← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Habu yace "kaji wani sakarci, tokai kana namiji Ina kaga ta zama? Sa'adun ne ko Sa'eedu? Namiji baya zama, kutashi muje"

Sa'ad yayi dariya yace "Sa'eed ne baba, ka ganeshi dakyau"

Haka suka fita badan ransu yasoba, mama Haajara ta kalli tukunyar da Waheeda ta 'Dora, tace "Waheeda wannan tukunyar a6ule take" Waheeda hankalin ta yana kan girki batajiba

Ihsan tace "Waheeda tukunyar da kika Dora a6ule take fa"

Juyowa tayi ta Kalle su, dama aciki take dasu, suna ganin ta tana aiki Amma babu Wanda ya taso acikinsu,sun Barta tana Fama da hayaqi, dankwalinta ta turo gaba, tulun dogon gashinta yafuto ta qeyarta, tace "kibarta taita zuba, Ina wuta tana ruwa, Sai muga wa Allah zai Bawa sa'ah"

Mama Haajara tayi dariya tace "a a Waheeda, ba za'ayi hakaba" tatashi ta nufi wajan girkin, suma yanbiyu suka taso, saita basu salat da tumatir su yanka

Majalissa Majalissa Baba Habu yake yawo dasu Babban Yaya yana nunawa abokai da yan'uwan Arziqi su, kan kace me, matasa sun taru a wajan Babban Yaya, wasu suyi photo wasu Kuma videos, wasu Kuma kawai binsa suke sunata zance, ayawon zaga Garin dasuke suka hadu dasu Yahya, sune suka janye Babban Yaya kasancewar su sa'anni,sannan suka nufi gonar dashi, daga baya baba Habu ya qaraso tareda su Sa'ad, gonakin yafara nuna musu yace "wannan Babbar gonar ta Usman ce, gata Umaru can agaba, duk ni nake kula musu dashi, dazaku iya da munje wasu gonakin daku duk kun Gani"

Babban Yaya yace "Baba gobe Sai muje ai, Sai muga gari ma"

Baba Habu yayi fara'ah yace "eto Kuma kaima kace wani abu, yanzu to riqe wannan fartanyar, gyara min Nan wajan kacire ciyawar nan data futo" 😂

Sa'ad yace "baba muda mukazo ganin gona Kuma saimu fara aiki?"🤔

"aiku ba mazaje bane, kubar namiji yayi aiki"

Babban Yaya yarasa abinda yake masa dadi, haka ya karba yafara cire ciyawar dasuka futo, abokan baba Habu ne sukazo wuce wa ya daga murya yace "malam idi, ku qaraso ku gaisa da yarana Yan birni"

Su malam idi suna zuwa sukace "masha Allah, Wai duka Nan yaran Usman da Umaru ne?"

Baba Habu yace "a a, duka yaran Umaru ne, shi Usman ai babu yaro awajansa"

Ya nuna musu Babban Yaya da Kansa yake sunkuye yana Fama da fartanya, yace "ga Babban yayansu Nan nasashi aiki, kuduba kuga qwanjinsa fa, inda zai haqura da wannan tamolar ya dawo Nan mudinga noma Aida yaji dadi, dashi kadai zanbarwa wannan gonar ya nome min ita, haba meza'ai da wata tamola" ☹️ya qarasa maganar yana yatsina fuska

Shide Babban Yaya baice komai ba, Sai abokan baba Habu dinne dasuke dariya dakuma su Sa'ad
Baba Habu yasake Kallan sa yace "kunji yayi shiru kamar salihi, Nan kuwa qungurmin tuzuru ne"

Babban Yaya baice komai ba yanzun ma, Shide fatansa yarabu da wannan tsohon lafiya, abokan nasa ne sukace "ai yanada Hankali, yanzu awannan zamanin ba kowanne Yaya ne zai debo qannan sa yakawo su ganin dangi ba"😂

Baba Habu yace "Eto tanan Kuma yayi qoqari"

Ya kalli Babban Yaya yace "dago haka, muje gida muci abinci kun debo hanya"

Sai a lokacin Babban Yaya yadago, fuskar Nan tasa a daure, babu wasa, haka suka tafi gida, yanbiyu da Waheeda suka zubawa kowa abinci, duk da yaran baba Habu suna zaune aqauye ne hakan baya Hana ganin tsantsar kamar dasuke dasu Babban Yaya, kana ganinsu kaga jini daya.

