← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 48

Sashe 20

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waheeda tayi shiru tana tunani, tana so tace musu yafada mata yarinyar dayake so to Amma Kuma data tuna yace mata sirri, Saitayi shiru, tayi ajiyar zuciya tace "nikam Ina sonta, tunda Babban Yaya zata aura, mutumin dayake taimako na aduk halin Dana kasance tayaya zanqi matarsa?"

Ihsan tace "to Allah yabada sa'a Waheeda, ke kikaga Zaki iya"

Daga Nan sukai shiru kowa da abinda yake saqawa Aransa

Ita Waheeda tana tunanin Babban Yaya, duk yanda zaiyi mata fad'a tana shiga damuwa muddin ta ganshi acikin damuwa, saboda Shima baya barinta acikin matsala, ta damu da damuwar sa sosai, batasan meyasa ba, wani lokacin zai mata hukunci akan laifin da tayi, gashi de shine ya6ata mata rai ta hanyar yimata hukunci, Amma Hankalinta baya kwanciya Sai ta bashi hakura taga ya haqura tukunna, gashi yanzu yana wani Hali saboda auran Ummi, batasan ta wanne Hali zata taimaka masa ba,zuciyarta tabata shawara akan tatayashi da addu'ah, haka ta dauki shawarar zuciyarta

Haka Babban Yaya ya wuni ad'aki yaqi futowa, Ummah Kota Kansa batabi ba, saboda tasan fishin nasa akan aure ne, Kuma aure Kam babu fashi

Washe gari yafuto daga d'akin nasa, yana Sanye da kayan ball, suma 'yanbiyu maza shine ajikinsu, zama sukai afalo kowa yana kokarin saka safa, yanmatan ne suka futo daga d'akinsu suma de kayan Ball d'inne ajikinsu, Amma nasu wandon dogo ne, rigar ma me dogon hannu ce, sa6anin na mazan dayake qanana, fita sukai zuwa filinsu na qwallo dayake gidan, shikuma Babban Yaya yana falon yana saka takalmin sa, gaba d'aya iyayen nasu suna compound suna shan shayi, da hajiya Anty da Ummah dakuma Daddy da Uncle Usman, akan idonsu yaran suka futo zasu fara buga Ball din, Amma babu Babban Yaya, a lokacin harya gama saka kambos dinsa, yana zaune ne yana amsa wayar Abokinsa dayake tambayar sa yaushe zai dawo, yana gama waya da abokin nasa wata wayar tashigo, yayi mamaki da'aka kirashi ta wannan number, saboda ba kowane yasan wannan number tashi ba, dauka yayi tareda sallama daga dayan bangaren akace "Yayanmu Ina wuni? Sunana Didat, qanwarka ce tabani number ka,Ina neman alfarma ne awajanka, maganar Gaskiya Ina sonta, idan kabani Dama inaso na nemi aurenta"

Babban Yaya ya Sosa girarsa guda d'aya yace "Sister na kuma?"

Daga d'ayan bangaren Didat yace "eh Yayanmu, na gansu ne abakin get d'in school d'insu, akwai mutum biyu masu kama d'aya, toba suba, d'ayar nake nufi"

Babban Yaya yana jin haka ya Lumshe Idonsa, cikin ransa yace "Waheeda"

Dafarko har yayi niyyar dakatar da Yaron, but Saiyayi tunani tayaya rayuwa zataci gaba da tafiya Ahaka? Yaushe ne zai daina hanata huld'a da samari? Duk Daren dad'ewa dole zatayi aure, wazai fara fuskanta da maganar datake damunsa?qalubalen dazai fuskanta akan haka ba d'an qarami bane, Kuma itama da alama sonsa take, tunda gashinan ta yarda harta amince a tambayeshi? Cikin Yan seconds yayi wannan tunanin, wani irin huci yayi yafitar da iska me zafi daga bakinsa sannan yace "Babu damuwa zaka iya zuwa"

daga Nan yakashe wayar tashi yafita zuwa compound da d'an gudunsa irin na 'Yan qwallo, acan Gefe ya hangi su Ummah sun baje suna shan Shayi, yana zuwa kuwa suka fara buga ball din mazan da matan, kusan mintuna talatin suka d'auka sunayi Amma Babban Yaya baici ko sau d'aya ba, mamaki ya kama iyayen nasu dasuke Kallan abinda yake faruwa, shida a qasar waje ma suke alfahri dashi akan iya ball, tayaya wad'annan yaran zasu dinga cinsa? Ada idan sunayin ball d'in kowa saduda yake, saboda sunsan comfirm 'Yan team din Babban Yaya sune da nasara, Amma yau Sa'ad da Babban Yaya, da intisar Sai sunci su Waheeda da Ihsan da Sa'eed suke yi.

