← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy yayi dariya yace "tunda kaga haka ai zancen bazai wuce na neman kudi ba zasu sauya mota, aikinsu kenan, kuje wajan yayanku yabaku, shine me kudi"

Murmushi sukayi, Sa'eed yace "Daddy Bahaka bane, dama gidansu Hassana ne akace muturo akai kudin gaisuwa"

Uncle Usman ya gyara zama yace "a a, babbar magana, kuce abun yazo" 😃

Sake sunkuyar da kansu sukai cikin kunya

Daddy yayi murmushi yace "Kundage de Kuma yanbiyu zaku aura kamar ku,kuje ku kiramin yayanku, ai dashi yakamata kufara magana, shikuma saiya fad'a mana"

Tashi sukai suka nufi wani daki kusa da 'Dakin Babban Yaya, babu komai acikin 'Dakin Sai kayan Ball, dagashi Sai qananun Kaya da ball, yana bugawa shi kadai, zama sukai suna Kallan sa, daina abinda yake yayi, ya dawo kusa dasu ya zauna yace "twins ya akayi ne?"

Sa'eed yace "Babban Yaya mun dade bamuyi Ball bafa"

Kallan sa yayi yace "shine matsalar?"

Sa'ad yace "Babban Yaya wallahi ba'ita bace, gidansu Hassana da Hussaina sunyi magana, mu turo akai gaisuwa, Dan Allah Babban Yaya kacewa su Daddy a saka harda ranar ma gaba daya"

Babban Yaya ya saki murmushi yace "um Um... Ashe aure kukeso shine kuka qi magana?"

Dariya sukayi dukansu, yace "to shikkenan, idan nagama zanyi magana dasu Daddy"

Godia sukayi masa sannan suka fice daga Dakin, yana ganin fitarsu yazube a wajan, yafada duniyar tunani, Sai yaushe ne matsalar sa zatazo qarshe ne? 🤔

Ko awa d'aya bai qaraba yanufi wajan su daddy Bayan yayi wanka yagama shirya wa, Kansa yana qasa, Bayan yagama yimusu bayanin abinda yakawo shi, uncle Usman yace "yanzu Kai haka kaza6awa rayuwar ka? Maryam qanwar 'yanbiyu tayi aure, abar wannan maganar ma, ita mace ce, toga 'yanbiyun suma sunyi magana, Naufal, yakamata ace ka nemawa kanka mafita, zamanka haka bazai iyu ba, musuka fara fad'awa maganar, muka turo su wajanka, munyi tunanin hakan zaisa kaima ka kawo taka Sai ahad'a ayi gaba d'aya, ashe har yanzu kana Nan kakasa tsaida magana d'aya, maganar gaskiya bazai iyu su Sa'eed su Riga ka aure ba, muna so Kai kafara saboda kaine Babba, tayaya zasu auri Yara sukawo su gidan Nan, Yara su dinga gaisheka a matsayin yayan mijinsu suna ganinka babu aure ba?, saboda haka mun yanke shawara, bazamu hanasu Kai gaisuwa ba, Amma babu maganar sa rana, saka rana Sai Bayan bikinka, kaikuma za'a saka ranar ka yanzu, Kai saka rana, sukuma Kai gaisuwa, Bayan bikinka Sai ayi nasu, akwai yarinya me Hankali sunanta Ummi, kama Santa, Nan maqo tanmu take, Bama saikaje ganintaba bare Asamu matsala, kawai za'a saka ranar, tashi katafi "

Tunda Uncle Usman ya fara masa magana yarasa gane Ina yake zaune? Jiyake kamar a mafarki Wai shi za'a had'a da ummi, yarinyar da kowa ya Santa batada kunya, sude burinsu shine yayi aure Amma babu ruwansu da yarinyar ta dace dashi ko bata dace ba, tasa qaddarar kenan kullum idan yazo Nigeria Sai anyi masa maganar aure, Bai iya cemusu komaiba Sai "to Uncle" daga Nan yatashi yanufi d'akinsa yana tafiya yana had'a hanya, domin kuwa wani irin baqi-baqi yake Gani, yana bude kofar d'akinsa yana kokarin shiga har bige goshinsa yake, Amma baidamu ba, abinda yake ji acikin zuciyar sa yafi bige goshin zafi,kulle Dakin yayi yafad'a kan gadon sa, wani irin hawaye me zafi ya silalo daga idanunsa, lokaci daya yaji duk duniyar tafita a ransa
Bashida wata sauran dabara illa ya kar6i ummi a matsayin matarsa, basu bashi Dama yaje ya ganta Bama bare yayi wata dabarar daya saba yarabu da'ita, tabbas yasan Ummi, yarinyar akwai muni ba laifi, ga rashin kunya, jikinta ne kawai me kyau, tsakanin gidansu da gidansu Babban Yaya gida uku ne a tsakani

