← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 48

Sashe 21

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy yayi murmushi yace "ranka yadad'e, kwana dayawa ba'a jinka"

Minister yace "wallahi kasan koda yaushe muna ta Fama da jama'ah, yanzu ma yarona ne Huzaifa yasaka ni agaba lalle lalle saina kiraka"

Daddy yace "a a ikon Allah, Huzaifa ya dawo qasar ne?"

Minister yace "wallahi ya dawo, cikin ikon Allah ya kammala karatun sa lafiya ya dawo, yazo ya sameni ne akan maganar 'yar wajanka, last week yaje 'Dauko sisters d'insa daga school sunyi party na candy, anan yaga yar wajanka Waheeda yace yanaso, shine da yayi bincike yagano 'yarka ce, Kuma kasan akwai sanaiya a tsakani, shine yace ayi masa tambaya aji ko an yiwa wani alqawari? "

Daddy yace"A a babu alqawarin kowa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi "

Daga d'ayan bangaren minister yayi godia tareda kashe wayar

Babban Yaya yanajin wayar da Daddy yake jikinsa yabashi akan Waheeda ake magana, Bai nuna komai akan fuskar saba, lafiya kalau suka gama cin abincin sannan ya dauki key din mota yafice daga gidan

Da yamma Didat yazo tareda abokinsa Mukhtar, yau wankan qananun Kaya yayi, ba qaramin kyau yayi ba, suna cikin zance da Waheeda yace "Gimbiya inaso kije gida ki fad'awa Ummah zamuje shopping idan ta amince"

Babu musu Waheeda ta wuce gida ta fad'a wa Ummah abinda Didat yace, Ummah tace "to karki tafi ke kad'ai, kuje keda yan'uwan ki"

'Dakinsu ta wuce, ta tarar Ihsan na wanka, Sai intisar dake karatu, tare suka futo da intisar basu jira Ihsan ba, suna zuwa kuwa Didat yace "lalle babbar Yaya, yanzu ashe Kuna ciki kun 6uya, ko sau d'aya bantaba ganinku ba"

Intisar tace "Wallahi muna Nan, abubuwa ne sukai yawa, yakake"

"Alhamdulillah, Ina lafiya kamar yanda gimbiya Waheeda take, dafatan de tare dake zamuje shopping din?"

Intisar tace "babu damuwa muje"

Tsayawa sukai suna jira yabud'e musu kamar yanda Babban Yaya yake musu, shikuma harya shiga motar, saida yajuya ya gansu a inda suke sannan yayi murmushi yazo ya bud'ewa Waheeda gaba, intisar Kuma suka zauna Abaya tareda abokinsa, suna hanya abokin Sai Jan intisar yake da zance, tana amsa masa kad'an kad'an, a wajan shopping d'inma Didat Kam kawai binta yake yana aikin kallon ta kamar wani sakarai, itace me za6ar komai, saida yakashe mata kud'i me yawa sannan suka Juyo gida, tun a hanya yaga tana amsa masa daqyar, Sai yatsina fuska take, suna qarasa wa gida kuwa intisar tayi ciki, ita Kuma Waheeda ta tsaya suna sake tattaunawa, Kallan ta yayi yace "Meyake damunki ne? Naga kamar bakya jin dadi"

Yatsina fuska tayi tace "wallahi jinake zazza6i yana son kamani"

Cikin rud'ewa Didat yace "Subhanallah, Amma shine kikai shiru? Meyasa baki fad'amin ba muje Asbiti?"

Tace "Babu damuwa, zansha pracitamol agida"

Didat yace "no, ga Mukhtar Nan yayi miki injection mana, akwai saura acikin motata Ina siya Dama saboda 6acin rana, idan kikaje gida saiki kwanta kihuta, Shima doctor ne"

Cikin damuwa Waheeda tace "no, karka damu wallahi"

Didat yace "a a, tsaya yayi miki please"

Bud'e motar yayi, ya 'Dauko allurar yabawa Mukhtar, Mukhtar ya kar6a yafasa ruwan allurar, ya kalli Didat yace "Ina sirinji?"

