← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 48

Sashe 32

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabansa ne ya tsanan ta fad'uwa, ya d'ago Kansa ya kalli iyayen nasa, daga Daddy har Uncle Usman kansu yana qasa sun kasa d'agowa kamar Wanda suke jin kunyar had'a ido da yaran nasu

Ya kalli Ummah yaga tana goge hawaye

Ya kalli 'yanbiyu yaga Sai gunjin kuka suke duka su ukun har Waheeda

Ya kalli su Sa'eed yaga kansu aqasa suma

Ya kalli Hajiya Anty yaga ta zubawa waje d'aya ido hawaye yana silalo wa daga idonta, idan akwai Wanda yaqi jinin yaga kukan ta Aduk duniya to Hajiya Anty ce, zai iya jure kukan kowa Amma banda Nata, har zuwa lokacin Hajiya ummi tana falon, ita bata tafi ba, Kuma takasa Bawa kowa haquri

Zuciyar sa ce take zigashi akan yafad'i abinda yake ransa, tayaya za'azo har gida, harcikin falon su aci mutuncin su kawai saboda maganar Aure? Tayaya zaiguji Waheeda? Tayaya zai raba zuciyar sa da soyaiyar ta Bayan da soyaiyar Tata aka halicce shi?
Lokaci d'aya yad'auki shawarar zuciyar sa, yanaso yafad'i abinda yake ransa Kuma Yana tsoron abinda zai biyo baya, gabansa yaqara tsananta fad'uwa, cikin sauri kamar an fuzgo maganar daga bakinsa ya kalli inda Daddy da Uncle Usman suke zaune yace "Daddy nizan Aure ta"

'Diffff...... Sai aka nemi masu kuka a falon aka Rasa,falo yayi shiruuu, kowa ya d'ago Kansa yana Kallan Babban Yaya, falon yayi tsit kamar babu wata halitta acikinsa, kowa Kallan sa yake cikeda mamaki, gaba d'ayansu yaran gidan babu Wanda mamaki bai kamashi ba Sai iyayen ne kawai dasuke Kallan sa cikeda d'inbum almara

Ummi ta miqe tsaye cikin tashin Hankali tace "ka auri wa? Wallahi saide ka za6a koni ko ita, Amma Bazan ta6a yarda ka aure ta ka shafamin qanjamau ba, saide mu rabu...."

Ummah ta kalli Babban Yaya tace "Naufal meyasa....?meyasa zaka fad'i wannan maganar?"

ta qarasa maganar tana dafe kanta dayake barazanar rabewa gida biyu 🤦🏻‍♀�

Cikin tashin Hankali Waheeda ta zaro idonta😳 Wanda yayi jajir kamar gauta saboda kuka, kamar ba itace take ihun kuka yanzu ba
Kallan Ummah tasake yi ko zata qarya ta maganar da Babban Yaya yafad'a, Amma saitaji Ummah tayi shiru, ta kalli su Daddy har yanzu kansu yana qasa sun kasa kallan mutanan falon, cikin tashin Hankali tace "Zaman Zina? Ni wallahi bazan yarda ba, banason sa, bazan iya Zaman aure dashi ba....."

tatashi tayi d'akinsu da gudu cikin tsananin kuka

Wani irin kuka ne yataso masa, yau shi Waheeda take cewa bata sonsa, wani irin abu yatokare masa maqoshi, ko yawu yakasa had'iyewa.

Ummi ta Kalle shi tace"Naufal jiranka nake, nabaka za6i tun d'azu kayi shiru, kana tunanin zan yarda kahad'ani kishi da wannan yarinyar ne? Wallahi bazai iyu ba saide asan nayi, zanje in fad'a agida yanzu yanzu "

Baqin cikin kalmar da Waheeda tafada masa ne yake addabar zuciyar sa, jiyake kamar yafashe da Kuka kozaiji sauqi Amma kukan yaqi zuwa, ga Kuma wannan yarinyar datake qara masa wata damuwar.
Cikin 6acin rai Shima yatashi tsaye, cikeda tsawa yace" toki fad'a mana, so what....? Idan kin fad'a musu kiqara musu da cewa Bana sonki, Bana qaunarki, bazan iya zama dake ba, saboda bakya respecting iyayena "

Yajuya ya nuna mata Hajiya Anty sannan yaci gaba da fad'in"matar dakika raina kike mata Kallan sa'arki itad'in mahaifiyata ce..."

