Sashe 28
Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ransa duk adagule ya kalli mashkur yace "mashkur lokaci yariga yaquremin.... Itama aure zatayi, tayaya za'a fasa dawani ayi Dani? Tayaya zan rabu da wannan nacacciyar yarinyar ummi? Wallahi haushin ta nakeji, idan ta kuskura ta aure ni ko.... Wallahi saina mata filla-filla aranar da aka kawota kuma da niyya"
Mashkur ya kwashe da wata irin dariya sannan yace "Abokina bakada Dama wallahi, kadena wannan tunanin, kasa aranka zaka yarda da qaddara mekyau ko marar kyau, sannan karka manta komai yayi zafi maganin sa Allah, a lokacin daka shiga cikin matsala kadinga tunawa cewa akwai Allah.... Saboda haka yanzu ma shi zamu kaiwa kukan mu, me muke yanzu a qasar? Mushirya gobe mutafi Saudia, daga Nan kawai muwuce England.... "
Sai a lokacin Babban Yaya yasaki wata irin ajiyar zuciya, yace
" nagode Friend"
cikin farinciki suka rungume juna
Washe gari karfe goma a compound tayiwa Babban Yaya, sunyi waya da mashkur zasu had'u a Airport, Waheeda da Yanbiyu ne suka rakoshi har wajan motar dazai shiga, wayar Ummah tana hannun Waheeda, Huzaifa ne ya kirata cikin murna ta d'auka tafara masa magana Sai wani kashe murya take.... Babban Yaya yabude motar zai shiga ya kalleta yace "mahaukaciya..." 🤣
Yanbiyu sunji abinda yace, sunsan cewa akusa yake, danhaka sukai murmushi suka juya ciki
Waheeda ta katse wayar sannan ta Kalle shi tace "Babban Yaya mekace?"
Cikin 6acin rai yace "bansani ba"
Jikinta ne yayi Sanyi, ta qarasa wajan sa tace "nayi laifi ne Babban Yaya? Kayi hakuri...."
Fasa shiga motar yayi, yafuto tareda d'ora hannun sa akan murfin motar, cikin masifa yace "au tambaya tama kike me kikayi? Kullum kina liqewa mutum saikace kaska, kwata kwata baki iya Jan aji ba, to Bari kiji, namiji tsanar mace me naci yake, marar aikin yi kawai..."
Kukane yakama Waheeda, ita tarasa meta masa tun ranar da aka kawo lefen ta yake daure mata fuska,komai tayi saiya dinga Jin haushinta, bata iya haqura ba saida ta rushe da Kuka Sannan tayi cikin gidan da gudu
Tsaki yasaki yanajin haushin zuciyar sa Kuma, Dan me zaisa Waheeda kuka? 🤣Yanzu haka kukan ma ya haddasa mata ciwon Kai, wani tsakin yasake saki, yarufe motar zaibi Bayan ta, domin yabata haquri
"Salamu Alaikum"
Juyawa yayi yaga meyi masa sallama, budurwa ce Babba, wankan tarwad'a, tanada tsayi had'eda jiki, saide babu alamun kyau atare da'ita, hannunta d'aukeda wani flask d'in abinci,Kallan rashin Sani yayi mata, beyi mata magana ba yajuya zaiyi cikin gida
Cikin sauri Tariqo rigarsa tace "Husband baka ganni bane?"
Cak! Yaja ya tsaya a'inda yake, sannan ya Juyo cikin nutsuwa yacire hannunta data riqe masa Riga, ya kalli idonta yace "Dama kece?"
Ummi tayi farrrr da idonta, cikin yanga tace "nice, meyafaru ne Naga kamar kana cikin 6acin rai? To kayi hakuri ga girkina nakawo ma da hannu na nayishi, idan Kaci zakaji dadi"
Cikin tsananin 6acin rai yanunata da hannu yace "Ummi!!!, kidena damuna, kidena shiga cikin rayuwa ta, waike Ana so dole ne? Sau nawa zan fad'a miki Bana ra'ayin ki? Ba girki ba, ko kanki Zaki Bani bazanyi ra'ayin ki ba"
Cikin rashin kunya tace "qarya kake wallahi, Kai d'in wa? Dazaka dinga fadamin baqar magana, cemaka akai ni dinma sonka nake? Inaso na aure ka ne saboda duniya tasan cewa eh Nima na auri mashahurin mutum, Naga alama bakasan darajar mace ba, Amma duk lokacin daka aureni saina koyama yanda ake...... "
Cikin 6acin rai yakai hannu zai wanketa da Mari tareda wata irin tsawa yace"Ummi!!!"
