Sashe 15
Beelal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da shi cewa an nisanta Beelal da gidansa sannan hankalinsa ya an kwanta. _Hajiya La ifa_ Tun bayan da Mai tsaron ofa ya sanar musu ganin da Alhaji Husaini ya yiwa Beelal suka shiga matu ar tashin hankali, gaba aya sun kasa zaune sun kasa tsaya suna ta jiran su ji daga Mai tsaron ofa game da yadda abun ya kasance dan sun tabbatar da asiri zai tono. Fatima da ita tafi kowa shiga tashin hankali sai kuka take tu uru tana da na sanin zuwansa gidan dama Kanon baki aya dan ko ka an bata son abin da zai ta a Beelal ji take da wani abu ya sameshi gwara ita abun ya same ta. Nasira sai faman lallashinta take yi duk da tana jin tausayinta tare da Allah wadai da wannan mummunar a ida ta gidan wannan da babu komai a cikinta sai jahilci. Hajiya La ifa ta kira Mai tsaron ofa ya fi a irga amma no answer hakan ne y mugun ara aga musu hankali. Fatima da ke zaune a kasan capet ta mimmi afa tana ta kuka ne ta ce "Dan Allah Yaya ko barni in fita in je wurin Beelal hankalina ba zai ta a kwanciya b idan har ban ganshi ba" "Ki yi ha uri Fatima zuwanki ba zai haifar da a mai ido ba, amma muke addu'a Allah ya zubawa abin ruwan sanyi yasa kar Alhajin ya fahimci komai dangane da shi" "Amin" Nasira da jikinta ya gama yin sanyi ta fa a tana bin su da kallo cikin tausayawa. aran kiran da ya shigo wayar Hajiya La ifa ne ya katse maganar da suke, da sauri ta duba wayar da dama a hannunta take ganin sunan Mai tsaron ofa ta aga wayar cikin fa uwar gaba. "Mai tsaron ofa ya ake ciki ne?" Ta tambaya cikin sanyin murya dan tsoron jin abin da zai fito daga bakin Mai tsaron ofa take. Nan ya shiga bata labarin gaba aya yadda abun ya kasance, da yadda ya yi aryar cikinsa ya aci da kuma yadda Beelal in ya kawar da tunanin Alhaji daga zargin da yake, sai dai maganar da ya fa a ce ta katsewa Hajiya La ifa murmushin da ya shimfi u a kan fuskarta, na labarin nasarar da aka samu, Fatima da ta mi e tsaye tun lokacin da Hajiya La ifa ta aga wayar ganin Yayarta ta na murmushin sai ta ji wani sanyi a ranta, amma ganin yanayin fuskarta ya sauya sai ta ji hankalinta ya tashi. "Suka tafi da Beelal in ina?" Ta tambaya hankali tashe. Wannan tambayar ita ce ta yi mugun agawa Fatima hankali jin wai an tafi da Beelal in?" MMN AFRAH *BILAL* NA MAMAN AFRAH FCW Da sunan Allah mai rahma mai jin ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah ma aukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin. *This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* Book 1 Page1 "Ina suka tafi mini da ana, ina suka kai shi?" Cewar Fatima cikin muryar kuka dan jin Hajiya La ifa na cewa an tafi da Beelal sai ta warce wayar daga hannun Yayarta ta. "Dan Allah ki yi ha uri, ni kaina ban san inda suka kai shi ba, kawai dai Alhajin ya ce musu su fitar da shi daga unguwar to yanzu sun ma da e da dawowa daga kai shin" Ya fa a cikin sanyin murya jin yadda Fatimar ke kuka da kuma yadda rauninta ya bayyana a muryarta za ka fahimci hakan. Sakin wayar Fatima ta yi ta cigaba da cewa "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allahu ma ajirni fi musibati waklifni kairan minha" Cikin sauri Hajiya La ifa ta auki wayar, Nasira kuma sai ta yi ka Fatima da ta ga ta yi tangal-tangal za ta fa i, tana arasawa kuwa kamar jira Fatima take ta tafi za ta fa i Nasirar ta tare ta sai kuwa ta fa a jikin Nasirar yif a sume. Hajiya La ifa gaba aya abu ya taru ya mata yawa hakan ya sanya ta yi ta maza ta danne kukan da ya taho mata dan ganin anwarta tilo babu numfashi Nasira ta jijjigata da kiran sunanta hakan ya bala'in aga mata hankali. Tana tsoron ta rasa ar uwarta da ta sha u da ita, a gefe aya kuma ga tunanin yadda za a tafi neman Beelal yaron da ba cikakkiyar lafiya ba gareshi ta san ko da a ce za a taimakashi ne to fa ba kowa ne zai taimakeshi ba saboda nakasar da ke tare da shi, dan wani gudun wahala da awainiya ma ba zai bari ya taimaka masa ba, bare yanzu ma a wannan zamanin da kowa ke ta kansa saboda hali da matsi na rayuwa iyalin mutum ma da yaya