← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 48

Sashe 26

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle Usman ya qarasa Dakin Daddy Bayan sun gama abinda zasuyi, Uncle Usman yace "Yaya yakamata fa Yaron Nan Huzaifa idan da gaske yake yaturo,inda zai iyu da anhada bikin Waheeda Dana Naufal"

Daddy yace "Eh da munji dadin hakan gaskiya, Bari zanyi magana da mahaifin sa, tunda Naga yanzu ta bashi Dama yana zuwa zance a koda yaushe nasan sun dedeta, zanyi magana da mahaifin sa, Saisuzo ayi magana kawai"

Kamar yanda suka yanke wannan shawarar kuwa, haka akayi, cikin satin iyayen Huzaifa suka zo neman aure, Daddy da Uncle Usman da baba Habu sukace sun basu 😥🤗

Waheeda dataji wannan labarin bata damu ba, asali ma murna taitayi cikin ranta, saboda har aqasan ranta tanajin soyaiyar Huzaifa, tana sonsa sosai, idan ta zauna ta dinga tunanin sa kenan, shiyasa tadauki zuciyarta gaba daya ta damqa ta ahannunsa

** *** **

A kwatuna ne a shirye daya kan daya guda goma Sha biyu masu launin brown
Minister ne a tsaye yana kokarin Kiran waya, tsaki yayi ya zauna tare da fadin "inaga babu network ne, tun dazu nake gwadawa Amma taqi tafiya, ai Gara afada musu lefe yahadu, yaushe suke ganin yadace akawo musu?"

Hajiya Babba mahaifiyar Huzaifa, tajuya ta kalli huzaifa dayake Sanye cikin kayan shan iska, yana danna laptop din gabansa, tasake juyawa ta kalli minister tace" yanzu Alhaji baka ganin wannan kayan sunyi yawa? Ina laifin ma a kwatuna hudu ko biyar? "

Kallan ta yayi yace" kinsan me kike fada kuwa? Kinsan matsayina awannan jihar kuwa? A kwatuna shabiyu ai sunyi kadan hajiya, ko bakisan gidan da za'a Kai bane? "

Cikin 6acin rai tace" nasani mana Alhaji, ba gidan buzayen Nan bane? Ni kwata kwata yarinyar Nan bata minba, kana ganinta daga ita har yan'uwan Nata kasan irin sadaka yallar Nan ne..., duk abi a rabaka da danka ta hanyar asiri "☹️😔

Huzaifa ya kalleta yace" Momy.... Ni inason Waheeda, Kuma gaskiya bazan iya barinta ba "

Minister yayi Dariya yace"to kinji, Kuma nikaina nasan idan Huzaifa ya auri yarinyar Nan zan samu jikoki kyawawa... Kisawa yaro Albarka kawai acikin auren sa"

Hajiya Babba takama jijjiga kafarta, ranta in yayi dubu ta ya6abaci.... Daga Dan har uban haka suka qyaleta, minister yaci gaba da neman number Daddy

** *** **

Washe gari karfe Tara nasafe, a Nigerian tayi masa,Kai tsaye wajan shopping yaje yasiyo panties da Bra, lokacin dazai za6a tunani yake wanne size zai d'auka mata? Shide bai ta6a ganinta azahiri ba,bare yayi hasashe ya d'auka mata Kuma pant da Brezia babu size din wadda yasani saina Waheeda, danhaka batare da tunanin komai ba ya 'Dauko mata daidai size din Waheeda 🙆🏻‍♀�

kasancewar sa mutum
na mutane bai samu zuwa gidan Hajiya Anty ba, Sai karfe goma Sha shad'aya, Kai tsaye gidan yashiga, kasancewar tana takura masa da waya yazo yaga lefe, yasan cewa idan ya wuce gidansu baizo yaga lefe ba, to zata dinga yimasa Mita ne, shiyasa Kai tsaye ya wuce gidan Nata, maigadi Sai washe masa haqora yake yana kwasar gaisuwa, saida yayi masa yayyafin kudi sannan yabarshi yasamu ganawa da Antyn nasa.

