Sashe 24
Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayancewa yayi yace "ke wasa nake miki, banason shirme, kawai.... Kawai de... Banji dadin yanda Daddy yamin maganar lefe bane"
Ya qarasa maganar a rarrabe fuskar sa cikeda fishi
"nikuma Babban Yaya banga abun fishi anan ba, zaka iya auren wadda kakeso daga baya"
Cikin 6acin rai yace "Kina tunanin zan hada abinda nakeso dawani abu daban? Kinga banason damuwa, muje kunfara shiga jirgi"
Kanta ta gyada masa batare datace komai ba suka tafi, saida yaga jirginsu yatashi sannan yakoma gida
Jirginsu yana sauka taga driver yana jiranta, mamaki ya kamashi ya kalleta dakyau yace "Waheeda yanaga kin sake kyau? Me yayan naku yake baki?" 🤔
Harararsa tayi tace "shafa kaji, ka bude min mota kawai, Kuma gidan Hajiya Anty zaka kaini"
Jinjina Kansa yayi, yasan rashin kunyar Waheeda, zatayi yafi haka, jakar hannunta ya kar6a sannan yace "lalle Waheeda idan kikai shekara a qasar waje bazamu ganeki ba, cikin abunda baifi 'Yan kwanaki ba kikai irin wannan kyau haka?"🤔
Tana jinsa tasaki wani Dan qaramin tsaki, damuwar ta daya yanzu shine Ummah, bata Isa taje wajan Ummah ba, Gara ta gudu gidan Hajiya Anty yafi sauqi
Suna hanya ta turawa Babban Yaya text cewa ta sauka, Saukarsu gidan Hajiya Anty keda wuya taci Karo da wasu akwatuna masu shegen kyau guda ashirin da hudu, dozin daya pink colour, dozin daya blue, akwatunan ne suka dauki hankalin ta, tafara ta6a jikinsu tana qwalawa hajiya Anty kira, futowa tayi daga d'akin ta tayi mutuqar kyau cikin atamfa dinkin Riga da siket, kullum cikin Gayu take bata gajiya
Tana ganin Waheeda tace "Oyoyo daughter" tafadi hakan tareda bude hannayenta, babu musu Waheeda tashige jikinta, Hajiya Anty ta rungume ta tanajin qaunar yarinyar acikin zuciyar ta
Zama sukai akan kujera Waheeda tasake Kallan kayan tace "Anty lefen Babban Yaya ne wannan?"
"lefensa ne, Uncle dinku ne yayi order su daga Dubai, abubuwa kad'an muka qara anan, Amma ba'a saka mata pant da brezia ba, zan Mai magana saiya tambayeta size dinta"
Waheeda tayi ajiyar zuciya "Anty Babban Yaya fa baya son auren Nan, kukuma Naga kun dage"
"zaiso ne Idan akayi, ai kinsan qiyaiya tana komawa soyaiya"
"to Anty, Allah yarufa asiri"
Anty tace "Amin ya Allah, kibude kigani mana"
"a a Anty, basai nagani ba, Allah ya basu Zaman lafiya"
Hajiya Anty tayi murmushi, takasa gane yanayin yarinyar, shin kishi take, kokuma kawai 6acin raine Dan taga yayan Nata ma baya son auren? 🤔
A gidan Hajiya Anty tayi Zaman ta har kusan sati daya da dawowar ta, koda wasa bata nufi gidan Ummah ba, sauqin ta daya, suna cikin hutu
Ranar da tayi kwana Tara, ranar su yanbiyu suka dawo daga Saudia, murnar dawowar yan'uwan Nata ne yasa tatafi gidansu, Hajiya Anty tarakata suka tafi tare, lafiya kalau suka gaisa da kowa, anan falon aka baje Ana hira, Ihsan ta kalli Waheeda tace "shikkenan Waheeda kin luser bakije Saudi ba" tafadi hakan cikin sigar tsokana
Waheeda ta yatsina fuska tace "ai zuwa makkah Kiran Allah ne, dama can banda ni yakira, Nan da lokaci kadan kunaji Kuna Gani zamu tafi nid Babban Yaya" tana fadar haka tatashi ta wuce dakinsu
Sa'ad da Sa'eed suka bita da kallo, Sa'eed yace "Sa'ad kasaka yarinyar Nan acikin addu'ah kuwa da mukaje Saudia?"🤔
Kafin Sa'ad yabawa dan'uwan nasa amsa, Ummah tatashi taciro wayar charger tabawa Sa'eed tace "jeka zanemin yarinyar can"
Babu musu kuwa Sa'eed yanufi Dakin nasu, adede lokacin Waheeda tacire Kaya zata shiga wanka, daga ita Sai towel, lokaci daya taji saukar duka ajikinta, ihu tasaki, su Ihsan suka qaraso Dakin suna temakon ta, memakon ya qyaleta, saiya had'a dasu yakama duka, aikuwa babu shiri suka futo kowacce tana Sosa jiki