Lokaci d'aya ummi ta qame a wajan, gabanta yafad'i, cikin mamaki ta bud'e bakinta, takasa rufe shi
Babban Yaya yahad'e hannun sa waje d'aya 🙏🏻ya kalleta yace "Dan Allah Ummi kifita daga cikin rayuwa ta, na roqeki"

Cikin kuka ummi Tajuya tafice daga gidan, Shima Babban Yaya batare daya kalli iyayen nasu ba yafice cikin sauri, saboda zuciyar sa tagama karyewa, qiris yake jira yafashe da kuka, yana zuwa compound yashiga motar sa yamata key yabar gidan a d'ari da Sittin, Kai tsaye gidansa ya nufa, yanda yake danna Hon yasa maigadinsa yabud'e masa da sauri, shigowa had'ad'd'an gidan nasa yayi tareda parking din motar sa, yad'ora Kansa akan sitiyarin motar yayi shiru, har yanzu maganganun Waheeda yawo suke masa a ransa, yana jin yanda wayarsa take qara Amma yaqi dubawa, saida kira na uku yashigo sannan ya d'auka

Daga d'ayan bangaren Mashkur yace " Bro... Ina kabar wayar ne?"

Sai a lokacin kukan dayake dannewa agida yataso masa, fashewa yayi da Kuka harda shashsheka, daqyar maganar sa take fita, cikin kuka yace "Mashkur bata sona..."

❤️
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama😇: SQ

Cikin sauri mashkur yace "wacece? Wacce yarinya ce wannan tasaka friend d'ina kuka haka?"

Kai tsaye Babban Yaya yace "Waheeda!"
Mashkur ya gyara zamansa yace "Waheeda Kuma? Ba sister d'inka ce ba?"

"Sister nace"

Cikin mamaki mashkur yace "but... tayaya...."

Babban Yaya ya katse shi yace "she's my Cousin Sister"

"Amma friend abun ya d'auremin Kai dayawa, Wai kanaso kacemin Dama itace wadda kake cewa kanaso bazaka iya rayuwa batare da'itaba? Itace wadda akanta mukaje Saudia muketa ruwan Addu'ah?" 🤔

Ahankali Babban Yaya yace "itace...., inason ta mashkur, but nafad'awa su Daddy d'azu, shine tace musu Wai ita bata sona..."

"dakata Bro,tayaya kake tunanin zatace tana sonka dan Allah? Koni Nan nayi tunanin Kai yayanta ne uwa d'aya uba d'aya, haka kawai Kai tsaye yarinya taji kace zaka aure ta, Dan Allah tayaya kake tunanin zata amince Karon farko? Kaine kake mata Kallan masoyiya, ita Kallan yaya take Maka, Amma kayi hakuri, kabar komai yalafa, insha Allah zata fahimce ka, kayi hakuri "

Babban Yaya yakashe wayar, ba tareda yace komai ba, sannan yafuto daga motar yashiga ciki

** *** **

Sa'eed ya kalli Ummah yace "Ummah ku fitar damu daga duhu mana"

Yasake Kallan iyayen nasu maza yace "Daddy, Uncle Dan Allah kuyi mana bayani, me Babban Yaya yake nufi? Tayaya zai iya auren Waheeda Bayan shi Yayanmu ne?"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace "Naufal zai iya auren Waheeda"

Yanbiyu da Sa'eed da Sa'ad suka maida Kallan su wajan Daddy

Daddy yaci gaba da fad'in, "koda ace Naufal bai bud'i baki yace zai auri Waheeda ba Toni dakaina zan d'auketa nabashi, saboda banta6a tunanin Yaron Nan Huzaifa zaimin haka ba, ashe bashida tarbiya tunda har zai iya Kallan idonmu, a matsayin mu na iyayensa, ya fad'a mana irin wannan maganganun,abinda yake faruwa Wanda ku Baku saniba shine....