Sunkuyawa yayi yariqe gwiwarsu, damuwa tataru tamasa yawa, idan ya tuna da maganar Ummi, yatuna da wayar da gayen Nan yamasa akan Waheeda, saiyaji gabansa yafad'i, daga qarshe ma kawai juyawa yayi zuwa falon su, intisar datake jin haushi anata cinsu, tayi sauri ta hura Whistle tace "wasa yatashi" 😂
Akan idanun iyayen Babban Yaya ya wuce falo yabar yan'uwan nasa, Waheeda tariqe hips d'inta cikin damuwa tana Kallan sa, daga Nan tabi bayansa, saide tana zuwa 'kofar 'Dakin nasa tayi nocking din duniya yaqi bude mata, dole Sai haqura tayi, ta wuce dakinsu.

Washe gari da yamma Ummah tana zaune ad'akinta tana tunani akan rayuwar Naufal, damuwar dayake ciki haqiqa itama tana ciki, yaqi yafuto fili yafad'a mata me yake tsoro dangane da aure a matsayin ta na mahaifiyar sa, duk sa'anninsa sun dad'e da aure, Sai yaushe ne shi zaiyi? Tun yanda ta ganshi jiya cikin damuwa har yanzu Hankalinta yaqi kwanciya, duk yanda yake dason Ball yamaqi yakoma bare tace ball din zata d'ebe masa kewa, Waheeda ce tashigo Dakin tana Sanye da dogon hijabi tace "Ummah zanje bakin get nayi baqo"

Ummah ta kalleta tace "Baqo kuma? Daga Ina kenan?"

Murmushi tayi tace "shekaran jiya nahad'u dashi abakin get din school dinmu, sunyi waya da Babban Yaya ma, shine yace yazo"

Ummah tace "kin tabbatar abinda kika fad'amin gaskiya ne Waheeda yayanku yasan da maganar sa?"

"Allah Ummah yasani"

"to shikkenan kije, Amma karki dade" cewar Ummah

Waheeda tafuto daga d'akin, ta qarasa wajan Didat, yana Sanye cikin shadda Light blue, hular daya saka ta dace da kalar kayan nasa, qarasa wa tayi tareda sallama, ta ajiye masa ruwan roba guda biyu da Lemo guda daya, baba maigadi yataso da sauri yasake gaida shi, sannan suka qarasa wajan wasu kujeru masu kyau Wanda aka qawata wajan da yar qaramar rumfa domin shan iska, Didat ya kalli Waheeda Bayan ya zauna yace "Ranki yadade gimbiya"

Waheeda tace "mudade tare"

Murmushi yayi yace "bakice nayi kyau ba, Bayan duka wankan naki ne, kinsan kafin nafuto daga gida saida nafadama mamana wajanki zanzo, tace nayi kyau sannan tana miqa saqon gaisuwar ta zuwa gareki"

Tace "nagode sosai, Ina amsawa, idan kakoma kace ina gaisheta"

"zataji insha Allah,ni sunana Didat"

Tace "nikuma Waheeda"

Kallan ta yayi yace "sunanki yanada dadi Waheeda, Ina fatan ace kin zamo wani bangaren na cikin rayuwa ta idan kin amince"

Tace "kamarya?"

"Ina nufin kibani Dama Nima adama Dani acikin Jerin masoyanki, Amma maganar gaskiya itace inada kishi sosai akan abinda nakeso, shiyasa ma nakawo miki wannan kyautar"

Yafadi haka yana bata wata leda, saida ta karba Sannan yace "hijabi ne da niqab, dakuma safa, gaskiya Ina kishinki Waheeda, aurenki nakeson yi bawai soyaiya ce ta kawo ni wajanki ba, banaso muyi shekara daya batare da munyi aure ba"

Murmushi Waheeda tayi tace "gaskiya ne, nayarda kanada kishi, tunda gashi kyauta ta farko daka fara min itace da hijab da safa da niqab, Amma Kuma duk kishinka baka Kai Babban Yaya ba" 🙆🏻‍♀️😳�

Cikin mamaki ya gyara zama sannan ya kalleta yace "waye Kuma Babban Yaya?"

Murmushi Tayi tace "nasan cewa kasan Big Brother ko?"