Gabansa tacika da kayan break fast, Sai Nan Nan take dashi kamar zata saka shi ajikinta, waya yake amsa wa cikin farinciki, yau yana jin wannan zuwan nasa na musanman ne, tunda har yazo Nigeria dan rad'in Kansa ba fitinar Waheeda ce ta kawo shi ba 😃

Yana ajiye waya, wata wayar tasake shigo wa, Kuma gaba d'ayansu masoyansa ne, tun yana amsawa harya fara gajiya, Amma duk da haka bai fasa d'aukar wayar masoyan nasa ba, saida Hajiya Anty taga abin nasa Bana qare bane, kawai saita kwashe wayoyin ta kashe su, sannan tafara bashi break fast din da kanta, saida yaci yaqoshi sannan tajashi zuwa wani d'aki, photunan Waheeda ne birjik acikin Dakin, saikuma na Babban Yaya dasu Sa'eed, saikuma na dukansu yaran gidan dasuka had'u suka d'auka tace "toga kayan lefenka..."

A kwatunan ya kalla guda ashirin da hud'u, ya kawarda da Kansa yace "nagani, sunyi"

Cikin mamaki ta Kalle shi tace "tayaya kasan sunyi Bayan ko bud'ewa bakayi ka Gani ba?"

Kallan inners d'in daya kawo tayi tace "sannan wannan kayan daka siyo sunyi wa ummi yawa, na ganta ai rannan, wannan bra din tamata yawa, bansan de pant d'inba, kaida nace ka tambayeta size dinta meyasa zaka siyo?"

"ai itace tace haka ne size din Nata" ya qarasa maganar cikin d'aure fuska

Hajiya Anty tace "to shikkenan, zanyi magana da ummanku, Sai muji ranar daza'a saka akai musu kayan"

Yana jin ta d'auko hanyar maganar auren sa, ransa yaqara 6aci, babu shiri yayi mata sallama yabar gidan yanufi gidansu.

Tun abakin get mutane suka masa cincirundo, Sa'ad da Sa'eed suka tar6eshi suka qaraso gidan, Ummah bakinta Qin rufuwa yayi, babu Wanda yayi tunanin zuwansa, Sai gashi ya basu mamaki yazo, Ummah ta Kalle shi duk farinciki ya cikata, ganin yanda yasaki ransa tasan cewa may be ya yarda da auran ne tace " 'Dana,me zakaci? Me kakeso nayi ma?"

Kallan ta yayi,yayi murmushi dimple d'insa ya lotsa, su yanbiyu da Waheeda Sai dariya suke musu shida Ummah, ganin yanda duk ta rikice ganin Babban Yaya kamar sudin ba sauran yaranta bane, kafin Babban Yaya yayi magana Daddy ya kalleta yace"haba Hajiya,Naga alama yakamata nadinga tuna miki cewa Naufal bashine auta ba "

Waheeda ta turo Dan qaramin bakinta gaba tace"Bayan Ummah tafi sonshi Dani"

Ummah ta kalli Waheeda ta kalli Babban Yaya tace "rabu dasu Dana, me zakaci nadafa ma dakaina? Karka damu da surutun su Dama can kishi suke dakai"

Fuskarta yakama yariqe yace "Ummah tah ta kaina, inason ki Ummah, naci abinci a gidan Anty, can nafara zuwa Naga Kaya, karki damu kanki, banajin yunwa, anjima de keda kanki Zaki Bani abinci da wannan hannun naki" ya qarasa maganar yana kissing hannunta, Ummah ta kalli Daddy alamun bata gamsu da maganar da Babban Yaya yafad'a mata ba, Daddy yace "yace miki ya qoshi hajiya,ai yana Nan a gidan babu inda zaije, anjima saiki bashi abincin"

Sai a sannan Hankalinta ya kwanta, ta kalli Naufal dayake Kallan ta cikin murmushi tace "to shikkenan, kaje daki ka kwanta ka huta, Kuma ka kashe wayoyinka kajiko"

Yace "to Ummah nah" daga Nan yatashi yayi dakinsa, Waheeda ta kalli brief case dinsa daya manta bai tafi da'ita ba, tasan Kuma kudi ne aciki, idanuwanta Tajuya, tana fatan ace yabata ko 50k ne, cikin sauri ta dauki jakar tabi bayansa

Tana shiga 'Dakin ta ganshi yana kokarin cire Kambos d'in kafarsa, Kallan ta yayi ba tare daya Dena abinda yake ba, cikin murna dajin dadin ganinsa tayi saurin qarasa wa wajan sa ta ajiye Brief case din akusa dashi tace "Babban Yaya ga kud'in ka" 😃

Murmushi yayi, ya kalleta yace "kud'i na kuma? Waya fad'a miki kud'i ne aciki?"