Tsananin tsoro ummi ta tsorata da yana yinsa,jikinta ya d'auki rawa batasan lokacin da flask din hannunta yafad'i qasa ba, jallop rice din ciki ta zube😂
Idanunsa harsun sauya Kala sun koma ja saboda 6acin rai, cikin sauri Hajiya Anty taqaraso wajan su tariqe hannunsa, shigowarta kenan gidan, ta tarar da wannan drama, cikin 6acin rai ta Kalle shi tace "Duka Kuma Naufal....?"
Yanda yaji tafad'i kalmar duka d'in kamar zatayi kuka duk Sai jikinsa yayi Sanyi, Amma sai huci yake, tunda yake ba'a ta6a yimasa rashin kunya kamar yanda ummi tamasa ba yau, Hajiya Anty ta maida Kallan ta wajan Ummi tace "kiyi hakuri, d'auki flask d'inki kitafi"
Ummi ta tsugunna ta d'auka, sannan ta d'ago ta kalli Hajiya Anty sannan tasakar mata tsaki, ta wuce tabar gidan
Babban Yaya yana ganin abinda Ummi tayiwa Hajiya Anty yabi Bayan ta zai damqo ta, Hajiya Anty ganin yabi Bayan ummi tasan tsaf zai lakad'a mata duka, Dan haka cikin sauri ta ruqoshi, tace "karabu da'ita nace"
"Amma Anty... Kina.... Kina ganin abinda tamiki fa..."
Yafad'i maganar a rarrabe cikeda qunan rai
Murmushi tayi tace "naji, karabu da'ita"
Jijjiga Kansa yayi, sannan yashiga motar sa yamata key yabar gidan,wajan Waheedan ma fasa zuwa yayi 🤗
😇😇😇
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama😇: QN
Kwanan su uku a Saudia suna gudanar da addu'ah shida mashkur, gaba d'aya kashe wayoyinsu sukayi, ibada kawai suka sa agaba,Sai akwana na hudun ne sannan suka koma England.
Kwanansu hud'u da komawa England yakira wayar Hajiya Anty, Bayan sun gaisa yace "Anty kiyi hakuri akan abinda yarinyar Nan tamiki, na lura kwata kwata batada kunya...... Sannan duk laifin ku ne dakuka liqa min ita"
Murmushi tayi "son rigima, to kayi hakuri mana watarana zata dena, karka damu babu komai, baka fita wajan aiki bane Naga kiranka da wannan safiyar?"
"Ina gida Anty, yau babu inda zanje, zan zauna agida inyi shara, inyi mopping, inyi wanke wanke, Anty Allah nagaji...." ya qarasa maganar cikin shagwa6a
Murmushi tayi tace "yau Kuma shagwa6ar ce tatashi?, ko Inturo ma Waheeda?" tafad'i hakan tana so Tasha cikinsa ko zataji wata maganar
Murmushi yayi, yasan Sarai da biyu tayi masa wannan maganar, yaganota, cikin dakiya yace "tazo tamin me? Anty wannan yarinyar ai damuwa ce... Nayafe tayi zamanta"
Murmushi tayi tace "to shikkenan, yaushe zaka dawo?"
Yatsina fuska yayi sannan yace "ai kinsan zuwan nawa yana hannun Waheeda.... Idan tayi wani abun to zaku ganni, but nide ara'ayina bazan dawo ba Sai biki"
Dariya tayi tace "Haka Waheedan tazama? Karka yimata sharri" 😃
Sun dad'e suna zance, daga baya sukai sallama.
** *** **
Cikin hawaye yake yiwa Baban nasa bayanin komai, Alhaji Attahir ya Jinjina Kansa cike da 6acin rai, duk abinda d'ansa yakeso Tofa Shima yanaso, wacce irin yarinya ce wannan da zata rusa farincikin d'ansa? Kallan sa yayi yace "ita yarinyar bazata iya hakuri harna dawo daga tafiya ba, insamu iyayenta muyi magana dasu? Yar gidan wacece ne?"
Cikin kuka Didat yace "yarinyar Alhaji Umar Arabo ce"
Alhaji Attahir yace "Nasan Alhaji Umar, ka kwantar hankalinka, zamuje dakai ayi magana, dole a warware wannan maganar auren datace anyi dawani, dakai za'ayi wannan auren, ka kwantar da hankalinka kaji?"
