← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma tayi banza dashi,Shima Dama Kiran Nata dayake qarfin Hali ne kawai, dama baya so tajuyo 😆
Babu musu yashiga cikin adedetan yatafi, yana zuwa wajan Dan adedetan ya futo yabashi key dinsa yace "nagode gashi"

Dan adedeta yace "Wai harka gama? Naga ko Minti talatin bakayi ba"

Motar sa yabude yashiga yace "nagode"

Cikin sauri Dan adedeta yace "toga agogon Naka"

Babban Yaya yace "Kabarshi kawai" yarufe motarsa yatafi,saboda hadari ne yake San tasowa, Kuma yanaso yaje ya Dauko su Waheeda a islamiya

*** ** ***

Tafiya suke ahankali suna zancen su gwanin sha'awa, Maya tace "Waheeda ki dinga sauri mana, ko bakya ganin hadari"

"ke barni inyi tafiya ta yanda nakeso, idan sauri nakema jikina ya dinga rawa kenan, nikuma banason wannan rawar"

Maya ta kwashe da dariya tace "su Waheeda manyan yanmata, zan so Naga mijinki Waheeda"

"Zaki Gani Maya, kijira munayin candy Sai aure nikam, banaso naci gaba da karatu, nafiso nayi aure na indinga kula da mijina, in shaga6ashi inyi masa abinda yakeso, kinga lokacin saina tafi makaranta, tun yanzu ma mata suna nemana, idan natafi University wakike tunanin zai nemeni? "

Kai tsaye Maya tace"Maza, Amma Kuma kinsan de Babban Yaya baya so ki dinga kula samari ko? Tayaya Zaki samu mijin? Bayan munkusa gama makaranta?"

" can ta matse muku keda Babban yayan, nikam daga Candy Sai aure insha Allah "

Maya tace"gaskiya yarinyar Nan wuyanki ya'isa yanka, nikam yanzu Ina Bayan Babban Yaya, tunda yabani kudin makaranta bazan taba mantawa da alkhairinsa agareni ba, Dan haka dole indinga tuna miki dokarsa a kanki "

Kafin Waheeda tace wani abu anfara yaiyafi, neman wajan 6uya suke Amma sun Rasa, abun Hawa suka fara tarewa Amma kowanne baya tsaya wa, ruwa yaqara karfi Nan da Nan mutane suka fara gudu musanman maza, ruwa yayiwa su Waheeda duka saboda babu mafaka, suna cikin wannan halin Babban Yaya yaqara so, yana zuwa yafuto daga cikin motar yanufesu, Waheeda taga ya sauya wannan kayan daya saka na dazu, murmushi tayi, cikin shagwa6a tace "Babban Yaya shine kaqi zuwa da wuri gashinan ruwa yamana duka nida Maya"

Bece da'ita komai ba, kawai gaban motar yabude mata, tareda fadin "I'm sorry, shiga"

Maya tana tsaye tana Kallan su, lalle Babban Yaya yana son Waheeda, wanne Yaya ne zai budewa qanwar sa mota saikace wata budurwar sa? Anya kuwa yayanta ne?

Saida Waheeda tashiga sannan yarufe, itama Maya tayi sauri tabude gidan baya tashiga, zagayawa yayi yashiga motar, yajuyo yana fuskantar Waheeda, cikin sigar lallashi yace "Sorry"

Bakinta ta turo gaba taqi magana, yasaka hannu yakamo kyakykyawar fuskarta yace "kinji"

Murmushi tasaki, dimple dinta suka futo, tace "shikkenan, Kuma alqawarin dazu, bazan fadawa kowa ba"

Murmushi yayi Shima yace "good girl"

Maya tayi gyaran murya, Dan taga alamun sun manta tana motar 😂
Tace "Babban Yaya Ina wuni"

Firgigit ya dawo haiyacinsa, shaf ya manta tana cikin motar, a taqaice yace "Lafiya"

Sannan yaja motar suka tafi, suna hanya Waheeda Sai zuba masa surutu take, Amma amsar dayake bata batada yawa, har suka qaraso gidansu Maya, suka ajiye ta sannan suka dauki hanyar gida, Bai wuce dasu gida ba saida yashiga tawani shago yasai mata waya qirar iPhone, ya ajiye agaban motar sannan yaja motar suka qarasa gida

Yana tsaida motar a compound din gidan nasu, Waheeda tafara kokarin fita, tana kama handle din kofar taji taqi buduwa, tajuyo tace "Babban Yaya bude"

Wayar daya siyo ya Dauko ya 'Dora mata akan cinyarta yace "Gashinan, nasan inda kinada waya Zaki kirani kicemin kun tashi, bazan Bari ruwa yamiki duka ba kamar yau"

Waheeda tafara kokarin budewa, tana Ganin wayar tasaki wani ihun murna ta rungume shi, yana jin yanda tudun qirjinta yake mintsininsa cikin ransa yace "yasalammmm!"

