← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 48

Sashe 40

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"babu rana" yafad'i hakan ransa a6ace, itama tanajin wannan furucin taja bakinta tayi shiru, tasan cewa ransa a6ace yake

Bata d'auki komai ba, kawai hijabinta tasaka, suka tafi, suna zuwa compound din gidan Ummah yayi parking,kafin suyi sallama yajuyo ya kalleta yace "karki dinga wasa dasu Ihsan har kuzo Ana rabaku akan abinda baikai yakawo ba,nasan halinki bakida kunya, kikama girmanki, da da dayanzu ba daya bane, duk abinda kike buqata kidauki ATM dina kije ki siyo kokuma kisa su Sa'eed su siyo miki"

Tace "Babban Yaya, kaida kace yanzu na girmi Ihsan nikuma tayaya zan kulasu har muyi fad'a?"

Cikin sauri yace "tayaya kika girmesu? Bayan kinqi Bani damar dazan maidake Antyn su?, Ina ta6abaki Sai kuka, ko bakya jin dad'in abinda nake miki?"

Yafadi hakan yana Lumshe Idonsa

Wata irin kunya ce takama Waheeda, tasaka hannunta tarufe fuskarta, Sai yanzu ne tagane inda yadosa, ashe Dama Abaya haukanta take tana hura hanci ita tazama babba, ashe wannan abun ne girman, cikin sauri ta6ud'e motar tatafi da gudu, ajiyar zuciya yasaki yanabin Bayan ta da kallo harta shige falo, sannan yayiwa driver magana yazo yajashi suka tafi

Satinsa d'aya da tafiya Waheeda taci gaba da zuwa makaranta dayake exam ma suke, yanzu tayi Hankali ta nutsu ta daina hauka, ko agida haka zaka ganta a zaune waje d'aya, wani lokacin har kunyar Ummah take ji saboda Gani take duk abinda yafaru tsakanin ta da Babban Yaya Ummah tasani, haka kawai saita dinga tsarguwa idan tana cikin su, da daddare kuwa kasa bacci take, tana ganinsu Ihsan suna kwasar baccin su Amma ita saide taita juye-juye, Kuma ba komai ne yake damunta ba Sai tunanin mijinta, Ida tunanin yayi yawa harji take kan nononta yana mata qaiqayi, saide tasa hannu ta Sosa Amma hakan bazai Hana anjima tasake jin wani qaiqayin ba, idan ta kirashi da wayar su Ihsan baya d'auka, saboda yasan itace, Sai yanzu ne take DANA SANI (first novel) akan hanashi haqqinsa da tayi ta dinga wahalar dashi, Sai yanzu yake bata tausayi, yau Satinsa biyar da tafiya, a ranar ne Kuma su Waheeda suka gama makaranta, sannan a ranar ne zasu buga wasansu, Hajiya Anty da Uncle Usman duk sunzo gidan antaru za'a kalli ball d'in, Anty Maryam itama tazo harda junior me sunan Babban Yaya, gaba d'ayansu sun nutsu kowa hankalin sa yana kan TV, Waheeda tana Gefe tana kallo itama,carbi ne a hannun ta Sai addu'ah take cikin ranta Allah yabawa mijinta nasara, dayake addu'ar mata akan mijinta batada hijabi a wajan ubangiji,cikin ikon Allah Ana fara wasa kuwa Babban Yaya shine mutum nafarko daya fara Ci, yana ganin yaci ya tsugunna yayi sujud shukr.

su Sa'eed suka tafa shida Sa'ad, falo kowa yafara murna

Wasa yayi wasa kowanne team sunaso sunga sunci, har tsawon wani lokaci sannan wani d'an team d'in su Babban Yaya yaciyo musu, Babban Yaya yana kar6ar Ball d'in ya dinga Sakata araga, saida yaci Sau uku ajere, Bayan guda d'ayan daya faraci, gudu yake sosai yana d'aga hannu, Yan team dinsu suna binsa Abaya, cikin murna suka rungume shi, Ummah bakinta yaqi rufuwa, Sai murmushi take idonta yana kan TV, su Daddy da uncle ma sunyi shiru kowa yana Gani, Hajiya Anty de addu'ah take cikin ranta Allah yakare mata d'annata, Allah yasake d'aukakashi yad'ora shi akan maqiyansa.
anci gaba da wasa kenan Babban Yaya yasake nasarar kar6ar qwallo daga wajan d'ayan team din, ya d'aga qafa zai bugata kenan Shima wani yakawo tasa qafar jikake qassss, yabige qafar Babban Yaya, lokaci daya jama'ar dasuke studio din suka fara fadin ohhhhh!
Lokaci daya hankalin masoyansa yatashi, suka miqe tsaye, cikin azaba Babban Yaya yariqe qafarsa yana runtse ido