(duk Wanda ya karanta min littafi be biya ba shida Allah)
Saida yayi mata lilis sannan Yabarta, yana futowa daga d'akin Daddy yashigo, ya zauna a kujera, cikin ladabi hajiya Anty ta gaishe shi sannan tayi musu sallama tatafi, Kallan Ihsan yayi yace "jeki kiramin qanwarku"
Dakinsu tashiga, Waheeda tana kwance aqasan Dakin tana kuka, duk jikinta yayi ja inda wayar tata6a ta,idanunta har sun kumbura gashi sunyi jajir dasu, fada mata saqon Daddy tayi, cikin kuka Waheeda tace "Dan Allah Ihsan d'agani, wallahi bazan iya tashi ba"
Ihsan ta kamata tatashi zaune har towel din yana kokarin cirewa, hijabi tabata tasaka, sannan suka futo falon, zama tayi aqasa tana sheshshekar kuka ahankali, Ummah ta kalleta tace "marar mutunci Ina wayata take?"
Cikin kuka tace "Dan Allah Ummah kiyi hakuri, wayar tana daki, Dan Allah karku fadawa Babban Yaya"
Daddy yace "Waheeda zancen Babban Yaya aiya qare, kifada wa shi wannan Yaron dayake zuwa wajanki yafuto ayi muku aure inda gaske yake, idan Kuma bakya sonsa to akwai huzaifa Yaron Abokina zaizo Shima ki ganshi idan yamiki shikkenan, bazaki gama karatu kamar yan'uwan kiba, aure zan miki "
Waheeda najin haka ta rushe da Kuka tafara Bawa Daddy hakuri, Amma mursisi haka Daddy yatashi yayi daki Yabarta anan, intisar ce ta kamata suka koma daki harda Ihsan ma, suna zuwa Dakin suka fara bata haquri, Amma Inaaa Waheeda Sai kuka take har kanta yazo yafara ciwo, daga qarshe, wani irin zazza6i me zafi yarufe ta
Da asuba daqyar tayi sallah Takoma ta kwanta, ko Yaya ta motsa jikinta saita runtse ido saboda yanda ko'ina na jikinta yake mata ciwo, qarfe goma da rabi Ummah taga abun na Waheeda gaba yake, tun jiya jiki yaqi dadi, Nan da Nan Kuma Hankalinta yatashi, tasa Sa'ad yakaita Asbiti, yanbiyu ne suka shirya ta suka tafi gaba dayansu.
Suna fita wayar Ummah tayi qara, number tagani, ta dauka tareda sallama, daga d'ayan bangaren akace "Mama Huzaifa ne"
Ummah ta fada da fara'art tace "Au Huzaifa, ashe kaine, ya mutanan gida"
"suna Nan kalau Alhamdulillah" daga Nan Kuma Sai yayi shiru baice komai ba
Ummah data fahimci inda yasa gaba, saitace "Huzaifa Waheedan bataji dadi bane, sunje Asbiti yanzu, Amma idan suka dawo, zata kiraka"
Cikin tsantsar damuwa yace "subhanallah.... Ummah meyake damunta? Suna wanne Asbiti, meyake damunta....?"
Ummah ta jijjiga Kai ganin yanda Yaron yarikice lokaci d'aya, tace "suna wani private Hospital Annoor"
Godia yayi mata, sannan yakashe wayar
(idan kinsan bada yardata kika karanta wannan littafin ba, keda Allah, nabarki da Allah, koba yauba karkizo neman yafiya ta ehe)
*** *** **
suna zuwa Asbitin Waheeda ta yanke jiki tafadi,bayan likita ta dubata tace "yarinyar Nan akwai qarancin jini ajikinta, dole zamu qara mata jini leda d'aya zuwa biyu"
Nanfa hankalin 'yan'uwan Nata yatashi, Sa'ad ya kira Ummah yafad'a mata halin da ake ciki, cikin tashin Hankali tace "gatanan zuwa"
Gidan Hajiya Anty tatafi, daga Nan suka nufi asbitin, suna zuwa adede lokacin Shima Huzaifa yazo, had'ad'd'en Gaye ne nabugawa a jarida, wankan tarwada ne, yanada tsayinsa daidai misali, kana ganinsa kasan hutu da jin dadi sun zauna masa, tare suka shiga Dakin da aka kwantar da Waheeda, suna zuwa kuwa numfashin ta yafara yin sama kamar zata suma, hankalin Ummah yatashi, Nan da Nan tafara hawaye, Hajiya Anty tace "Haba Hajiya, idan kina kuka sukuma yaran mezasuyi kenan?"