Didat yace "aikuwa na manta wallahi babu, but ga Wanda akamin allura dashi ban yarda shi ba, kayi mata dashi kawai"🙆🏻‍♀�

Kallan Waheeda Mukhtar yayi yace "babu damuwa ayi miki gimbiya?"

Tace "babu damuwa"

Kar6ar sirinjin yayi yazuqe ruwan allurar, sannan yayi mata a hannunta, basu qara ko minti biyar ba, sukai sallama, tajuya zata tafi gida, adede lokacin Babban Yaya ya dawo gidan, fuskarsa ad'aure take babu wasa, ya gansu Amma saiya nuna baima gansu ba, Didat da baisan da shigo war Babban Yaya ba, ya qwalawa Waheeda kira, tana juyowa yayi kissing hannun sa, sannan yahura mata tareda kashe mata ido, yashige cikin motarsa

Babban Yaya yana Kallan su, yakashe motarsa Bayan ya ajiye ta a parking space yafuto, adede kofar shiga falon suka had'u da juna, cikin ladabi tace "Sannu da zuwa Babban Yaya"

Cikin 6acin rai yace "aikece za'ayi wa sannu,mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi, Kin tsaya yana miki hauka Amma ko ajikinki, kwata kwata bakya kishin kanki, idan kikai wasa naqara ganin qafar Yaron Nan a gidan Nan saina kakkarya qasusuwanki ...."

"Subhanallahi .... Naufal?"
Cewar Hajiya Anty da shigowarta kenan taga yana zazzaga wa Waheeda masifa

Kallan ta yayi, yayi qasa da Kansa, idanun Nan nasa sunyi jajir tsabar 6acin rai, Sai huci yake kamar zai Fashe, ita kanta hajiya Anty ta tsorata da yana yinsa, ta kalli Waheeda datake share hawaye tace "Ke wuce ciki"

Kallan sa tayi tace "Kayi hakuri" sannan ta wuce cikin falon nasu

Hajiya Anty ta kalli Babban Yaya tace "yanzu bakaji kunya ba? Kagama yimata fad'a Amma daga qarshe haquri take baka ko kallo bata isheka ba? Hakan dakayi daidai ne kenan?"

Yace "Anty kissing dinta fa yayi" yayi maganar kamar zai Fashe da Kuka

Hajiya Anty tace "to naji tayi laifi wannan fad'an dakake mata shine zaisa ta nutsu? Qanwarka cefa, jininka ce tayaya bazakaja yarinya a jikinka ba zakadinga mata fada irin haka,?to tun tana jin tsoron ka, watarana zata daina, kaja Qanwarka a jikinka kaji nafada ma, fad'a ko duka basa shiryar da yaro"

Qwalla ce take son futowa daga idanunsa yana dannewa, idan yatuna yanda Didat yake huro mata kiss, jiyake kamar yayi ihu, cikin 6acin rai yace "Anty niba qanwata bace, kidena cewa Qanwata"

Hajiya Anty tayi sakare tana Kallan sa, a fili tace "ikon Allah, to ba Qanwarka bace, karka jata a jikinka, gata Nan ka kashe ta"

Daga haka tajuya cikin gida tabarshi a wajan, Shima shigewa yayi ransa a6ace

Tunda yashigo 'Dakin yakasa sukuni, tunani yayi masa yawa, daga qarshe ma tashi yayi yafara had'a kayansa, gobe da safe zai koma England bakin aikinsa, kwata kwata bayajin zai iya zama yana ganinta tana mu'amula da wani namijin bashi ba

Cikin qanqanin lokaci yagama had'a komai,kawai jiran wayewar gari yake

Kamar wasa Waheeda tana kwanciya bacci ya dauketa marar dadi, sakamakon abinda yafaru tsakanin ta da Babban Yaya , haka Shima anasa bangaren, baiji dadin baccin ba, har yanzu wannan kiss d'in ya tsaya masa aqahon zuciyar sa,washe gari kalau tatashi babu wani alamun zazza6i atare da'ita, 'yanbiyu basa 'Dakin Sai ita kad'ai take juyinta akan gadon, doguwar Riga ce ajikinta ta bacci Amma me kauri, bata nuna shape dinta ba kwata kwata, saide kana iya ganin tsayayyun breast dinta yanda suka tsaya a tsaye cak tacikin rigar, brush taje tayi tadawo 'Dakin nasu taga Maya na kiranta awaya, d'auka tayi tace "uwar 'Yan Fassara ya akayi?"

