu na ku uta yanzu kuma yana son kawo min cikas"Nasira ta fa a a zuciyar ta a fili kuma ta ce "Eh a wajen get muka ha u da ita Hassana ce fa kamar baka gane ta ba"Ta ce tana wulwulga ido, tare da fatan Allah sa kar ya hango jirginta. "Hassana fa kika ce? Hassanar kuma ciwon baki take ne da ta kasa min magana kin san ta fa da shegen surutu, amma ko zolata bata yi ba"Ya fa a yana washe baki. "Ciwon ha ori take kuma idanunta ma ciwo suke shi ya sa ra rufe fuskar"Ta ce tan an zungurin Fatima alamar su tafi tun kafin ya gano su. "Ikon Allah sai na ga ta ara tsawo sannan ji afafunta jajir da su kamar wacce fa zo faga indiya" "Cin man gya a ne ya mata yawa shi ne anya ta kama ta" Nasira ta fa a tana ara zungurin Fatima wacce ta ji e jagaf da gumi saboda ru ewa sai addu'a take a zuciyar ta. Haka suka tafi suka bar shi wajen yana ta mamakin yadda aka yi aka haihu a ragaya. "Fatima ki rage sauri, mu tafi sannu -sannu dan kar a gan mu a zargemu kin san su gidan nan zargi bashi da wahala a wurinsu saboda tsabar rashin yarda" Cewar Nasira su ka ci gaba da tafiya. Sun kusa kai wa part in Hajiya La ifa kawai sai suka hango Hajiya Mariya mahaifiyar mai gidan kuma sirika a wurin su Hajiya La ifa, sanye take da doguwar riga mai adon duwatsu, kai da ganin rigar ka san ba aramin ku i aka sanya wajen siya ba,ta aura an kwalin rigar sai kuma ta yafa mayafi wanda ya shiga da rigar.Sai tabarau a fuskarta an aikinta guda biyu suna take mata baya sai wata tafiyar ta ama take tana hura hanci. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil idan matar nan ta gano mu yau aryarmu ta are"Cewar Nasira tana zare idanu. "Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu ma ba za ta gan mu ba" Fatima ta fa a cikin ra "Baki san matar nan ba wallahi, kawai mu bi jikin flowers mu uya idan sun wuce sai mu fito tun da ba hanyar get suka nufa ba angaren sauran matan gidan za ta je" Nasira ta fa a tana an waiwaya inda za su uya gabanta na lugude. Cikin flowers suka shiga suka la e, gaba ayan su a tsorace suke dan kar asirinsu ya tonu, gashi dole dai sai su Hajiya Mariyar sun wuce ta gaban flower da suka ratse suka oye a ciki dan hanyar part in Hajiya Nuratu suka nufa ita ce wacce ke da tsohon ciki a yanzu kuma ita ce ake ji da ita tamkar nama aya a miya ake kuma tarairayarta kamar wai.Har Hajiya Mariya ta kusa gota flower kamar wanda aka dakatar da ita sai kawai ta tsaya a setin inda su Nasira suka la e, aikuwa nan da nan zukatansu suka shiga lugude tamakar ana daka hatsi a turmi.Dan hatta numfashinsu sai da suka dakata da sha a saboda suna ganin kamar idan ta jiyo za ta san da zaman su a cikin flowers Hajiya Mariya kwa fuska a ha e ta sanya hannu ta gyara zaman gilashin fuskarta, kafin cikin izza ta bu e baki ta ce. "Nasira! Fito daga ma oyarki" irjin Nasira ne ya bada wani sautin dimm har wani fitsari ta ji yana arin wace mata, su kuma sauran an matan da ke yiwa Hajiyar aiki mamaki suke a ina Hajiya ta ga Nasira da har take mata magana amma ba su yi mamaki ba saboda sun san Hajiyar da idanu kamar na walati shegen gani ne da ita.Nasira kwa jin Hajiyar ta ce ta fito duk da hankalinta a tashe yake sai ta sanya hannu da danne cinyar Fatima alamar kar ta tashi, tare da mata alama da hannu a kan bakinta alamar ta yi shiru.Dan ta san da ace Hajiya ta gan su dukansu cewa za ta yi su fito amma jin ita ka ai ta ambata sai ta an ji sanyi-sanyi a ranta. Cikin sanyi jiki ta fito daga cikin ma oyar ta bar Fatima a ciki wacce ke tsugunne gaba aya abin duniya ya isheta, ga tunanin ta bar Beelal a bakin get ga kuma tunanin wannan tsaka mai wuya da suke ciki dan ta fara hasashen da wuya su tsallake sira i babban tashin hankalinta kuwa bai wuce halin da ar uwarta La ifa za ta shiga idan har asirin nasu ya tonu.Nasira bake -bake ta