Sashe 2
Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yanda nafada Naufal shine babba acikin yaran Alhaji Umar (Dady) shekararsa Talatin da shida, beyi aure ba, iyayen sunaso yayi aure kasancewar sa babba a gidan, yana kula da qannansa yanda me karatu baya zato, shiyasa ko wani abu ne yafaru saide kawai iyayen su fada masa, shikuma zai warware komai, kwata kwata baya wasa da yan'uwan nasa, idan kaga ya ware yana fira wasa da dariya to da abokan sa ne, musanman yayan Baba Habu dasuke jigawa, koda yaushe fuskarsa a daure take, bala'in tsoransa sukeji musanman qannansa mata, kana laifi kadan zai daka Maka tsawa, shiyasa suna ganinsa kowacce take shiga taitayinta, babu ruwansa duk wacce tayi masa laifi zaneta yake, suna komai duk abinda suke so, saide yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, saide Hijab, Kuma suna kiyayewa mutum daya ce take bashi ciwon Kai acikin qannansa, itace auta WAHEEDA, itace tafara kiransa da BABBAN YAYA, daga Nan kowa yake fada masa, babu Wanda zakaji yace Yaya Naufal, saide BABBAN YAYA.👌ðŸ»
Cikakken Dan qwallon qafa ne Wanda akeji dashi afadin qasar tamu ta Nigeria dakuma kewayen ta, lokacin daya gama Degree dinsa na biyu, (Masters) iyayen sunso yayi aiki a qarqashinsu, domin su qara habbaka kasuwancin su, Amma BABBAN YAYA yace inaaa! Shifa harkar qwallo zai fara, saboda Dama can tun yana qarami abinda yake so kenan, daga Alhaji Habu na qauye har mahaifin sa Alhaji Umar Qin bashi goyon baya sukayi, daqyar Alhaji Usman yadage akan su harya shawo kansu suka yarda, da farko Yan kano pillars yabugawa Ball, daga baya wata qasar ta daukeshi, daga Nan Kuma yakoma qasar Spain, Bayan wasu shekaru yakoma qasar dayake a yanzu yana buga musu Ball inda yake daukar albashin sa Mai tsoka duk sati.
Lokacin dazai fara Ball babu sunan daya fad'o masa Arai sai Wanda fitnanniyar qanwar sa WAHEEDA tasaka masa, BIG BROTHER, shiyasa jikin Jessy dinsa, p-cap dinsa,sunan BIG BROTHER ne ajiki, Yan gari, Yan unguwa, fan's dinsa na ko'ina kowa Big Brother yake ce masa, inde yashiga cikin jama'ah kawai haquri yake, saboda yanada masoya masu dimbin yawa, kawai Yan gidansu ne suke kiransa da BABBAN YAYA, Amma jama'ah kowa da kowa Big Brother ake ce masa,yanmata kuwa kullum cikin kiransa suke, yana alfahri da hakan.
Iyayensa sunaso yayi aure saboda shekaru irin nasa, Amma yace shi har yanzu baiga wacce ta kwanta masa ba, tun yana qarya yana cewa zai kawo wacce yake so aqara masa lokaci, har iyayen suka dawo daga rakiyarsa suka fara hadashi da yaran abokai da Kuma yan'uwa, Amma har yanzu duk wadda aka hadashi da'ita yasan irin dabarar dazai mata Dan su rabu cikin hikima, kamar de yanda ya kasance a tsakanin sa da Habiba Yanzu 🤪
Duk cikin yanmatan da'ake hadashi dasu babu wadda yataba baiyana mata Kansa, inde yakira wayar su yana fada musu cewa sunansa Naufal, baya cewa Big Brother saboda yasan cewa muddin yafadi wannan sunan, to babu Wanda bai sanshi ba, wannan kenan
*** *** ***
Tafe suke hannunta dauke da wani yaro Wanda bai wuce shekara uku ba, Sanye take da hijab pink colour, me hula, ta gaban hijabin kadai zaka iya sanin cewa Allah yayi mata tarin suma da yawa, kasancewar wuyan yayi mata yawa kadan, yarinya ce bazata wuce 18 years ba, ranar datake dukansu itada Yaron yasa ta yatsina fuska, Amma duk da haka kyawun fuskarta yana Nan, duk da babu kwalliya kodaya a fuskar, Sai haki take da alama Yaron yamata nauyi, suna zuwa bakin get din gidansu ta sauke Yaron, kudi tafuto dashi daga cikin handbag taware 5k tabawa Yaron sannan taja hannun sa suka qarasa gida, babu kowa afalon nasu, Kai tsaye dakinsu tashige, mutum uku ne zaune a Dakin, 'Yan biyu daya tana yiwa daya tsifa, saikuma wata Babba tana duba littafin azkar, gaba dayansu kama suke da juna, kana ganinsu kasan jini daya ne, hijabin jikinta ta cire ta wullar dashi anan, lokaci daya tsantsar dirin jikinta ya baiyana, mace ce har mace, gata yar qarama Amma Allah yamata baiwar kyakykyawan jiki.