Waheeda taji kunnanta yayi mata wani dimmm haka kamar bataji, kamar Kuma a mafarki, miqewa tayi tsaye tanufi gaban TV, gabanta yana fad'uwa, tuni hawaye suka wanke wa Ummah fuska ganin ankawo wani irin gado marar qafa, andora Babban Yaya akai, anfita dashi daga filin wasa

Kallan Daddy tayi cikin kuka tace"Alhaji tafiya zanyi, sun kashemin Dana "

Cikin tashin Hankali daddy yace" Ina zakije Hajiya? Kiyi hakuri mana "

Uncle Usman yafara neman wayarsa, Hajiya Anty ta Kalle shi cikin rawar murya tace" bazaka sameshi ba, yacemin kashe wayarsa zaiyi idan zasu fara wasan "

tana fad'in hakan hawaye yazubo daga idonta, su yanbiyu ne suka janyo Waheeda, Sai girgiza kanta take tana hawaye Amma takasa magana, Sa'ad yatashi yakashe Kallan, Anty Maryam tariqe Waheeda tace" kiyi hakuri Waheeda, insha Allah zaiji sauqi "

Cikin kuka tace"niku rabu dani, ku d'in shiru zakuyi idan mijinku ne?, Dan Allah Dan Annabi Daddy kabarni natafi, dama fishi yake Dani, qilama nice sila....."

tafadi hakan tana fashewa da wani irin kuka

Hajiya Anty ta rungume ta tana bubbuga Bayan ta, babu Wanda baiyi kuka ba acikinsu, saisu Daddy kawai, suna mutuqar qaunar d'an'uwan nasu, haka suka zauna shiru suna faman addu'ah, shide ba'a Nigeria yake ba bare sutafi koba visa, a wata qasa yake, Kuma yanzu dare ne dole zasu jira suga wanne mataki qungiyar tasu zasu dauka akan ciwon da yaji

Babu Wanda yayi yunqurin kwanciya acikinsu, kowa wayace ahannunsa yana try number Babban Yaya ko zata shiga, Waheeda ce kawai babu waya Sai faman kuka take har numfashin ta yana sama kamar wadda take shirin suma, Sai wajan karfe biyu sannan cikin sa'a Daddy ya sameshi, cikin sauri ya miqe tsaye yace "Alhamdulillah tashiga, yabud'e wayar"

Kowa Matsowa yayi kusa da Daddy duk suka taru suka yanyameshi, Daddy daya ga haka saiya saka wayar a hands-free, harta katse bai d'auka ba, saida yasake kira Akaro na biyu sannan yada'auka, kuka yafara ji yana tashi sama sama Kuma ba kukan mutum d'aya ba, cikin ransa yace sunga abinda yafaru kenan

Daddy yace "Son, kana lafiya? Yaya jikin Naka?"

Kafin Babban Yaya yayi magana Ummah ta qwace wayar, cikin kuka tace "kafadamin halinda kake ciki, Hankali na yakasa kwanciya, sonake nataho, bazan iya zama ba"

Ahankali yace "Ummah...., ki kwantar da hankalinki, anduba min qafar, harma sun Bani injury, zan dawo gida insha Allah"

Cikin kuka Ummah tace "karka dawo in kasan jikin babu sauqi, mu saimu biyo ka"❤️😂

Memakon yabata amsa saiyace "Ummah Ina Anty? Ina Waheeda?"

Wayar tamiqawa Hajiya Anty, Anty ta share Hawayen idonta, sannan takar6i wayar tace "sannu Naufal, yajikin naka?"

Ahankali yace"jiki da sauqi Anty, kikulamin da Waheeda nasan Hankalinta yatashi "

Anty batayi magana ba, saita Bawa Waheeda wayar, saboda tasan yana jin nauyin ta bazai iya cewa tabawa waheedan waya ba, Waheeda kuwa tana kar6ar wayar Takoma Gefe, kuka take sosai takasa magana, cikin sanyin murya yace"kiyi shiru..., ba sosai bane ciwon"

Cikin kuka tace "kayi hakuri nadena, daga yanzu nadena hanaka komai, naji tsoro sosai, jinake kamutu"