bare kuma ya auki awainiyar bare, ba ma wannan ba shin wane loko da sa o za a tafi neman Beelal? Waye ma zai tafi neman nasa? Ta ina ma za a fara nemansa? Tabbas neman mutum a gari mai girma kamar gari Kano ba abu bane mai sau i, cikin wannan sa e-sa en da zuciyarta ke mata ta tsinkayo maganar Mai tsaron ofa ta cikin wayar yana cewa "Hajiya bakya ji na ne?" Hannu ta fara kaiwa ta share hawayen nata kafin ta ce "Mai tsaron ofa ina suka kai mana Beelal? Shin ka san ya Beelal yake a wurinmu?" Ta sake jefa masa wata tambayar ba tare da ta jira ya bata amsar tambayarta ta farko ba. "Hajiya babu yadda zan yi ne, Allah ne ma fa ya taimaka da yaron nan bai bayyana cewa mahaifiyarsa na cikin gidan nan ba" "To ai wallahi gwara ya fa i cewa mahaifiyarsa na cikin gidan nan, in ya so a mana duk abin da za a mana a arshe dai na san bai wuce aurena ya mutu ba, a kan a ce an jefar da Beelal babu ta inda muke da tabbas in samun yaron nan" Ta fa a hawaye na zubo mata. Ajiyar zuciya Mai tsaron ofa ya sauke, jin muryar Hajiya La ifa ya san kuka ita ma take sannan ya ji lokacin da Nasira ke kiran sunan Fatima tana kuka tana ambaton ba ta numfashi, tabbas ya kamata ya yi wani abu a kai a matsayinsa na namiji dan su duk mata ne mata kuma akwai su da rauni ga zuciyarsa ta kasa barshi ya yi sukuni da tunanin Beelal saboda tana tariyo masa kukansa a lokacin da za a aukeshi yana jin lokacin da yake cewa "Jakar kayanmu, ku barni na auki jarkarmu" Amma ko sauraron yaron basu yi ba suka sanyashi a mota. Sannan shi kan sa ya san irin karamcin Hajiya La ifa a garesu tabbas ba zai manta ba cewa wata rana lokacin ba a hana su fita unguwa ba za ta fita siyayya tana cikin mota direban yake horn, horn in ne ya katsewa Mai tsaron ofa tagumin da ya yi, da kuma dogon tunanin da ya lula, hakan ya sa ya tashi da sauri ya bu e get in, Hajiya La ifa ta dakatar da direban ta bu e glass in mota ta yiwa Mai tsaron ofa alamar ya zo da hannu, da sauri ya zo cikin girmamawa, sai ta tmbayeshi damuwarsa a nan yake fa a mata cewa mahaifinsa ne ba lafiya kuma wata ya yi nisa bashi da ku in da zai kai shi asibiti, hakan ta bu e jakarta ta akko ku e masu yawa ta bashi. Tabbas ba zai ta a manta alkairanta gareshi ba, amma wannan shi ne wanda yake kasa manta irin fitar da shi da mahaifiyarsa, wacce ita ma ke cikin damuwar rashin lafiyar mijinta daga matsananciyar damuwa, da kuma ceton rai da ta yi na mahaifinsa. "Hajiya in sha Allah idan duhun magariba ya shiga zan fita neman Beelal, zan bi sawun hanyar da suka bi, da yardar Allah zan gano in da yaron yake" "Haba Mai tsaron ofa yanzu har a bari zuwa magriba duka -duka fa ba a da e da yin la'asar ba kar yaron nan ya yi wano wajen" Hajiya ta fa a tana jiran amsar sa. "Hajiya hakan shi ka ai ne mafits saboda matu ar na fita yanzu za a gane, kuma ni ba na so ku shiga cikin matsala idan kuka fito amma zuwa magriba idanu ya auke sai na saci jiki na tafi nemansa ba tare da sanin kowa ba" "To nagode warai Mai tsaron ofa" "Ba godiya tsakaninmu Hajiya, kin cancanci fiye fa hakan ma" Kashe wayar Hajiya La ifa ta yi tare da nufar wajen ar uwarta da Nasira ta kwantar ta tafi akko ruwa a frige, Nasirw na kawo ruwan aka zuba mata, sai da aka zuba mata sau uku sannan ta an motsa hannunta, ka an sai kuma ta saki numfashi, cikin fatinciki Nasira da Hajiya suka shiga kiran sunanta. Fatima kuwa bata san abin da suke ba, dan ba a hayyacinta take ba, kawai dai numfashinta ya dawo ne. Idanunta na a rufe take kiran sunan Beelal hakan ne ya sanya Hajiya jin wani tausayin ar uwarta ta, kama-kama suka mata suka hau da ita sama saboda gudun kar wani ya shigo, a aya daga cikin akunan suka kwantar da ita a kan gado har lokacin tana kiran sunan Beelal.Tana a hakan sai bacci ya yi awon gaba da ita hakan ya sanya Nasira da Hajiya suka fito suka rufo mata akin, dan sosai Hajiya ta ji da i da bacci ya auke Fatima dan ta san matsawar idanunta biyu ba aramin tashin hankali za ta shiga ba da rashin Beelal, hakan ya sanya Hajiya addu'ar Allah ya sa lokacin da za ta falka an samo Beelal.