***

Abu kamar wasa washe gari aka saka ranar Babban Yaya da Ummi ,wata uku kacal,Amma ba'a saka date din Daurin auren ba, Sai ankai lefe,duk wani hidima da akeyi na al'ada Daddy ne dakansa yayi ta

yau su yanbiyu sukai candy Sai abun yahad'u ya zama kamar wani 'Dan qaramin biki ake, har zuwa lokacin Babban Yaya yana d'a kinsa a kwance, duk abinda yake faruwa hajiya Anty ta fad'a masa ta waya saboda taje 'Dakin nasa taji shi a rufe,saide duk text din data masa babu guda d'aya da yayi mata replay

Acan makaranta kuwa, Waheeda saida ta jira su 'yanbiyu suka gama party a school sannan suka taho, yau driver bai d'auko suba, da kansu zasu taho, suna futowa daga get din makarantar, wani matashi me cikar kamala da kyau, gashi 'Dan Gayu, ya doko musu sallama, Ihsan ce ta amsa masa, yajuya yana Kallan Waheeda yace "qanwata idan babu damuwa Dan Allah inaso kibani number ki"

Waheeda ta tuna karonta da Babban Yaya saita qi bashi amsa tajuya masa baya, murmushi yayi yace "haba qanwata, kamar Wanda zan sace ki?"

Intisar tayi murmushi tace "Gaskiya Yayanmu yahanamu kula samari, Amma zamu baka number sa, idan ya amince shikkenan"

Murmushi yayi yace "gaskiya kun birgeni, daga Gani daga gidan tarbiya kuka futo, insha Allah zan nemeshi, yabani Dama indinga zuwa muna gaisawa da qanwata"
Yaqarasa maganar yana Kallan Waheeda, itade ba tace masa komai ba, saboda idan ta tuna Babban Yaya da police station din dataje, da 6atan wayarta, saitaji duk samarin sun fice mata Arai

Number Babban Yaya Intisar ta bashi, sannan suka tafi, duk inda sukabi Sai an Kalle su, kyawawan yanmata su uku, kana ganinsu kasan ba hausawa bane, napep suka Hau yakaisu har 'kofar gida, suna shiga falo suka tarar da Hajiya Anty taci kwalliya, wuyan ta da kunnanta Sai qyallin gold suke, matar ta'iya daukan wanka na fitar Hankali,yar Gayu ce ta qarshe, raba Goro da alawa take, ga Kuma kudi Nan agaban ta dami dami, zama Waheeda tayi akusa da ita, jikinta yana gogar Nata.

Tad'auko alawar guda d'aya tana sakawa a bakinta, sannan tacire hijabin jikinta, dogon gashinta ya baiyana,kwanciya tayi tareda d'ora kanta a cinyar hajiya Anty,sannan tace "Anty kayan me kike rabawa"

Ummah tace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba waheeda, kin sameta tana aiki memakon ki temaka mata, saide kihau cinyarta"

Bakinta ta turo gaba cikin shagwa6a tace "Ummah Anty cefa"

"eh saboda Anty ce saiki kashe mata cinya"

Hajiya Anty tayi murmushi tace "Goron saka ranar Yayanku ne, yau ansaka masa rana,su Sa'eed Kuma ankai musu gaisuwa"

Da Waheeda da 'Yanbiyu lokaci d'aya suka matso kusa da Hajiya Anty sukace "Babban Yaya?"

Hajiya Anty ta d'aga musu Kai, haba ai da gudu Waheeda tayi d'akinsa, tura kofar tayi tashiga ta ganshi a kwance, ya rungume Fillo a qirjinsa, cikin murna ta fad'a Kansa tana sakin ihun murna, yana jin yanda aka fad'o Kansa yasan ba kowane zaiyi masa hakaba Sai ita, yatsina fuska yayi sannan ya tureta daga jikinsa yace "Yaushe zakiyi Hankali ne?"