Maya tace "ke dalla malama yau babu Fassara,Wai baqi mukai daga Abuja, shine wani daga cikin su yace yanaso na, ya tambayi mama yaushe zan gama karatu tace masa nanda wata shida, nikuma gaskiya Waheeda banason aure yanzu, nafison nayi karatu me zurfi, sannan baki ganshi ba Babba nefa, yakai Babban Yaya girma da shekaru, ko kunya babu waini yakeso, Dan Allah tayaya zan iya Zaman aure dashi Aida kunya"

Waheeda takwashe da dariya tace "lalle ma Maya, to miye abun kunya? Tab wallahi karkiji kunya, ba aurenki zaiyi ba? Aiba haramun bane"

Ummah ce tashigo 'Dakin zata fad'awa Waheeda taje gidan Hajiya Anty takira mata 'yanbiyu, Sai tajita tana waya, saboda haka saita dakata tagama wayar sannan ta fad'a mata Aiken, ita Kuma Waheeda kwata kwata bataji shigo war kowa Dakin ba
Daga d'ayan bangaren Maya tace "ke bazaki gane ba, novel damuke karantawa duk fa abinda akeyi a novel idan akayi aure Nima fa haka zanyi, wallahi bazan amince ba babu ruwana, ni kunyarsa nakeji, gashi qato"

Waheeda tasake fashewa da dariya tace "nikuma idan nice keko wallahi amincewa zanyi, tabdi to menene aciki ba mijina bane? Har wankansa zan dinga yi, keni har abar tasu zan kama na wanke, qarshe de kenan....." 🙊🙈🙆🏻‍♀�

Hawaye ne ya silalo daga idanun Ummah, innalillahi wa inna ilaihirraji'un yanzu Waheedanta ce take wannan maganar?Har abar zata kama ta wanke? Cikin kuka Ummah tace"Waheeda?"

Gaban Waheeda ne yayi wata irin bugawa, kanta ya Sara, cikin sauri ta kashe wayar jikinta yana rawa,ko'ina na jikinta kyarma yake tama kasa yiwa Ummah magana Sai kanta datake girgizawa alamun Bahaka bane

Ummah tayi kukan kura ta kamata tafara dukanta, ihu take tana neman temako Amma babu kowa a gidan, cikin ikon Allah tasamu tafuto daga 'Dakin, Ummah ta zauna a wajan tana kuka.

tana zuwa compound adede lokacin shikuma yashiga motarsa kenan zai rufeta, ganinta yayi aguje ta nufoshi, kanta babu ko dankwali Sai dogon gashinta daya bazu agadon bayanta, kana ganinta kasan tana cikin mutuqar tashin Hankali,saboda fuskarta ma kadai gumi ne yake futowa ga hawaye sha6e-sha6e tanayi, duk ta rikice jikinta yana rawa kamar mazari, hakan yabawa cikakkun Breast dinta damar rawa kamar Wanda take kad'asu da niyya, tunawa da tayi jiya ransa ya6aci saboda ita, Sai taja ta tsaya cak a wajan tana waigen Bayan ta ko Ummah zata biyota, saboda tasan cewa Shima tana zuwa wajansa Dukan ta zaiyi.

tausayi ta bashi, lokaci d'aya jikinsa yayi Sanyi, duk yanda akai ba qaramin laifi tayi ba, shiyasa take neman mafaka, dama shine Mai taimaka matan, to Shima yanzu tsoron zuwa take, tana tsoron tunkararsa saboda tasan confirm zaiyi mata hukunci, tunowa yayi da fad'an Hajiya Anty, Kuma yasan idan Yabarta ma zataci gaba da haduwa da wannan Yaron ne, yanzu yana hura mata kiss, to gaba gaba kiss din zaiyi mata a aikace, Gara ma sutafi tare kowa ya huta, ahankali tamkar baya son magana yace mata "shigo mutafi"

Ai kamar jira Waheeda take , cikin sauri ta fad'a cikin motar, yayi mata key suka bar gidan
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama😇: BB
Chapter 21 · 0% Book details