← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 48

Sashe 6

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuwa Babban Yaya baisan sunayi Bama 😂Kallan intisar yayi yace "ke tashi ki kira wannan yarinyar tazo tayi kallo"

Intisar tasan da Waheeda yake, ita kadai ce bata futo falo ba, cikin sauri ta nufi dakinsu, tana shiga tahau kan gadon ta yaye bargon da Waheeda tarufa, bude idon ta tayi ta kalleta, duk yanda Waheeda take gane yanbiyu, take banbancesu dukda tsananin kamar dasuke, yau kasa ganesu tayi,🤣 intisar ce tazo kiranta Amma Waheeda tana qare mata kallo cikin wahala tace "Ihsan Dan Allah ki temaka ki taro ruwan zafi a toilet kizo ki gasa min cinyoyina, jikina yayi tsanani bazan iya tashi ba"

Dariya ta kama Intisar, saita danne gudun karsuzo suna fada, tace "Babban Yaya ne yace kifuto kiyi kallo kowa yana falo banda k....." kafin ta qarasa magana taga Waheeda ta duro daga kan gadon 😂
Kokula sauran zancen batayi ba tafice daga Dakin, tana zuwa falon babu Wanda ta nufa Sai shi, har gefen qafarsa ta zauna, hawaye yazubo daga idanunta, a Hankali tace" Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri kaji.... "

Babu Wanda yasan metake fada masa, saboda ahankali tayi masa maganar, Shikuwa banza yayi yarabu da'ita, hawayen tasake gogewa tace"kaji" memakon yabata amsa saiya tashi daga falon yashige dakinsa, haka ta zauna a wajan tana Kallan dole, saida takusa minti talatin tana kallo Amma bata fahimtar komai, Dan haka tatashi Takoma dakinsu tafara gabatar da sallah

Karfe bakwai daidai afalo tayi masa,yayi kyau sosai cikin manyan Kaya, yanda yaqara cika da kamala zakace yanada aure, agogon hannun sa ya kalla yadubi Ummah yace "kice musu Idan sun gama Ina waje Ummah"

Ummah tayi dakin yaran tace "kuyi sauri kufita yayanku fa kuyake jira"

Yanbiyu ne suka futo sun shirya cikin uniform dinsu, suna zuwa compound din suka hangeshi yana Dukan tayar motar da qafarsa yana Kallan agogo, suna ganin haka suka qara sauri suka shige motar, shida Kansa yayi driving din, Kai tsaye yanufi makarantar su

Suna zuwa kuwa Kai tsaye yanemi iso zuwa office din director, teachers dinsu maza Wanda suke harkar ball suna ganinsa suka fara zuwa suna gaisawa dashi, yana gaisawa da director yanemi afwa akan yanbiyu, babu bata lokaci sukace komai ya wuce Yara sukoma aji, Amma waccan dayar de kar akawota bazasu karbeta ba

Duk da haka saida yaqara basu hakuri sannan yayi musu ihsani yafuto daga makarantar, daga Nan ma ba gida yakoma ba, kofar fada ya nufa, yana tambayar gidan Alhaji Hamza aka nuna masa, futowa yayi ya jingina da motar yace ayi masa sallama dashi, Alhaji Hamza yana futowa yaga farin buzu a kofar gidansa, qarasa wa yayi yabashi hannu suka gaisa, Babban Yaya yace "Alhaji sunana Naufal, da Alhaji Hamza nake magana ko?"

Alhaji Hamza yace "nine samari, ba kaine yaranmu suke cewa Big Brother ba?"

"nine Alhaji, dama nazo ne akan maganar qanwata dakuma Yaron wajanka Aryan"

Alhaji Hamza yace "to menene yafaru?"

"Alhaji, Yaron wajanka yana soyaiya ne da qanwata, shine nazo muyi magana akan yaturo iyayensa idan aure zaiyi yanzu"

Alhaji Hamza yace "Wai Aryan wannan Dana Sani Dan wajena kake magana akansa?"

"shide Alhaji"

Murmushi Alhaji Hamza yayi yace "samari Aryan fa shekararsa goma shatara ne Idan nayi lissafi daidai, tayaya za'ayi masa maganar aure yanzu?"