Cikin farin ciki tace "Babban Yaya, Dan Allah da pink colour da blue, dakuma green wanne ne yafi kyau?"

Cikin mamaki ya daga Kansa ya kalleta batare daya tashi ba, yace "meyafaru?"

Dantsan hannun sa takama ta riqe, tace "sonake kafadamin wanne ne yafi kyau saimu dakko ankon bikinka"

Wani irin baqin ciki ne yakama shi,cire hannunta daga jikinsa yayi,ya maida Kansa fillo cikin damuwa yace "ni banason auren"

Bata lura da yanda yake rabata da jikinsa ba tasake matsawa jikinsa tace "Meyasa Babban Yaya?"

Juyowa yayi yana Kallan ta, yace "Akwai yarinyar danake so"

Cikin farinciki tace "wayyo Allah, Babban Yaya Dan Allah wacece?"

Kallan ta yayi yakasa magana, zuciyar sa ce take zugashi akan yafad'a mata, to Amma tayaya zata dauki maganar?, qalubalen dayake gabansa dangane da fad'a mata wannan maganar ba qarami bane
Waheeda tace "Babban Yaya nikake kallo, wacece yarinyar?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Sunanku d'aya, kamar ku d'aya"

Wani irin fari tayi da idonta tace "Dan Allah Babban Yaya kakaini wajan ta mugaisa, ka nuna mata ni, kafad'a mata nice qanwarka wadda kafi so"

Lumshe idonsa yayi yabud'e, sannan yace "zan kaiki, Amma karki fad'awa kowa wannan maganar, sirri"

Dariya tayi tace "bazan fad'a ba, Babban Yaya kasan me? Wallahi inaso kayi aure, sonake Naga matarka ta haihu, muga dawa yaran zasuyi kama"

Tashi yayi zaune ya kalleta yace "ke har farinciki kike da bikin ne?"

Tace "sosai ma, wallahi inaso kayi aure"

Cikin wata irin gigitacciyar tsawa, wadda bata ta6ajin yayi mata irinta ba yace "tashi kibarmin dakina, tunda farinciki kike da aure na"

Tace "Babban......"
kafin ta qarasa yatashi tsaye cikin fishi kamar zai rufeta da duka, tana ganin haka tatashi tsaye, jikinta yafara tsuma saboda tsoro, qwalla ce tataru a idonta, tafuto daga Dakin cikin sanyin jiki

Ayi hakuri da wannan ba yawa, muna tayaka murna Babban Yaya 😂

Bazanyi zagi ba, Amma duk wacce ta karanta batare data biyaba, nabarta itada mahaliccinta, saboda babu yafiyata aciki

Amnah
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama😇: Tana fita daga d'akin ya zauna akan gadonsa tareda dafe Kansa da hannun sa🤦🏻‍♂�
Ita farinciki ma take, meyasa bazata fahimceshi ba? Yace sunansu d'aya, yace suna kama, tayaya zai futo fili yafad'a mata gaskiya? Tayaya zata fahimce shi? Mezai fad'awa iyayensu idan suka ji daga inda maganar tafuto?

Kansa ne ya Sara, yazube akan gadon yana fadin "hasbunallahu wa ni'imal Wakeel"
Bayajin zai iya rayuwa batare da Waheeda ba, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, ya cusa Kansa cikin fillo yana kuka babu me lallashi kamar ba Babban Yaya ba 😂

Tana barin 'Dakin nasa, d'akinsu tashige, ta zauna agefen gado tana Kallan p.o.p din 'Dakin,
'yanbiyu ne suka shigo, intisar tace "kekuma lafiya kikayi wani iri kamar marar lafiya?"

Cikin damuwa tace "Babban Yaya ne"

Ihsan da intisar sukasa dariya, Ihsan tace "to me yamiki Kuma?, kema da rawar Kai daga jin ansa masa rana kika d'iba da gudu kikaje"

Kallan su tayi cikin damuw tace "Wai baya son auren ne"

Inti tace "to yanzu ke menene naki aciki? Hanawa zakiyi? Mema za'ai da wannan Ummin, ni wallahi Bana sonta, kullum kaganta tana magana da maza"

Ihsan tace "wallahi kuwa, inajin su Daddy basu Sani bane shiyasa, nifa shiyasa banyi murna ba danaji ance itace, Amma Waheeda uwar rawar Kai harda tafiya wajan sa da gudu, dama yasani yamiki shegen duka"
Chapter 19 · 0% Book details