Yaron yatafi da gudu wajan mamansa yace "Momy munje Kuma anbamu kudi da yawa, Nima anty Waheeda tabani, kingani?" ya qarasa maganar yana nuna mata kudin hannun sa
Murmushi tayi tace "Lalle Waheeda kice kudi kuka samo keda junior"
Zama tayi a bakin gadon tareda cire ribom din kanta, hakan yabawa dogon gashinta damar zubowa gadon Bayan ta
Tace "eh Anty maryam, dubu goma aka bamu, shine naraba mana"
Kafin wadda aka kira da Anty Maryam tayi magana, daya daga cikin Yan biyu tace "Qarya kike Waheeda, Anty wallahi qarya take, kawai cutar Yaron tayi, kamar bakisan halin Waheeda ba, Allah qwace masa kudin zatayi"
Cikin rashin kunya ta kalli me maganar, duk tsananin kamar dasuke kasancewar su identical twins Sarai Waheeda take ganesu, tace "to Ihsan na qwace din, ai tare aka aikemu da junior din ko? Kiyi abinda zakiyi"
Anty Maryam ta kalleta tareda riqe ha6a, tace "lalle Waheeda wuyanki ya'isa yanka, yayun naki kike fadawa haka?"
Wadda ake yiwa tsifar ce tatashi ta nufi Waheeda tace "Na hanaki daukar min hijabi na Amma kinqi yarda ko, tsabar masifa da naci kinada hijabai bazaki saka ba kin goge su kin 6oye saide ki dinga daukar namu kina sakawa saboda Kin raina mana Hankali, nayi Miki last warning karki sake daukar min hijab, sannan Ihsan ba sa'arki bace karki sake mata rashin kunya "
Cikin tsiwa tace"wallahi yanzu nafara saka hijabi saide in bangani ba, baki Isa kimin in qyale kiba intisar"
Anty Maryam tace "Waheeda kanki daya kuwa? Dama rashin kunyar Taki haryakai haka?"
Ihsan tace "rabu da'ita Anty, ai taga kanmu daya ne,Mp muke itama shi take yi, brezia muke sakawa itama shi take sakawa,taga ta girma tafimu nonuwa, tayi tsawon qafa, Gani take shekarunma daya muke da'ita, yau kuwa zakici ubanki, zaki San kin mana rashin kunya"
Tashi tayi tsaye ta kallesu ta watsar tace "ai Dama ba yau kuka fara hademin Kai ba, Naga su Sa'ad ma qarewa, balle ku Yan biyun qarshan zamani, qarqari kumin taron dangi kumin duka, to bazaku birgeni ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata"
Anty Maryam tatashi tsaye tace "lalle Waheeda kullum girma kike kina sake zama marar kunya, zan fadawa ummah abin naki yayi yawa, yanzu har takai su Yaya Sa'ad ma sunansu kike fada" tana fadar haka tafice daga Dakin cikin fishi
Ihsan ta kalli Intisar, basu tsaya wata wataba suka rufe Waheeda da duka, intisar takama gashin ta tanaja, Ihsan kuwa Sai dukanta take, dama haka suke, hadin kaine dasu sosai, duk lokacin da Waheeda tamusu rashin kunya haduwa suke suyi mata shegen duka
Hajiya Anty ce tashigo gidan, tana Sanye da kayan likitoci komai fari, tana Sanye da glass fari a'idonta, kana ganinta kaga mace yar Gayu, da alama daga Asbiti take wajan aikinta, da kukan Waheeda tafara cin Karo, Kai tsaye Dakin nasu ta nufa, 'Yan biyu suna ganinta suka daina Dukan Waheeda, haka tadago kanta idonnan yayi jajir tace "Kuma wallahi saina Rama, bashi kuka dauka"