Daurewa kawai yayi, ahankali yazareta daga jikinsa yace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba, kina ta6ani any how kamar wani muharraminki"

Kwata kwata Waheeda batama kalli inda yakeba bare tayi nazari akan kalamansa, cikin murna tace "Toda menene inba Shiba? Babban Yaya, nagode, Allah yasa kadinga cin ball a koda yaushe, Allah yaqara girma"

Saida ya hadiye wani irin yawu, sannan yace "Amin" yabude mata motar tafita dagudu tanaso ta nunawa yanbiyu itama tayi waya

Da daddare suna kallo gaba dayansu, Waheeda tana saka number Yan gidan tana saving dinsu cikin sabuwar wayarta, yanbiyu suna nuna mata wasu abubuwan da bata Sani ba, su Sa'ad da Sa'eed tareda Babban Yaya Sai labarin qwallo suke, Babban Yaya anta6o masa inda yakeso, wato zancen qwallo, Sai hira suke sunata dariya kamar bashi ba, Ummah ta Kalle shi tace "Yayansu Yaya kukai kaida Nadiya ne?"

Kallan ta yayi yace "Ummah naje tace bata sona"

Gaba dayansu Yan falon suka Juyo suna Kallan sa, wacce yarinya ce zatace bata son yayansu?

Ummah tace "kamarya?"

Juyowa yayi yasake Kallan Ummah yace "Ummah ki tambayeta kiji, naje nace mata Ina sonta, kifada mata nine naje da adedeta saboda motata tasamu matsala a hanya, Kuma tace koda na aureta bazata iya kula dakeba Ummah,sannan tare naganta dawani Gaye suna zance, kinga kenan itama tanada Wanda takeso,to menene amfanin auren ta? Ummah duk wadda bazata iya kulawa da mahaifiyata ba, bazan iya auren taba "

(Kai Babban Yaya irin wannan batu haka 🤣😂)

Ummah tadauki wayarta takira wayar maman Nadiya, Bayan sun gaisa maman Nadiya tace
" Hajiya Baqon namu Kuma baizo ba, muna ta jira angama shirya masa abin motsa baki Amma Nadiya tacemin baizo ba Kuma bai kira wayarta ba"

Ummah tace" Yanzu nake tambayar sa yacemin yazo tace masa bata sonsa, Wai tace bazata iya kula daniba koda ya aure ta"

Maman Nadiya yace "Anya hajiya itace kuwa? Amma Bari inkirata"

Ummah tanaji maman Nadiya ta daga murya takira Nadiya, nadiya tana zuwa maman ta tace "Big Brother yazo kince masa bakya sonsa, kince kokin aure shi bazaki kula da umman saba, anyi haka ko ba'ayi ba?"

Nadiya tanajin wannan bayani tatuna mutumin dayazo wajan ta dazu a adedeta, ta d'ora hannunta aka 🙆🏻‍♀️tafashe da Kuka tace "wallahi mama bansan shibane, yaudara ta yayi, Allah Ina sonsa" cikin kuka tanufi dakinta da gudu

Maman Nadiya ta sassauta murya tacewa Ummah "Hajiya komai fa ya lalace, zamuyi magana daga baya" daga Nan ta kashe wayar

Babban Yaya ya kalli Ummah yace "Ummah kinji da kunnanki ai naje ko?"

Cikin bacin rai Ummah tafara girgiza kafarta tace "naji Naufal, ai banyi tunanin yarinyar zatace bazata kula daniba, bansan haka tarbiyar ta takeba"

Wani farin ciki ne ya mamaye shi, yaga Ummah ta yarda da komai, to tun kafin waccan Nadiyar tazo ta musu bayanin komai ta fada musu 6oye kamarsa yayi, Gara yagudu yabar qasar😂

Cikin ladabi yace "Ummah, muna shirye-shiryen fara World cup very soon, zan fara training Jibi, Insha Allah gobe da Asubar fari zan wuce" 😂😂

Ummah tace "Allah yakaimu Son"

Firar da ba'a qarasa dashi ba kenan, ya wuce dakinsa ransa fess👌🏻

Sonake agano min iyayen wadannan taurarin guda biyu NAUFAL DA WAHEEDA

To Babban Yaya yatsira wannan lokacin, kome Waheeda zata aikata ya dawo dashi qasar?