Babban Yaya yace "hakane, to ita yarinyar dayake nema aurenta zamuyi, saboda haka Dan Allah Alhaji ajawa yaro kunne yadena bibiyarta, jiya matsala ce tafaru a makarantar su har hakan yasa suka Koreta daga makaranta, so aja masa kunne please"

Alhaji Hamza yace "Subhanallah, ashe yar'uwarka ce yaro, to kuyi hakuri Dan Allah, insha Allah zanyi wa tufkar hanci"

Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi gida

Yana zuwa gida ya tarar da Hajiya Anty da Ummah afalo, can ya hangi Waheeda a dinning tana cin abinci
kwanciya yayi akan doguwar kujera ya Dora Kansa akan cinyar anty yasaki wani irin murmushi dimples dinsa suka lotsa duka biyun yace "Anty nah ta kaina"

Sumar Kansa ta shafa tace "yayansu nayi fishi, kazo Amma koka leqoni, yanzu ma sannu da zuwa nazo yima dakuma wani albishir"

Hannunta datake shafa sumarsa yariqe yayi kissing Bayan hannun sannan yace "Ina jinki Hajiya Anty"

Tace "wallahi wata yarinya ce take zuwa Asbiti Ina dubata lokaci zuwa lokaci, shine nayaba da Hankalinta, nace zan turo mata Dan yayata su daidai ta ko Allah zaisa ayi abun da'ita"

Cikin sauri ya tashi daga kan cinyarta yace "Anty me kikace?"

"abinda kaji nace"

Kansa ya shafa yace "Anty Kode neman Kai kuke Dani ne?"

Tace "mekake nufi yayansu?tayaya zamu nemi Kai dakai?"

Bata rai yayi cikin shagwaba yace "to Anty gashinan Kuma arasa da wadda za'a hadani Sai majinyaciya?"

Ummah ce tasa musu baki tace "tunda kaqi lafiyayyu ai sai kakoma kan majinyata" tajuya ta kalli hajiya Anty tace "ki fada masa komai, kidena wani Lalla bashi"

Hajiya tace "yayansu harna yiwa uncle dinka maganar yarinyar shida Dadynka, Amma Kai Yaya kagani?"

Ummah tace "Yaya zai Gani kuwa? Yama amince kawai"

Tashi yayi daga wajan su yace "to Anty idan nasamu lokaci zanje naganta"

Ummah tace "yaushe zakaje?"

Kansa yadafe da hannun sa 🤦🏻‍♂️yace " wayyo Allah Ummah, zanje wallahi, anjima zanje"

Anty tace "to idan katashi zuwa ga wannan kayan kwalliyar kakai mata"

Uwar ledar data turo masa gabansa ya kalla, cikin ransa yace Dama de sun shirya komai
Yace "to"

Bai dauki ledar ba ya wuce ta gaban Waheeda yayi dakinsa,yanaaji yana cewa "good morning Babban Yaya" Amma ya shareta
wani qullutun taqaici ya to kare mata maqoshi, tasan yanzu Babban Yaya ya tsaneta, gashi ya maida yanbiyu makaranta Amma banda ita.

Hajiya Anty tana tafiya gida Waheeda taje wajan Ummah ta zauna, Ummah ta kalleta tace "Lafiya Waheeda?"

Girgiza kanta tayi tace "Ummah, Babban Yaya baya sona yanzu, ya tsaneni"

Ummah ta kalleta tace "yayanki uwa daya uba daya tayaya zakice baya sonki Waheeda? Halinki ne baya so, Waheeda bakya jin magana, saikin masa laifi Kuma kizo abun ya dameki, yanzu ni me zanyi muku akan haka?"

Idanunta ne yayi qwalqwal hawaye yana shirin futowa tace "to Ummah kinajifa nagaidashi Amma ya share ni"

"bai gama hucewa bane, kibari zuwa anjima ai zai sauko"

Hawayen data riqe ne ya silalo daga idanunta, tasa hannu ta share, sannan tayi dakinsu domin ta watsa ruwa

Umma na ganin tafiyar ta ta nufi Dakin Babban Yaya, yana kwance agadon sa yayi mata shi da hannayensa, duniyar tunani yatafi ita wannan yarinyar ta wacce hanya zaibi yarabu da'ita?