Baba Habu ya kalli Babban Yaya yace "Ai kamata yayi daga Nan kunufi gida can Niger, can ma kuje kuga yan'uwa"

Sani yayan Yahya yace "qwarai Kam baba, kaga Yan biyu da Waheeda ma Sai suhau a male, nasan basu taba Hawa ba"

Babban Yaya yace "saide wani lokacin baba, saboda makarantar su, idan aka musu hutu, Sai muje"

Uzurin daya basu ne yasa suka amince da maganar tasa, Amma badan makaranta ba, yasan Sai sunje.

Washe gari suka fita ganin gari da safe, Waheeda wani Riga da wando tasaka, kayan sun kamata sosai, amma data saka dogon hijabi babu Wanda yake ganin ta, sunga gari sosai, sune har Rafi ganin ruwa, su Sa'ad suna tareda su Yahya, shikuma Babban Yaya yana bayansu Waheeda yana tafiya yana danna wayarsa.

Fakar Idonsa Waheeda tayi, tacire hijabin Nata,hips dinta yacika wandon taf, sannan ta tattare qafar wandon, tashiga ruwan tafara wasa, suma yanbiyu da sukaga Babban Yaya hankalinsa yana kan waya suma suka shiga, dago Kansa yayi ya gansu suna wasa, bece musu komai ba yanemi waje ya zauna yaci gaba da abunda yake

Cikin tashin Hankali yanbiyu suka fara Kiran sunansa, suna nuna masa Waheeda, yana dago Kansa ya hango Waheeda acan tsakiyar ruwa tana mututuwa idonta Sai juyawa suke ruwa yana gaba da'ita, baisan lokacin da yayi jifa da wayar ba, ya qwala mata kira, sannan yanufe ta da gudu

Yanbiyu suka futo da gudu sukayi wajan su Yahya da Sa'eed zasu fada musu

Batare da tunanin komai ba, Babban Yaya yafad'a cikin ruwan, kafin ma ya qarasa wajan ta hartasha ruwa ta suma, d'aukota yayi tamkar ya dauki jaririya

Cikin tashin Hankali yafara tatta6a jikinta yaji shiru, jikinsa ne yad'auki rawa, fuskarta yakama yariqe yana fadin "ke! ke!! Dan Allah karki tafi"

Jijjigata yake yana fadin haka Amma Waheeda shiru ko motsi takasa, gaba d'aya yanemi nutsuwar sa Yarasa, gabansa yafara fad'uwa kana Kallan faffad'an qirjinsa zaka tabbatar da haka, ta hanyar bugun zuciyar sa, shiru yayi yarasa abin yi, tunani yayi Ana danna cikin Wanda yasha ruwa, yasaka hannunsa akan shafaffan cikinta ya danna Amma ruwa be futo ta bakinta ba, zuciyarsa ce take bashi wata shawara yana yakicewa, daga qarshe Sai ra'ayin zuciyar tasa yabi, saida ya qarewa lallausan pink lips d'inta kallo, sannan ahankali ya sunkuya yahad'e bakinsu waje d'aya🙆🏻‍♀�
Duk yanda zuciyarsa take gargad'insa akan kar yayi komai Bayan iska dazai hura cikin bakin Nata, hakan bai samu ba, laushi da Kuma santsi irin na lips din Waheeda ya d'ebeshi yafara kissing dinta,wannan ne Karon farko daya ta6a kissing din mace a rayuwar sa,wani irin dad'i yaji sosai,saida ya tsotsi lips dinta son ransa, sannan yahura mata iska cikin bakinta da qarfi, sannan ya d'auke lips d'insa daga kan Nata.
wani irin Tari ne yataso mata, a Hankali tafara bud'e idonta, harta bud'esu gaba d'aya, ta d'orasu akan Babban Yaya daya zuba mata ido yana Kallan ta, babu Wanda ya tankawa d'an'uwansa acikinsu, Sai ido dasuka zubawa juna, kowa yana tunani cikin Ransa, tsantsar kyawun dan'uwan Nata take kallo, haqiqa yahad'u harya gaji da had'uwa, shi abin sone ta kowanne fanni,ita kanta tana sarawa yayan nasu wajan iya Gayu dakuma d'aukar wanka.

idanunta Babban Yaya yake kalla a zahiri, Amma abad'ini yayi Nisa cikin tunani, inama zata soshi kamar yanda yake sonta?koda yaushe zuciyarsa tana fad'a masa cewa, bashida mata Sama da'ita, ita din tasa ce shi kad'ai, but tayaya hakan zai kasance?

