Sashe 1
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data BEELAL *BILAL* NA MAMAN AFRAH Page1 *Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ba Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.* Rayuwa tana da matakai kala-kala, sannan tana cike da alubale wanda rayuwar ke sanya lamura su juya, wani lokacin idan ta maka wani sauyin sai ka ji tamkar an lasa maka zuma a baki.Sa anin wani sauyin nata da ke zama mafi munin ano tamkar ma aci.Kowane an adam yana da addara a rayuwarsa, wani rashin iyaye, wanda hakan yake sanya shi ya ji babu wani abu da ya fi maraici rashin galihu, wani kuma addararsa talauci musamman idan bashi da wadatar zuci .Sai ya auki hakan wani abu mai girma, wani ma har yake nema ya yi sa o, dan yana gani kamar shi ka ai aka toshewa hanyar samu.Wani kuma rashin abokin rayuwa na gari, wala mata ko miji, mai nagarta hakan na zama tamkar nakasu a duk rayuwar aya daga cikinsu, idan namiji ya yi rashin mce ta gari to tamkar ya rasa wani angare na jin da i ne a rayuwarsa.Manzo S.A.W ya ce duniya wani waje ne na jin da i amma mafi jin da in ta shi ne mace ta gari.A angaren mace ma rashin dace da abokin zama na gari idan bata dace da samun miji na gari ba mai tsoron Allah da kiyaye dokokin ubangijinsa, ta kan rayu ne a gidan aurenta tamkar baiwa, tana rayuwa ne ga ta dai a raye amma tana jinta tamkar matacciya! Domin za ta rayu ne a cikin gidanta, tamkar ma abarta take jin gidan nata, domin kuwa bashi da bambamci da kabari. Shi ya sa ake so a koyaushe mu nemi za in Allah, ba wai son zuciyar mu ba. Wannan tana daga cikin babbar addarar da mace take samun kanta a ciki, har hakan ke sanya ta ji ina ma bata yi auren ba, saboda babu wani farinciki da za ta yi ikirarin ta samu kanta a ciki daga mijin nata.Wannan addarar ita ce ta afkawa Fatima, domin kuwa gaba aya abubuwan nan guda uku ta samu kanta a ciki, maraici domin kuwa ta rasa gaba aya iyayen ta, da kuma kakaninta da suka taso a hannun su bayan rasuwar mahaifan nasu.Abu na biyu shi ne talauci, sai kuma uwa uba ginshi in rayuwar mace bayan barin gaban iyayenta idan ta yi aure, wato miji! Domin kuwa auren Idrisu ya sanya tana jin a koyaushe zuciyarta na cikin unci da takaici,ha e da, da na sani marar misaltuwa.Tana jin a ranta ina ma ba ta yi aure ba ina ma za a dawo da baya gaba da kuwa ba ta auri Idrisu a matsayin miji ba, da bata za i Idrisu abokin rayuwarta ba, da babu yadda za a yi ta za i Idrisu ya zame mata uban anta ba, domin kuwa Idrisu bai zame mata bango abin jingina ba.Dan kuwa ya yi watsi tare da yin fatali da duka awainiya da kulawarta da suka rataya a wuyansa.Hannu ta sanya ta share hawayen da ke ta safa da marwa tare da rige-rigen sakkowa daga kumburarrun idanunta, a hankali ta juya ta kai kallonta wurin da take ajiye kayan abincinsu, wasu hawayen ne masu zafi suka sake zubo mata domin kuwa ba ta jin akwai abincin da za su ci yau in nan, cikin sanyin jiki ta tashi daga kwancen da take tana jin jiri na ibanta ga kuma wani nauyi da zuciyarta ta mata tamkar an ora mata dutse, saboda tarin ba inciki da takaicin da ke unshe a cikinta ga yunwa da kuma rashin arfin jiki suka sanyata kwanciyar dole. aramin buhun da take zuba shinkafa ta duba duka bata fi gwangwani aya ba, bokitin da take zuba wake ta duba duk da ta san ya are amma sai take ganin idan ta bu e kamar za ta samu saura ko ka anne amma shi ma babu ko waya a ciki, haka ta dinga dudduba sauran ma'ajjin kayan abincin amma komai ya are hatta taliya ma kwalin ne kawai ta ajiye amma babu komai a cikinsa.Cikin sanyin muryarta wacce ta ci kuka ta oshi muryar har sha ewa take ta ce "Yaya shin me ya hanaki zuwa kwanaki da yawa, kinsan dai ke ka ai gareni kuma ke ka ai ke taimakona, wanda nauyinmu ke kansa da alama ma ya manta da wanzuwarmu a doron asa bare har ya tuna da ha inmu da ke kansa ya waiwayemu" Ta kai arshen maganar tana sakin wani kuka dan ita ba ta kan ta take ba, ta fi tausayin Beelal idan har ita za ta iya jurewa to shi ba lallai ya jure ba.Bare yunwa babba ma da yaya bare kuma yaro. Shinkafar nan ta akko ta fito daga akin nat,a tana so ta dafa wa Beelal kafin ya dawo daga makarantar boko in ya dawo ko da gishiri da mai ne sai ya ci, dan ta ga lokacin taso su har ya yi.Cikin sauri ta shiga ha a wuta da