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

11&12

Suna tashi da safe sukahau shirin school,awajan break fast Waheeda taga babu Babban Yaya, anan taji cewa yatafi tun asuba kamar yanda yafada jiya da daddare

Bataci wani abincin kirki ba, Sai tea me kauri, ta kalli 'yanbiyu taga Sai lokacin zasu fara cin abincin, tatashi tayi d'akinsu da gudu

Kowa yabita da kallo Amma babu Wanda ya tanka mata, wayarta tad'auko ta kunna ta sannan takira Babban Yaya, a lokacin suna cikin jirgi har anfara sanarwa a kashe waya jirgi zai tashi, yayi mamakin ganin number ta tana kira, already yanada number tun jiya yayi saving d'inta a wayarsa
Dauka yayi tareda cewa "Lafiya ko laifin kika sake yi?"

Dariya tayi tace "Babban Yaya,Aina Dena laifi yanzu, nayi Hankali Nima"

Yace "Allah yasa, kinga de wannan Karon munrabu lafiya dake, banaso wani abu yasake faruwa kisa in dawo qasar Nan kwana kusa, kinga yanda nasamu narabu da rigimar su Ummah akan yarinyar Nan Nadiya, to banaso kisake aikata wani abun dazaisa nadawo Nigeria ta dalilin ki "

Bakinta ta turo gaba kamar yana Kallan ta, sannan cikin shagwa6a tace" Babban Yaya to ai wannan dinma ba nice da laifi ba, Basaida na nuna ma abinda akamin ba?"

Runtse idonsa yayi, Waheeda zata kashe shi, yadade da mantawa Amma saida tasa ya hango cikakkun breast dinta a'idon zuciyar sa, cikin sauri yace"naji,naji, menene Kuma saikin tuna min?" 😂

Tace "to Babban Yaya kayi hakuri, yaushe zaka dawo?"

Kai tsaye yace "Babu rana, kuma nafada miki banaso kema kiyi sanadin zuwana Nigeria"

"Angama Babban Yaya, Allah yakiyaye hanya" daga haka ta kashe wayar Tata, Takoma falo,Ummah ta kalleta tace "lafiya?"

Tace "Da Babban Yaya nayi waya"

Sa'eed yace "um kaji masu waya"

Dariya tayi kawai, ta jira yanbiyu suka gama sannan suka fita compound driver ya daukesu suka tafi

Bayan uncle ya fita daga ajin nasu,Maya ta kalli Waheeda tace "Waheeda waiya kuke da Babban Yaya ne?"

Kallan Maya tayi tace "Kamarya ya muke? Mekike nufi?"

Maya tace "Ina nufin Wai Ummah ce ta haifeku dukanku?"

Kai tsaye tace "itace mana, me kikaga?"

"babu abinda nagani Waheeda, kawai de Naga kinshaqu dashi fiyeda yanbiyu, sannan Shima yana sonki sosai, shine nace koba Ummah ce ta haifeku ba"

Waheeda tayi mata wani banzan kallo tace "toba Ummah ce ta haifemu ba waye yakawo mu duniya Kenan? Nasan nashaqu dashi yanda bakya zato, saboda tun Ina qarama nasaba dashi, sannan dakika ce yanaso na wannan Kam Ina tantama, saboda idan yana sona ma, to wannan soyaiyar dayakemin bata hanashi yamin hukunci, idan nayi laifi zaneni yakeyi wallahi, kinbani mamaki Maya, ashe zarginmu kike "

Maya tace" innalillahi.... Waheeda zargi Kuma? Meyasa zan zargeku Bayan yayanki ne uwa d'aya uba d'aya? Kawai de kun birgeni ne jiya danaga yanda yake baki kulawa, harfa mota yabude miki, shine nayi tunani idan ku masoya ne abun zaifi dadin Gani, yana miki soyaiya kina maida masa martani "

Cikin masifa Waheeda tace" A'uzubillahi.... Maya kamar wata marar Hankali Zaki dinga dangantani da yayana?"

Maya ta kamo hannunta tace" yi hakuri qawata, nabata miki rai, kiyi hakuri Dan Allah "
Chapter 13 · 0% Book details