Hajiya Anty batace dasu komai ba taja Dakin tarufe, tawuce wajan ummah, Sai a lokacin ummah tashigo Dakin nasu taji ba'asin fadan, da alama Hajiya Anty ce ta turo ta, Dan lokacin dazata shiga Dakin nasu ma mita take tana cewa fitinar Waheeda ta isheta☹ï¸
Da yamma sukai baqi daga qauye, a lokacin hajiya Anty tana nan bata tafi ba, megadi ne yayi musu jagora har cikin falon gidan, Anty Maryam de Takoma gidanta, Amma gaba dayansu yaran suna Nan, 'Yan biyu suna zaune waje daya suna ganin wani abu a wayar ihsan, Waheeda kuwa tana zaune agefe cikin kujera ita daya, tunda 'yan'uwan suka daketa taketa kumburi, taso ace ummah da Hajiya Anty basa Nan, dasai tahada wa 'yanbiyu wata muguntar da bazasu taba mantawa da'ita ba, yanda ta zauna waje daya tayi shiru zaka rantse wata kamilar yarinya ce, saboda ta nutsu sosai kamar ba'ita ba,itace tafara tashi takawo musu lemuka da ruwa, sannan ta gaishe su, aikuwa suka amsa cikin girmama wa, tasake komawa wajan zamanta ta zauna, Ummah takalle su cikin sakin fuska tace "Saide kuyi hakuri fa, Amma bamu gane Kuba"
Namijin ne yafara dariya yace "Hajiya ai 'yan'uwan kune daga wani gari Kaburma, ai Alhaji Habu ne yace duk lokacin da muka shigo Garin naku, mu qaraso mu gaisa nida iyalina, aini kamar qani nake awajansa" yafadi maganar yana Kallan Waheeda
Waheeda ta Kalle shi dakyau, Bama qanin bane kenan, kama ce, tunda yace kamar qani yake a wajan Baba Habu, Kai Shima de Baba Habu da yayime-yayime yake, ita Kuma umma Sai washe musu baki take
Hajiya Anty tace "Amma kun kyauta wallahi, ai Gara daban wuce gida ba, yanzu gashi munga juna"
Matar datake gefen namijin tace "Eh wallahi, ai Baba Habu akwai zumunci, Amma wadannan Yan biyu ne ko?"
Ta qarasa maganar tana Kallan Yan biyu
Dariya sukayi sannan suka amsa mata, Tajuya tasake Kallan gefen da Waheeda take zaune tace "kekuma fa qawata kinyi shiru babu ruwanki da kowa"
'yanbiyu ne suka hada ido suka kwashe da dariya, Wai Waheeda ce babu ruwanta, shine abunda ya basu dariya
Matar tace "yakuke mata dariya, ai Naga tayi shiru da alama zatayi hakuri,qawata ya sunanki?"
Waheeda tayi murmushi tace"sunana Waheeda"
Kallan mijinta tayi tace "Baban Halima kaji suna me dadi, idan nasake haihuwa Nima ka sakawa yarmu irin wannan sunan"
Dariya yayi, ya kalli Yan biyu, ya kalli Waheeda, yace "yanzu Nan duk 'ya'yanane?"
Dariya sukayi kawai, babu wadda tace masa komai, yace "toku Yan tagwaye wayece babba acikin ku?"
Ihsan tace "nice babba, Sai Intisar, Sai qanwarmu Waheeda"
Washe baki yayi yace "ikon Allah kenan, toke ashe kece Gambon su"
Waheeda tace "Uhm..." Daga Nan tatashi tayi daki
Matarsa tace "Allah sarki, kunga ita tatafi daki ma babu ruwanta baiwar Allah, Baban Halima Bari naje wajanta musha hira"
Tatashi tabi Bayan Waheeda, duk yanda taso share matar hakan bai iyu ba, Dan dolenta tasaki jiki da'ita suka Sha hirarsu, Sai yamma lis suka tafi, Hajiya Anty taje gidanta takawo wa matar atamfa da kudi, ummah Kuma tabasu kayan abinci sannan tasa driver yamaidasu har gida.