Kafin Ummah tabata amsa tajuya ta kalli likitar tace "doctor me kuke jirana Baku saka mata jinin ba?"
Likita tace "wallahi hajiya bamuda irin jininta, anje asiyo har yanzu basu dawo ba, group o gareta, jinin yana mana wahalar samu"
Cikin 6acin rai tace "jini yana wahala kenan haka Zaku Barta tamutu mune da asara kenan?"
Likitan tace "Hajiya Bahaka bane kiyi hakur...."
Gyaran murya Huzaifa yayi yace "A a, Anty kiyi hakuri, zanbata, irin jinina ne"
ya kalli doctor yace
"muje lab din ku d'iba"
Tafiya sukai,ya kwanta aka 'Debi jininsa, zasu gwada ko akwai wata cutar, tunani huzaifa yayi hakanma qarin wani 6ata lokacin ne, yafada musu su dauka kawai a saka mata, shi lafiyarsa kalau, haka ya kwanta aka Debi jininsa leda biyu, sannan taje ta daurawa Waheeda tareda allurar bacci, shikuma ya kwanta zuwa wani lokaci sannan yatashi yakoma Dakin da aka kwantar da Waheeda yaharde hannun sa a qirjinsa yana qare mata kallo, Sai yanzu nema yake sake ganin tsantsar kyanta, lokaci daya yaji sonta yana sake qaruwa acikin zuciyar sa, idan bai sameta ba, bayajin zai iya yin aure a rayuwar sa
Sai dare sannan Waheeda taji Dama Dama aka sallameta tareda alqawarin hajiya Anty zataci gaba da dubata agida.
har zuwa wannan lokacin Huzaifa yana Nan bai tafi ba, su 'yanbiyu Sai Kallan sa suke afakaice suna gulma ganin yanda yake komai nasa cikin aji da kamun Kai, saida sukaje gida lokacin karfe Tara nadare, sannan yayi musu sallama yatafi
Washe gari da safe ya dawo dubata, babu laifi jikin Nata akwai sauqi sosai, har falo aka shigo dashi, ta zumbula hijab dinta tafita, kallanta yayi yace "Baby yajikin?"
Wasa take da yatsun hannunta kanta aqasa tace "Alhamdulillah Yaya"
Yatsina fuska yayi yace "Yaya Kuma Waheeda? No.. No... Banason sunan Nan, ki sauya min wani"
Daga Masa Kai tayi, ledar dake hannun sa ya ajiye agabanta, yace "dazan taho ne nashiga super market namiki shopping, nasan bakinki babu dadi tunda rashin lafiya kikayi"
Kanta yana qasa tace "to nagode"
Dan qaramin murmushi yayi yace "Waheeda bazaki Kalle niba?"
Dagowa tayi ta Kalle shi, Saitayi saurin sunkuyar da kanta qasa, sakamakon wani irin abu dataga yana futowa daga Idonsa yana shiga Nata, gabantane yafadi, harta kasa 6oyewa saida tasa hannunta a setin qirjinta, huzaifa yana ganin haka yayi tunanin ko jikin Nata ne yatashi, ahankali yace"sorry na tsaida ke, nasan kin gaji ko? "
Hannunsa yasaka acikin aljihu ya Dauko wani zobe na gold me kyau, yamiqa mata tafin Hannunsa yace" Bani hannunki "
Kallan sa tayi da mamaki, shikuma ya Dan daure fuska yace"bani mana"
Ahankali tad'ora tafin hannunta akan nasa, yatsun hannun ya kalla Zara Zara dasu dogaye, akwai zoben gold a hannunta Wanda Babban Yaya yasiya musu, saiya cire shi yasaka mata nasa yace"wannan yafi kyau, karki cire shi"🙊🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Daga masa Kai tayi, ya dauki wayarsa yayi kira, Ana dauka taji yace "Momy ga Waheeda ku gaisa"
Daga bangaren ta tace "to bata wayar"
Waheeda yabawa wayar yace "ga momy na zaku gaisa"
Waheeda ta karba suka gaisa da'ita cikin mutunci, sannan ta bashi wayar, shikuma yayi mata sallama yatafi