Kakar Didat dake zaune agefe tayi murmushi, ganin mahaifin nasa zai samo masa abinda yake so, haqiqa tana tsananin son Didat, bata son abinda zai shiga tsakanin sa da farincikin sa, tun Bayan rasuwar mahaifiyar sa, itace taci gaba da Kula dashi, shiyasa take jinsa har cikin zuciyar ta
** *** **
Tafiya suke ahankali agefen titi suna hirarsu ta qawaye, Maya ta kalli qawar tata, "gaskiya qawata na gode da ziyara, naji dad'in zuwanki gidanmu"
Waheeda tace "Dama rashin dama ne yasa Bana zuwa ai"
Maya ta kalleta tace "yanaga yanayin ki kamar kina cikin damuwa?"
Ajiyar zuciya tayi "wallahi Maya, Babban Yaya ne, fishi yake Dani, narasa yanda zan masa, ya cika rigima wallahi"😔
Maya tayi wani murmushi Mai d'auke da ma'anoni tace "inyee saikace wani Babynki Babban yayan kike cewa yacika rigima? Meya miki to?"
"tunda akai maganar auren Nan, narasa gane Kansa, kwata kwata baya sakarmin fuska kamar baya, sannan Bahaka yakewa 'yanbiyu ba"
Maya ta riqe hannunta tace "qawata ki kirashi kibashi hakuri, nasan yana jin maganar ki, sannan ki marairaice masa kamar Zaki masa kuka, aikin gane dai, shagwa6a Zaki masa duk ki haukata shi"
Zare hannunta tayi daga cikin na Maya tace "me kike nufi? Waike Dan Allah meyake damunki ne? Saurayina ne dazan dinga masa wannan abun? Maya Babban Yaya fa nace Miki ba Huzaifa ba"
Maya ta yatsina fuska ganin plan d'in Nata bai samu kar6uwa ba tace "toki rabu dashi kawai, ai zai huce ne, yaushe Zaki fara gyaran jiki ne? Biki Sai matsowa yake, Gara fa tun yanzu kifara shan abubuwa Wanda zasu sa kifara tsiyaya, sonake kisa Huzaifa kuka a Daren farkon ku"
Ajiyar zuciya tayi tace "Anty tace gobe zan fara zuwa, kitaho da safe ki sameni a gidan Hajiya Antyn, saina yiwa Huzaifa magana yazo yakaimu gidan, namanta ma ban fada miki ba, Su Daddy sunce muje Asbiti ayi mana text, na jini, kinsan yanzu yanayin rayuwar ya sauya komai Sai ahankali "
Maya ta Jinjina kanta, tafara wani tunani, ta kalli Waheeda tace"hakane Kam, saikaje ka auri me sikila ma baka Sani ba, Gara kuje din Kam, wanne Asbiti zakuje? "
Zuciya d'aya Waheeda tace"na fad'awa Huzaifan de, yacemin tunda gobe zamuje wajan gyaran jiki,jibi Sai muje asbitin, akwai asbitin da ake duba 'Yan gidansu, (Al'islah Hospital) private ne, can nake tunanin zamuje"
Maya tace "to shikkenan, Allah yakaimu goben, saina shigo"
Daga Nan sukai sallama, kowa yatafi gida
** *** **
Washe gari da safe Maya a gidan Hajiya Anty tasamu Waheeda, anan sukayi breakfast sannan Waheeda takira Huzaifa yazo yad'aukesu suka tafi
Maya tana gidan baya, Waheeda da huzaifa suna gaba, Sai kashe mata murya yake suna soyaiya, hankalin Maya yana kan wayarta tana daddannawa, a gidan da Hajiya Anty ta fad'a musu yasauke su, sannan yatafi, gidan suka shiga aka fara yimata gyaran jikin yanda ya kamata, tsawon lokaci suka d'auka ana mata abu d'aya,Bayan angama gyaran jiki matar tabata wasu magungunan na mata, ta zaunar da'ita a gabanta, saida taga ta Shanye sannan,wani irin qyalli Waheeda tafara, gyaran yau ma kenan, ita kanta Maya Kallan ta take tana mamakin yanda tayi kyau, to rana d'aya ma kenan idan kuma aka gama gyaran gaba d'aya Yaya Waheeda zata kasance? 🤔
basu gama da wuri ba Sai wajan yamma, sukayi mata sallama saikuma gobe idan sun dawo