To Alhamdulillah free page yazo qarshe 🥱

Gashi zan Dena yimuku posting Baku fadamin suwaye iyayen Naufal da Waheeda ba😂😂

Dama nafada muku BABBAN YAYA na kudi neko?
Ina Wadanda suke buqatar jin qarshan labarin? Kwamacala tana gaba aradu, yanzu aka fara wasan 💃💃💃

Da abaka labari gwara ka bayar 👇🏻

200 posting daya a rana

VIP 400 posting biyu a rana

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaku turo shedar biya ta wannan number👇🏻
08033300034

Ga masu kira, text message, whtsapp, duk ku nemeni ta wannan number👉🏻 08033300034

Next Novel SHAHAB.....

Salonsa daban yake, zaizo muku bada dadewa ba 💃💃💃

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama😇: Jikinsa ne yayi Sanyi Bayan tunawa da irin qalubalen dayake gabansa akan hakan, ahankali yakawar da fuskar sa Gefe, sannan ya tashi zaune yakama hannunta yariqe yana kokarin tashinta, jitayi kamar bashida qarfi, taga jikinsa yayi Sanyi, shi kuwa Babban Yaya yanayin daya shiga ciki ne bai gama sakinsa ba, ashe haka akeji? Kokuma de shine yaji dadin sosai saboda wadda yake soce yayiwa kiss din? Tashi tayi zaune, har zuwa lokacin hannunta cikin nasa, tana 'Dan qaramin Tari kad'an, a taqaice yace "Sannu"

'Daga masa Kai tayi tace "Babban Yaya da yanzu na mutu, nide mubar Garin Nan, tsoro nakeji"

Fuskarta yariqe yana Kallan qwayar idonta yace "kidena cewa Zaki mutu, banaso"

Murmushi tayi masa, kafin tace wani abu su Yahya suka qaraso,'yanbiyu suka jata zuwa gida,tafiya suke a hanya gaba d'ayansu suna jajantawa juna akan abinda yafaru

Da daddare kasa bacci yayi, haka ya dinga juyi akan gado hannun sa yana kan mararsa datake masa wani irin mugun ciwo, yana tuno laushin lips din Waheeda saiyaji kamar yaje yaqara😳🙆🏻‍♀�, Sai gab da asuba yasamu bacci ya d'auke shi Bayan ya kwanta rub da ciki, saida ya makara sallar asuba, baida tsarki, saida yayi wanka sannan yayi sallah sakamakon wani irin mafarki da yayi na Waheeda me dadi.

Sai wajan shad'aya
'yanbiyu suka kawo masa abinci, yanaci kuwa yafuto tsakar gida d'aukeda kayansu, koda ace Waheeda batace tanajin tsoron Garin ba, ya zama dole sutafi, bazai juri rashinta atare dashi ba, idan ta mutu a wannan qauyen shi waya kama kenan? 😂🤔

Baba Habu yace "a a, ya naganka da Kaya? Ina zakaje"

Kasa yayi da Kansa yace "baba anmin waya ne a wajan aiki, Ana nemana, shiyasa zamu tafi"

"to Amma tafiya babu shiri Naufal? Meyasa bazaku Bari Sai goben ba?"

Murmushi yayi yace "baba zamu sake dawowa"

Haka yahad'a kan qannansa kowa yahad'a kayansa, suna saka kayansu cikin booth din motar wasu samari suka qaraso wajan Babban Yaya suka bashi wata latter, dubawa yayi sannan yayi murmushi, ya Kalle su yace "inde kayan Ball ne, zan turo muku dashi, harda takalma"

Ihu suka Hau yi kowa yana qara yimasa godia, inna Haajara tacika su da kayaiyakin qauye su manshanu da Kuka, dakuma kindirmo, haka suka tafi cikeda kewar 'yan'uwan su su Yahya.

Washe Garin ranar dasuka dawo daga qauye, Daddy da Ummah da Uncle Usman suna zaune afalo suna kallo, Sa'ad da Sa'eed suka shigo falon kansu aqasa, agaban Ummah suka zauna, uncle Usman yace "to 'yanbiyu mekuke sone Naga Kuna sunkuyar da kanku?"

Sa'eed ya Sosa qeyarsa yace "Uncle Dama... Dama uncle..." saikuma yayi shiru yana zungurin Sa'ad
Chapter 18 · 0% Book details