Tun muna Yara nida Usman ne kawai mukai karatun boko, Yaya Habu baiyi ba, shiyasa Lokacin da muka bar nijar muka dawo Nigeria da zama, a lokacin muka zauna da Yaya Habu akan Garin dazamu Yada Zango, a lokacin ya nuna mana shi yana jin dadin Zaman Garin jigawa, saboda haka mubashi wata dukiyar tamu da mukai gado a wajan iyayen mu, ya zauna yaci gaba da juya mana ita acan qauye, mukuma muje birni muyi abinda muka ga yadace

A lokacin babu Wanda ya haihu acikin mu duka mu ukun, Bayan mun dawo Nan da zama a lokacin muka qara karatu, mukasa iyayenku mata a a makaranta, Antynku tana fara karatu Sai Allah yabata ciki, Tasha wahala a lokacin, Yaya Habu yazo ganinta, anan yake sanar damu cewa Shima me d'akinsa tasamu juna biyu, munyi farinciki sosai, Bayan wasu watanni Matar Yaya Habu ta sauka, Aka sakawa yaro suna Yahya, a lokacin muka shirya muka tafi jigawa Wajan suna, tun muna hanya Ummanku take cikin damuwa, saboda tasan zata had'u da danginmu na Niger a gidan Yaya Habu, Kuma sha'anin surutun dangi, tabbas Sai sun fad'a mata magana akan haihuwa, na tambayeta dalilin damuwar ta, ta fad'a min komai bata 6oyemin ba, ashe aloakcin Uncle d'inku dakuma Hajiya Anty, suna jinmu, munje anyi taron suna lafiya angama lafiya, abinda Ummanku take gudu saida yaso yafaru, domin kuwa duk Wanda yaga Anty Da tsohon ciki ita Kuma bata dashi saide su dinga yimata wani Gani-Gani, saida na tsawatar musu

Washe Garin haihuwar Yahya a ranar Antynku ta haifi Naufal, Halaccin da bamu ta6a tunanin zasu mana ba itada Usman shi suka mana, saida suka kira Yaya Habu Dani da umman ku, sannan suka d'auki Naufal suka bamu shi halak Malak, Dafarko naqi yarda nakar6a, saboda suma shi kad'ai suka mallaka, Amma sai Yaya Habu yace mana mukar6a tunda sune suka bamu, tunda ita Antyn tafara haihuwa insha Allah zata sake Haifar wani, Amma yanzu mubarshi ta shayar dashi, saimu kar6eshi, tunda muka dawo gida Ummanku take kula da Naufal, tsakanin sa Da Antynku shine shayarwa dakuma wasa irin na d'a da uwa, har Allah yasa aka yaye Naufal, tazo da kanta ta kawo mana shi,a lokacin yaqi yarda ya zauna damu duk da yasaba da ummanku, dare yanayi zai fara kuka yana Kiran Anty, haka muka haqura saida ya tasa, sannan ummanku ta kar6eshi, a lokacin da hankalin sa Sarai ya dawo gidannan, yasan komai, yasan bamu ne muka haife shi ba, Amma abun mamakin koda wasa baita6a nunawa wani cewa bamune iyayen saba.

Ahankali ahankali soyaiya take sake shiga tsakanin sa da ummanku, har suka saba babu inda zasuje ace shi ba d'anta bane, cikin dangi kowa yasan Yaro na Ummah ne Amma Anty ce ta haifeshi

Bayan wani lokaci tun muna jiran Antynku tasake haihuwa har muka gaji muka barwa Allah, muka d'auki son duniya muka d'ora wa Naufal duka mu hud'un, har tsawon shekara goma

A lokacin kamar wasa ummanku tafara zazza6i muna zuwa Asbiti akace tanada juna biyu, a lokacin Nan gidan Antynku tatare take kula da komai, har Allah yasa ummanku ta sauka ta haifi Yan biyu maza, nida Usman Muka sanya musu Suna Sa'ad dakuma Sa'eed

Daga baya tasake samun wani cikin muka sanya mata sunan mahaifiyar mu, wato Maryam, Bayan shekara biyar tasake haihuwar wasu yanbiyun muka sanya musu suna Intisar dakuma Ihsan, a lokacin munyi tunanin Usman da Antynku zasu kar6e Naufal daga wajanmu, Dan har Ummanku tafara zazza6i tana tsoron arabata dashi saboda yanda yashiga ranta, tasaba dashi fiye da 'ya'yanta na cikinta, Amma koda wasa basu ce mu basu Shiba, Bayan shekara biyu da haihuwar su Ihsan muka sake Haifar Waheeda.
Chapter 32 · 0% Book details