Turo kofar tayi tashigo, yana ganin shigowarta ya tashi zaune, zama tayi akusa dashi tace "Yayansu, magana nakeso muyi"

Nutsuwa yayi yace "to Ummah"

Tace "akan Waheeda ne, yakamata kadinga Jan 'yan'uwanka ajiki, qannanka ne bakada kamar su, idan Bama Raye kaine zasu kalla a matsayin ubansu, yarinya qanqanuwa Waheeda har tana min magana akan rashin kula da'ita da bakayi, tacemin yanzu kadena sonta, hannunka fa baya ru6ewa ka yanke kayar, yakamata kadinga janta ajiki kanuna mata fari da baqi, tunda Dukan bazaisa ta sauya ba saika dinga yimata nasiha "

Kallan ta yayi yace"Ummah nasiha bazata shiga qwaqwalwar yarinyar nanba, batajin magana, kullum itace takemin sanadin zuwana Nigeria "

Ummah tatari numfashinsa tace" kaikuma gashi baka son zuwa Nigeria saboda kar muyi ma maganar aure ko? "
Qasa yayi da Kansa yace" Bahaka bane Ummah, insha Allah zan jasu ajikin kamar yanda kikace "

Tashi tayi tsaye tareda fadin" Allah yamaka Albarka "

Cikin jin dadi yace"Amin Ummah tah"

Dayamma suna kallo afalo, Amma dukansu su ukun suna saka kayan makarantar islamiya, jira suke kawai lokaci yayi sutafi, futowa yayi daga dakinsa yayi wankan qananun Kaya kamar ka saceshi kagudu, wandon Jeans yasaka baqi, Sai Riga me kama jiki ruwan toka, dakuma yar sama me ratsin baqi, yasaka kambos Shima baqi me ratsin brown, yayi kyau sosai sumar Nan tasa Sai sheqi take, Ummah ta Kalle shi tace "masha Allah, yayansu Sai ina?"

Kansa ya shafa yace "inda hajiya Anty tace naje"

Fara'ah ce ta wanzu a fuskar Ummah, tace "kace gidan surukar tawa zakaje, irin wannan wanka haka ai dole a dedeta, Bari in Dauko Maka kyautar Tata"

Baice komai ba, yanemi kujera ya zauna, tareda daukar remote ya maida tashar Kallan ball, Kallan Waheeda yayi, suna hada ido tayi qasa da kanta, yace "4 o'clock kuke tafiya islamiya ko?"

Atare suka amsa da "eh"

Yasake dubanta yace "tashi ki rakani"

Cikin murna tatashi tayi dakinsu, farinciki take yayan Nata da alama yahuce, uniform dinta tacire tasaka doguwar Riga, sannan ta dauki dogon hijab dinta tasaka, tana futowa Ummah ma tana futowa daga daki, ta bashi ledar kayan, ya nuna mata Waheeda ataqaice yace "bata"

Ummah tace "yanaga kincire uniform din ko tare zakuje zancen?"

Waheeda tasaki wani murmushin jindadi, tace "eh Ummah"

Kallan ta yayi sosai, sautari idan yarinyar tayi wani abu saiya ga Takoma photocopy dinsa sak, musanman idan tayi dariya ko murmushi duk dimples dinta suka bayyana kamar de nashi, kauda tunanin yayi daga ransa yafita daga falon ita Kuma ta Mara masa baya, saida tajuyo tayiwa yanbiyu gwalo 🤪Sannan tafita

Ummah ta girgiza kanta cikin ranta tace gaskiyar sane daya ce bazata sauya ba

Motar dasuka shiga glass din motar tint ne, ba zakaga naciki ba, mafi yawan lokaci irinta yake Hawa saboda shi mutum ne na mutane, ko Yaya yafuto awaje dole ne kasamu Wanda yasan shi
Suna cikin tafiya ya kalleta yace "Bani labari"

Kallan sa tayi tace "Babban Yaya wanne labari gashinan muna shirin zuwa Naga Anty"

"wacece Anty?"

"Babban Yaya wadda zamuje wajan ta, budurwarka, harna matsu naganta wallahi"

Haushi ne yakama shi, yace "to naji Dan Allah, ni labari nace kibani bawani shirme ba"

Kallan sa tayi, cikin ranta tace zancen budurwar tasa yake cewa shirme to in hakane komai ma ta fada bazai birgeshi ba, duk da haka saita Juyo tana fuskantar sa tace "Babban Yaya inaso Naga kana Ball, ka'iya ball sosai, wani lokacin idan ka saka qwallo araga Sai inji jikina yana tsuma kamar nice nasaka"

Dariya tabashi, saida yayi dariyar sa sannan yace "ke meyasa bazaki Koya ba?"

"Bayan wacce kake Koya mana agida?"

"yes, idan kinaso saina sake Koya muku"

"muna so wallahi Babban Yaya,nafiso nafi yanbiyu iya Ball"
Chapter 6 · 0% Book details