Yace "sosai ma kuwa, waye zaice baisan Shiba? Aini shine 'Dan qwallon dayake mugun birgeni"

Tace "to shi nake nufi, ai shine Babban Yayanmu"

Didat yace "ok, Allah sarki, haba shiyasa Naga gidanku unguwa guda gashinan aljannar duniya" yafad'i hakan cikin sigar tsokana

Waheeda tace "Shima yanada kishi, yafi son muyi karatu karmu kula samari"

Yace "ya kyauta min, inda yabarku Aida Nima bazan sameki ba, nasan da tuni wani alhajin ya dauke ki"

Murmushi tayi tace "nagode, zan koma gida, Ummah tace karna dad'e"

Shima tashi yayi tsaye, ya ajiye mata rafar kudi Yan hamsin hamsin guda daya, aqalla zasu Kai dubu hamsin, daqyar da Fama Waheeda ta d'auki kudin, sannan suka rabu akan zai sake dawowa gobe ko jibi, tanada son kudi Amma Bana hannun mutane ba, saide na Babban Yaya, tasan yayanta ne bazai taba goranta mata a kan hakaba, abinda ta lura dashi shine, shi mutum ne me kishi kamar yanda yafad'a, sannan daga Gani bashida matsala ko kad'an

Da daddare gaba d'ayansu suna zaune banda Daddy, Ummah ta kalli Babban Yaya dake danna waya yana qara Bawa Corch dinsu hakuri akan dad'ewar da yayi,Kallan Ummah yayi yace "Ummah nanda kwana hudu yaran Nan zasu tafi Umarah insha Allah, gaba d'ayansu"

Cikin farinciki Ummah tace "Alhamdulillah, Allah yayima Albarka, to Allah yakaimu lokacin, Kai banda Kai ne?"

Girgiza mata Kai yayi sannan yace "su kad'ai"

Ummah tace "To madallah, Allah yaqara hore Maka,"

Murna suka hauyi gaba d'ayansu, Nan take suka fara zuba masa ruwan godia, Waheeda kuwa jitake kamar taje ta rungume shi Dan murna, Amma babu Dama yanda taga ya d'aure fuskar Nan tana zuwa kusa dashi tsaf zai maketa 😂

Ummah ta sake Kallan sa cikin farinciki sannan tace"Yauwa yayansu ga wannan kud'in, saurayin Waheeda ne yabata dazu"

Kallan kudin yayi Asheqe sannan yace "ok"

Ummah tace "bangane Okay ba, bazaka kar6a kasa mata Albarka ba?"

Yatsina fuska yayi yace "Ummah dubu hamsin d'in kamar Wanda yayi kyautar bajinta?" ☹️

Mamaki yakama Ummah, sukuwa su Sa'eed dariya suka saka, Sa'ad yace "haba Babban Yaya, dubu hamsin fa, kodan Kai mekud'i ne shiyasa, wallahi Ummi tahuta"😃

Wani irin banzan kallo yamasa, lokaci d'aya yashiga taitayinsa

Kafin su qara cewa komai wata yarinya 'yar kimanin shakara 11 tashigo da sallama hannunta d'aukeda wani flask na abinci, ta tsugunna ta gaida su Ummah sannan tace "Wai gashi inji Anty Ummi abawa Yaya Naufal" 😅

Haushi yakama Babban Yaya, ya kalli yarinyar yayi tsaki a ransa, ko'ina ya zama yayanta harda wani Yaya Naufal,?

Ummah ta saki ranta tace "Allah sarki, to kice ya gode, zai kawo mata kular da Kansa kinji, Allah yamiki Albarka,"

tad'auko fos dinta dake Gefe tabawa yarinyar dubu biyar, yarinyar cikin murna ta karba tafice daga falon

Waheeda ce tataso tabud'e flask din taga abinda yake ciki, sannan tayi murmushi ta kalli Babban Yaya tace
"Babban Yaya farfe...."

kafin ta qarasa cewa farfesu ne, yatashi cikin fishi, yabar falon gaba d'aya, Ihsan da intisar suka zabgawa Waheeda harara suma sukai d'aki, Waheeda ta kalli Ummah cikin shagwa6a kamar zatayi kuka, Ummah ta janyo ta jikinta tace"rabu dasu, idan sun gama fishin zasu sakko"

Washe gari da safe, suna break fast, wayar Daddy tayi qara, yayi mamakin me Kiran nasa, domin kuwa ba kasafai suke waya da minister of Education ba, d'auka yayi Bayan sun gaisa, Daga d'ayan bangaren minister Abdullahi Wakili yace "Alhaji Umar Arabo"
Chapter 20 · 0% Book details