← Book details Beelal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bai kawo ba kuma babu abin da ya kawo na tsaraba a tsawon shekara kusan biyu da baya nan kuma babu wata alama ta jin da i ko samun ku in da yake ta amar cewa nemansu ya tafi. "Ai ke baki da aiki sai kuka kullum cikin zubar da hawaye kike kuka kamar matar marigayi haka kike, dan na fa a miki gaskiya ina nuna miki hanyar samu shi ne ya zama lefi har kike kuka?" "Haba Baban Beel... "Kar ki sake kirana da Baban Beelal" Ya katse ta da sauri hakan ya yi dai dai da dawowar Hameeda da Beelal, maganar ta sauka a kan kunnuwansu, Hameeda da sauri ta juya ta fice daga gidan tana kuka, ganin yadda Beelal ya tsaya daga inda yake yana kuka. "Wai shin me kake yi haka ne me yake damunka, a kan me za ka haifi a da cikinka amma kake in sa har baka so a kiraka da sunan mahaifinsa to da sunan wa kake so a kira shi? Wai yaushe ne Beelal zai yi farinciki ya yi rayuwa kamar yadda kowane a yake yi babu yara ba tsangwama, kai kenan idan ka tafi Lagos sai ka kwashe sama da shekar baka dawo ba amma an zuwan da zaka yi ba zaka iy baiwa anka kulawa ba ko yaya take, sai dai ya samu musgunawa da untatawa daga jama'a kuma ya samu daga gareka ko tausayinsa baka ji, babu wata sha uwa ko soyayya tsakaninku, ta yaya kake tunanin zai ji an ka a nan gaba bayan kana untatta masa baka so ya ra e ka?" Duk an da ba a jin tausayinsa ba ya jin an wanda ba ya son sa, duk an da baya samun kulawa ba ya koyar yadda zai bada kulawa, ya kan tashi da ashashshiyar zuciya babu yadda za a yi a tan wasashi ko a tausasashi, domin an gama sanya masa rashin tausayi a cikin zuciyarsa duk da ba na fatan hakan daga Beelal amma ina fa a maka ne domin ka kiyaye" Ta fa a tana fashewa da kuka mai cin rai, dan babu wani abu da yake ata mata rai ya sanya zuciyarta tururi da mugun zafi sama da a atawa Beelal ko a yareshi ko ya aibata halittarsa wannna ka ai shi ne damuwarta, saboda bata son ko ka an Beelal yake jin sa kamar ba aya yake da kowa ba. "Lallai Fatima raini ya shiga tsakaninmu har kina da bakin da zaki fa a min magana son ranki, to lallai babu shakka wuyanki ya isa yanka, to da kike wasu maganganu waye ya mutu waye ya falko waye zai yi rai, ni ba damuwata bace hakan, kuma waye Beelal baki ga yadda halittarsa ma take ba bahu abin da ta dace a yi da ita sai dai bara maga Allah ma ga annabi ya bashi sai dai ya bi sahun an Allah baku mu samu, ta yaya zai samu abin da har zai kasa jin aina ko an fa a miki ni ina neman taimakon wanda yake neman taimako wanda shi ma taimaka masa yake so a yi, sannan da kike cewa Beelal ina cewa kar a ha ani da shi ake kirana da sunana Idrisu, ai ban ce ba ni na haifesa ba na dai ce na bar miki shi ne nan gaba idan kin haifi me lafiya sai ki kirani da ubansa" Kuka sosai kawai Fatima take tana jun tamkar ta tashi ta sha e idrisu ko ta samu sassauci daga abin da yake yiwa Beelal wanda abubuwan da yake masa ke ta a mata zuciya tana jin ina ma ita ka ai ake yiwa ba tare da aramin yaron da bai ji ba bai gani ba. A hankali Beelal ya taka daga inda yake tun lokacin da suka shigo da Hameeda ya arasa wajen Fatima ya dafa kafa ar mahaifiyarsa da hannunsa na hagu mai lafiyar ya ce. "Mama ki daina kuka, kike kirana da sunanki, tun da ke ko mutane sun ce miki Maman Beelal bakya cewa kar a fa a miki, shi Baba ki daina fa a masa tun da ba ya so" Ya fa a cikin in'innarsa yana kuka. Hannu biyu ta sa ta rumgumeshi tana kuka tare da bubbuga bayansa, yaro arami me shekara shida a duniya amma ya iya fiskantar matsalolinsa, har ya iya banbance mai son sa da wanda ba ya son sa mai aunarsa da wanda ba ya aunarsa, mai yamatarsa da wanda ba ya yamatarsa. "Hhhhh ashe dai ka gane yaro hakan ma ya yi wallahi, ka ga wata ila uwartaka ta ji shawararka ta daina dan ni na yi na yi da ita amma ta i dainawa" Cewar Idrisu yana aga kofin ruwa yana sha abinsa hankali kwance. "Wallahi Idrisu ka ji tsoron Allah kuma ka ji tsoron ranar ha uwarka da Allah, sannan ka tanadi amsoshin tambayoyin da zai maka a kan dannewa anka ha insa" "To malam me wa'azi da taoronki zan ji in ban ji tsoron Allah ba" Ya fa a yana tashi ya gyara zaman rigarsa ya shiga aki ya auno shinkafa kwano biyu daga cikin shinkafar da suka zo