Wani irin dad'i yaji ya ratsashi, yanzu Kam yagama tabbatar wa Waheeda tana sonsa, saboda haka wannan ciwon Koya warke bazai nuna mata hakan ba, yasamu mafaka ta yanda zai dinga zuba mata shagwa6a son ransa

Ahankali yace "I luv you so much.......muahhhh,, muahhhh" 💋💋

Yasakar mata kiss har biyu ta cikin wayar, sannan yaci gaba da fad'in "kimin addu'ah kinji, insha Allah zanji sauqi, jeki kaiwa su Daddy wayar

Tace"to" sannan tatashi takai musu wayar, Sai a lokacin Hankalinta ya kwanta, Sai ajiyar zuciya take, jikin Hajiya Anty Takoma ta lafe kamar wata mage, bata Jima da kwanciya a jikin nataba bacci yasoma d'aukarta

Yana gama wayar dakowa acikinsu harda junior, sukai sallama Bayan yagama kwantar musu da Hankali, Kiran mashkur ne yashigo wayar tasa, d'auka yayi tareda sallama, mashkur yace "friend mutanan nanfa sun hanamu shigowa Dakin, sunce har yanzu kana buqatar hutu, Sai lalla6a ka suke kamar qwai"😂

Murmushi yayi yace "rabu dasu mashkur, zamu hadu ai idan nafuto insha Allah, ciwon fa Bana kirki bane, kawai tsagewar qashi ne, da niyya na langwa6e musu, nagaji da ball d'in Dama hanyar guduwa wajan amarya ta nake nema, to Kuma Sai haka tafaru....." 🙊

Mashkur ya kwashe da dariya yace"wato me jiran kukane aka jefeshi da kashin awaki, banga laifin ka ba Abokina,Naga ma sun sanar katafi injury, Kasha Amarci lafiya...."

Babban Yaya yayi murmushi yace "thanks Friend"

Pls kuyi hakuri Dan Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
1/28/22, 20:52 - Ummi Tandama😇: RD

Basu sukabar falon ba Sai wajan karfe uku da rabi, a ranar daga Waheeda, har Ummah da Hajiya Anty, basu runtsa ba, su Waheeda suna zuwa daki alwala tayi tazo tafara sallah tana yiwa mijinta addu'ah Allah yakare mata shi, su kansu yanbiyu da Anty Maryam sunyi mamakin Waheeda, sun kuma tabbatar lalle aure yana saka mutum nutsuwa da Hankali, gashi de kamar ba Waheeda ba 😂

Da safe wani irin zazzafan zazza6i yarufe ta, babu 6ata lokaci Hajiya Anty tayi mata allura, sannan bacci me nauyi ya d'auketa

Koda suka sake Kiran wayar Naufal yana tambayar su ita, suka fad'a masa tana kwance batajin dad'i

Wasa wasa saida Waheeda ta kwashe kusan sati d'aya a kwance batada lafiya, kullum tana d'aki a kwance cikin blanket, Hajiya Anty duk ta damu,yau shiryawa sukai suka tafi Asbiti, suna zuwa tayi mata awon fitsari tayi tunanin ko ciki ne 🙊
Amma da result yafuto saitaga babu komai, akayi mata text aka Gano typhoid ne, anan suka had'o magunguna suka dawo gida

Tana fara amfani da magungunan kuwa cikin ikon Allah ta warware 👌🏻

Amma kana ganin fuskarta zakaga tayi wani irin haske, ita kanta Ummah tayi tunanin cikin ne, saida taga result d'in Nata sannan ta yarda batada ciki

Kwanan Babban Yaya Tara, yaji dad'in jikinsa, dama Allah Allah yake ya dawo gida, aikuwa Ana sallamar sa yayiwa Ummah waya yafad'a mata gashinan zuwa

Waheeda tanajin labari tafara had'a Kaya 😂
Ihsan dake maqale da waya a kunnan ta tana magana da mashkur ta kalleta tace "Ina Zaki ne?"

Kai tsaye tace "gidana"

Intisar ta kwashe da dariya tace "su Waheeda masu gida,yau Kuma keda kanki kike cewa gidanki Zaki tafi?"

Cikin gundura da zancen nasu tace "to saina zauna anan haka kawai Bayan ga mijina can yana hanya? Sai in zauna yazo yaganni Ahaka ya rainani?"

😳Zaro ido inti da Ihsan sukai, sunji abun mamaki Wai Babban Yaya ne zai rainata, kafin suyi magana Waheeda tasaka hijabin ta tad'auki jaka tafuto tareda ja musu qofar
Chapter 40 · 0% Book details