sauran itacen da suka rage, haka ta hura wutar ta ora ruwan duk da ba ta jin arfin jikinta. "Mai afa a lan washe" "Beelal" " Baki a karkace" "Beelal" " Hannu a lan washe" "Beelal" "Ba ya iya magana" "Beelal" Fatima ta jiyo muryar yara suna fa a da arfi suna tafi idan aya ya ce mai afa a lan washe, sai sauran yaran su ce Beelal, duk abin da ya fa a sai su masa amshi.Wani abu ne ya tokare mata a ma oshi tana ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, shin sai yaushe ne yaran gari za su bar anta ya sarara? Sai yaushe ne za su barshi ya yi karatu hankali kwance ? Shin mai ya sa iyayensu ba sa kwa arsu a kan abin da suke? Mai ya sa Malaman makarantar ko ta kai musu ara amma yaran ba sa dainawa, shin ba sa tsawatar musu ne ko kuma yaran ne suke da taurin kai? Duk cikin ranta take jefowa kan ta wa annan tambayoyi. Da sauri ta shiga aki ta akko hijabinta ta sanya ko gama dai daita wuyan hijabin bata yi ba, dan wuyan a karkace yake, hanyar ofar gidan ta nufa cikjin zafin nama tana jin tamkar idan ta fita ta fara dukan yaran sai an waci gaba aya yaran a hannunta.Tana fitowa ta ga dandazon yara ne an makarantar su Beelal in sanye da kayan makaranta suka rako shi kamar yadda suke yi a kullum.Idan ta aikeshi ko kuma in zai je gidan su Hameeda, haka zalika ko makaranta ya je bai tsira ba, hakan ya sanya ta gwammace duk inda za ta aike shi ta jr da kan ta.Tana fitowa suka fara watse wa kowa na kama gabansa, amma kuma bakinsu bai bar fa ar wa ar da suke ba.Beelal da ke dur ushe yana kuka sai Hameeda da ke tsaye a kansa tana kukan ita ma, cikin sanyin jiki Fatima ta nufesu tana arasawa Hameeda ta rungumeta tare da sakin kuka cikin kukan take cewa. "Mama wallahi kullum ba ma tsokanar kowa, amma su sai sun biyo mu hanya idan aka tashi daga makaranta suna tsokanar Ya Beelal babu abin da ya musu" Cewar Hameeda tana ara rushewa da wani kukan. Wani sabon kuka ne ya taho mata tare da tsananin tausayin yaranamma sai ta danne kukan dan tana so ta lallashe su, musamman take jin aunar Hameeda har cikin ranta saboda aunar Beelal da yarinyar ke yi ba tare da yamatarsa ba kamar yadda sauran yara ke yi kai har ma da manya, domin wasu ba sa duba da cewa kowane an adam Allah ke halittarsa, kuma uwa idan ta haifi a duk muninsa tana son kayanta sannan idan duk duniya za su taru a kan su canja wa mutum halittar da Allah ya masa babu wani abu da za su iya canjawa.Kawai mutane na shagala ne da abubuwan rayuwa har su kan manta cewa an adam daga ta o aka halicce shi, sannan mutum ba komai bane fa ce wanda aka samar daga igon maniyyi, sai dai an adam da ba a iya musu har suna iya tantance tare da bambamce kyakkyawa da kuma mummuna, ba i da kuma fari wani lokacin ma har ka ji ana cewa har da ruwan tarwa Mutane na mantawa cewar Allah shi ke samar da halittarsa, shi ne mahaliccin mutane da aljannu, shi ke yin su yadda ya so kuma babu wani an adam da zai iya ko da canza halittar farcen mutum ne! Amma ake cewa wance mummuna wane hanci shi gajere wance dogon goshi da dai sauran kushe halittu.Bare kuma a ce mutum nakasashshe ne, sai mutane su ora masa karan tsana ake masa wani kallo na da ban bashi da ikon shiga cikin jama'a kamar kowa bashi da halin aiwatar d rayuwarsa kamar kowa shin shi ne ya halicci kan sa? Ko shi ne ya ce a halicceshi haka? Ko kuma ita uwar an ce ta halicci an nata a haka, bayan ita ma bata ta a sanin mai za ta haifa b sai ranar da Allah ya adarta fitowar an duniya!!! Allah ne ya halicci masu tafiya a kan afa biyu (Mutane) Da masu tafiya a kan afafu hu u (Dabbobi) Da kuma masu tafiya a kan cikin su (Miciji d.s) Allah shi ke halittar abin da ya so. Hannun Hameeda Fatima ta kama ta ri e gam, ta ja ta zuwa inda Beelal in ke dur ushe ya kifa kan sa a gwiwa yana rera kuka kallon Hameeda ta yi yarinyar duka -duka shekararta hu u, shi kuma Beelal in shekararsa shida ita tana primary 1 shi kuma a primary2 saboda babu nursery a makarantar auyen nasu.Cikin sanyin jiki ta dur usa a gaban Beelal in tana jin wani tausayinsa na ara rufe ta, ga nakasa ga rashin galihu na uba! Hannu ta mi a ta kamo hannunsa mai lafiya ta ce. "Haba Beelal in Mama yaron kirki, kai da na ce maka duk wanda ya tsokane ka, kar ka yi kuka ka ce masa haka Allah ya halicceka ko zai gyara maka amma shi ne yau ka