da ita ya fice abinsa zai je ya siyar, Fatima tana kallonsa amma babu yadda ta iya da shi, dan fa an da ya fi arfinka maidashi wasa, haka ta lalla a Beelal ya yi shiru, wayar tata ma Ummar Hameeda ta kaiwa ajiya sai bayan Idrisu ya tafi ta kar o har ku en da ta dawo da su ma duk ta bata ta ajiye mata sai bayan ya tafi ta kar o in ba haka na tana ji tana gani zai rabata da su. ~BAYAN SHEKARA UKU~ GIDAN SU HAMEEDA Bayan sallar isha'i ne Baban Hameeda ya shigo gidan ri e da ledarsa, sannu da zuwa Ummar Hameeda ta masa, ta kar i ledar lokacin Hameeda ta yi bacci dan lokacin tara na dare har ta gota, bayan ya ci abinci dama ya fita tsakanin magriba da isha'i shi ne sai yanzu ya dawo. Hirarsu suke shi da Ummar Hameeda abinsu, ledar da ya shigo da ita ta akko, aurin gya ar amaro ne a cikin guda biyar a ulle a wata ba ar ledar, sai kuma maganin era da ya siyo shi ma a ulle a wata farar leda irin wannan na barba awarne wanda yake cikin ar rakarda. Haka ta auki gyadar ulli uku ta juyo musu a faranti ta murje musu ta bushe awon gya ar, guda biyun kuma ta ajiyewa Hameeda, maganin meran kuma ta auka ta je ta adana dan ya ce sai gobe idan ya siyo kankana ko kifi sai a barba awa erayen a sa musu saboda sun damesu erayen su yi ta musu arna. Haka suka ci gya arsu suna hirarau, har suka cinye daga arshe dai suka yi shirin kwanciya. Cikin dare Ummar Hameeda ta falka da wani matsanancin ciwon cikin da ya sanya ko zaune ta kasa tashi, tana arin ta a Baban Hameeda sai ta jiyo sautinsa asa- asa yana cewa cikinsa, haka suke ta mur ususu babu me taimakon kowa ga shi ba za su iya ko da tashi ba bare su nemi taimako ciwon cikin ciwo ne me tsanani wanda suka kasa gane kansa da afarsa. ```Da safe``` Hameeda ta farka daga bacci, ta ga iyayen nata sun sauka daga shinfi a da yake kwanciyar waje ake, saboda zafi, sai Hameeda su kwanta da Umma shi kuma Baban nata a masa tasa shinfi ar. Ganinsu a asa kowa ya kama gabansa sai ta shiga kiransu tana ta jijjiga su ganin basu motsa ba ta fita da gudu ta kirawo Mamar Beelal haka suka taho hankalin Fatima a mugun tashe, tana zuwa ta ga kumfa sai fitowa take daga bakinsu babu alamar rai a tare da su, haka dai aka zo aka tabbatar da mutuwarsu dan har sun yi dafara, da aka bincika sai aka samu ashe gya ar nan ce ta yi ajalinsu saboda an ha ata da maganin era a leda aya duk da maganin yana cikin takardarsa kuma an ulleshi a farar leda, amma saboda guba ne ashe ya bugi ledar gya ar haka ne ya yi sanadin mutuwarsu. *Tsokaci*(Wannan abin na ha a maganun era da abin da za a ci ya faru da gaske, a cikin janairun wannan shekara da muje ciki ta 2023, .ma gidancin ya siyo abun ci a inda ya sako maganin era a ciki ganin yana ledarsa a ulle hakan ya sanya bai yi tunanin komai ba da kuma hakan ne silar mutuwarsu, sun ci abin sun kwanta suka mutu su uku miji mata da kuma ar su, jikar ce guda aya da yake da kwananta a gaba sai bata mutu ba, dan Allah jama'a mu kiyaye ha a abu wuri aya da poison, Allah kiyaye). Haka aka sallaci gawar Umma da ta Baba aka kaisu makwancinsu kuka sosai Hameeda da Beelal suka sha, haka aka yi sadakar bakwai aka watse, Yayan Baban Hameeda haka ya auki Hameeda ya mayar da ita gidansa gaba aya kayan gadon nata ya hau ka shi da matarsa sun mur ushe yana ganin babu mai masa magana tun da shi ka ai ubanta gareshi. Haka rayuwar Hameeda ta taso a wannan gida a hannun wa annan mutane mararsa imani. rayuwa ce marar gata da galihu, rayuwa ce da kowa ya ganta sai ya tausaya mata, hatta makaranta sun hana yarinyar zuwa bata komai sai yawon tallah, hatta Beelal an raba tsakaninsu da ita, sai dai idan ta fito talla ta je gidan su Beelal in a oye haka Fatima za ta bata abinci ta ci wani lokacin ma tsoro ya hana yarinyar cin abinci idan bata siyar da kayan tallar ba duka ake mata ga aukan ruwa kamar kwa uwa kullum tana fama da fanteka, tabbas yarinyar ta ga maraici iya maraici ga antar shekaru ga maraici ga mari a mararsa imani. Fatima ko sawu nawa za ta yi domin ta ga Hameeda ba za a barta ta ganta ba sai dai idan ta fito talla su ganta haka rayuwa ta cigaba da kasancewa a tare da yarinyar, sosai Beelal ke tausayinta har sai yake ganin ta fishi abin tausayi a kan tsokanarsa da ake
Chapter 24 · 0% Book details