Hannun sa takama tacire daga kan takalmin nasa dayake so yacire, ta qarasa cire masa takalmin kamar wani mijinta, sannan tacire masa safar tana cusata cikin takalmin, takama dogayen yatsun kafarsa masu laushi tanaja ahankali sannan tace "ai nasan kudi ne aciki, Dan Allah Babban Yaya ka temaka kabani kudi ko dubu hamsin ne"

Ba tareda tunanin komai ba yace "bude ki d'auka"

Kafarsa tasaki tabud'e jakar, da daloli tayi tozali, cikin mamaki ta d'ago ta Kalle shi tace "Kai kai Babban Yaya ashe kudin ne aciki? Allah jinake ba kudi bane, kawai fad'a nayi"

tafad'i hakan tana rufe jakar, sannan tatashi Takoma kan gadon ta zauna kusa dashi

Babban Yaya ya kalleta yace "ki d'auka duka nabaki"

Cikin mamaki tace "me? Wai kudin?"

Yace "Emana, kid'auka nabaki"

Kanta ne ya d'aure tace "Babban Yaya, daloli ne fa aciki, me zanyi dasu?"

Juyowa yayi yana fuskantar ta, yace "tome kike so? Idan kud'in kike so kitafi dashi, saiki saka cikin account dinki"

Murmushi tayi, dimple dinta yafuto kamar nasa tace "Babban Yaya kana magana kamar ranka a6ace, please kasaki ranka mana"

Murmushi ne ya qwace masa ba tareda shirya ba, yace "naji, tashi kibani waje, Ummah nah tace na kwanta nahuta"

Bakinta ta turo gaba, cikin shagwa6a tace "Babban Yaya Dan Allah mu 'Dauko anko? Wallahi Dama kud'in danace inaso d'in sonake naje kasuwa mu 'Dauko anko"

Dariya ce ta kamashi yace "kuma anko da dubu Hamsin?Bari kiji, babu wani anko da zakuyi, tunda bason auren nake ba, Kuma ta shafeku"

Tace "Dan Allah Babban Yaya kaji, wallahi muna so, Dan Allah muyi? To wai Kai meyasa baka son auren?"

Cikin damuwa yace "nafad'a miki Bana burin zama da wadda banaso, karki sake min wannan tambayar, Sai me Kuma kike so Bayan wannan?"

Lallausan Hannun sa takama tariqe cikin Nata, Kallan ta yayi cikeda mamaki ya kasa magana haka Kuma ya kasa qwace hannun sa, cikin nutsuwa tafara yimasa magana tace"nikam ai nagama samun abinda nakeso a rayuwa Babban Yaya, iyayena suna sona, Babban Yayanmu yana sona, sannan Huzaifa yana sona, Bana tunanin komai akansa, nasan ko Bayan munyi aure zai riqeni Amana kamar Babban Yayanah, saide Kuma naso ace nasamu me kama dakai Babban Yaya"

Gabansa ne yake Dukan Tara Tara, tunda tafara yimasa wannan maganar, kwata kwata yafita haiyacinsa, zuciyar sa ce take zigashi akan yafad'a mata komai, karyayi wasa da damar sa, karya Bari abinda yadad'e yanaso yakufce masa

Cikin sauri kamar Wanda aka mintsineshi yace "koda nine....?"

Kallan idanunsa tayi, cikin rashin fahimta tace "kamarya?"

Shima Kallan qwayar idonnata yayi yace "Zaki iya auren me kama Dani, meyasa ni bazaki aure niba....?"

Kuyi hakuri Dan Allah 🙏🏻🙏🏻
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama😇: SM

BB

Cikin sauri ta d'ago ta Kalle shi, tsananin mamakin abinda yayan Nata yafad'a ne yasa takasa rufe bakinta, gabanta yafara fad'uwa ganin yanda fuskarsa ta nuna kamar da gaske yake, wata zuciyar tace da ita ke mahaukaciya ce? Tayaya hakan zata faru tsakanin ku?yayanki uwa d'aya uba d'aya tayaya?
Dariya ta kwashe da'ita tace "Babban Yaya aure Kuma? Tayaya? Tayaya zan aure ka? Please Mekake so kace? Nasan inajin sonka acikin raina fiyeda yanda nake jin huzaifa acikin zuciyata, saboda Babban Yaya ubane, Kuma ba'a sauya uba,shi kuwa Miji Ana sauya shi"

Kansane yasara har saida yariqe goshinsa, lokaci d'aya ya dawo cikin haiyacinsa, yatuna irin kato6arar da yayi, cikin sauri yace "lokaci ya quremin, Sorry....kuje kuyi ankon tunda Kuna so, tashi kije"
Chapter 26 · 0% Book details