← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 48

Sashe 37

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummah tayi murmushi me ciwo, duk da yafad'a mata abinda zaisa taji dad'i akan maganar mashkur da Ihsan, hakan baiyi tasiri a ranta ba, tafi damuwa da batun Waheeda, taga alama Waheeda bazata sauya ba, Naufal yadad'e baiyi aure ba, yana buqatar kulawar matarsa, inbanda itan ce ta sameshi ta tabbatar idan wata ya aura da tuni yafara kula wasu yanmatan,ajiyar zuciya tayi tace "to Allah ya tabbatar da alkhairi, Son kaje kakaiwa Waheeda takardar ta...."

Cikin sauri ya d'ago ya kalleta yakasa magana, beyi tunanin wannan maganar daga bakin Ummah ba, haushin Kansa yaji, daya Sani be fada mata laifin Waheeda ba, cikin sauri yace "Ummah Dan Allah kiyi haqurrr....."
Hannu ta daga masa✋� tace "kaje kayi abinda nace kawai"

Beqara ce mata komai ba yafice daga gidan, driving yake Amma baya tareda nutsuwa, tayaya ummah zatace yaje yasaki Waheeda? Ko batasan cewa sakin Waheeda daidai yake da sakin zuciyar sa ba?Anya kwa Ummah tasan irin wahalar dayasha akan Waheeda?

Har yazo gidan yarasa abinda zai aikata takameme, falon yashigo anan ya ganta zaune kan kujera tana share hawaye, wucewa yayi d'akinsa, ya kwanta akan gado tareda fad'awa cikin duniyar tunani, wani tunani ne ya fad'o cikin ransa, cikin sauri yatashi yanemi paper da biro yayi rubutu aciki, ya ninke takardar sannan yafuto daga d'akin, Kai tsaye wajan ta ya nufa, yad'aure fuskarsa yace "idan ban manta ba, last time kince min in temaka in sakeki ko?"

Cikin sauri ta Kalle shi takasa magana, ya kalli qwayar idonta tayi jajir da alama Tasha kuka, cikin kuka tace "Bana baka haquri ba?"

Dariya ce taso kamashi, Amma sai yayi fuska yace "lokaci yaqure Waheeda, akwai wadda zatamin abinda narasa awajanki, har abada bazata iya neman saki awajena ba, saboda tana amfani da ilmin ta, ga takardar ki Nan" ya ajiye mata takardar yajuya zai fita

Ihu tasaka tace "wallahi ban saku ba, babu wadda zaka aura, wallahi bazan bud'e wannan takardar ba garama kazo ka d'auke abarka, Allah ban saku ba...." kuka take sosai tana fad'a masa hakan

Juyowa yayi ya kalleta yace "to idan kin gama kukan ki kulle min gidan,kitafi gidanku, Nima natafi wajan masoya yi ta"

Yana fad'ar haka yafice daga falon yanata dariya, be koma gidan Ummah ba, Kai tsaye gidan Hajiya Anty ya wuce

** *** **

Cikin kuka takira Uncle Usman, yana zaune a office d'in Daddy yayi tunanin Intisar ce saboda number ta yagani, d'auka yayi tareda sallama, saiyaji shiru da alama kuka ake, zamansa ya gyara yace "Intisar meyake faruwa? Lafiya kike kuka?"

Cikin shashshekar kuka tace "Ba inti bace.... Wa... Wahee.... Waheeda ce, Uncle Babban Yaya ne yasakeni, gashinan yabani takarda ta...."

Uncle Usman yatashi tsaye cikin tashin Hankali yace "innalillahi wa inna ilaihirraji'un...., innalillahi wa inna ilaihirraji'un....,kina Ina yanzun?"

"Ina gidansa" cewar Waheeda cikin Jan zuciya

Uncle yace "Kije gidan gamu Nan zuwa"

Daddy ya Kalleshi yace "meyake faruwa?"

Cikin damuwa uncle Usman yace "Wai Naufal ne yasake ta"

Gaban Daddy yafad'i, yace "what?! muje gidan, bari in kirashi, muje muje da sauri"

Cikin hanzari suka fita ko office d'in basu rufeba

Suna hanya Uncle Usman yakira Babban Yaya, yana d'auka ko amsa sallamarsa baiyi ba yafara magana cikin fad'a "ashe bakada Hankali?" 😂🙆🏻‍♀�

Babban Yaya dayake kwance a cinyar Hajiya Anty yace yatashi da sauri yace "Innalillah.... Uncle me nayi?"

Cikin fad'a Uncle Usman yace "nikake tambaya me kayi? To duk abinda kake kabari kazo gidanku ka sameni yanzu yanzun Nan"

Babban Yaya yayi shiru bece komai ba, Uncle Usman yakashe waya, Daddy yace "dabaka kirashi ba Usman, na tabbatar laifi tayi masa shiyasa yakawo qarshan Zaman nasu, shiyasa Nima ban kirashi ba, koma menene muje gidan zamuji komai ai"

Uncle Usman yayi shiru Sai hura hanci yake,tunanin irin yanda zai 6atawa Babban Yaya rai yake, tayaya za'ai yasaki yarinya yamaidata qaramar bazawara?

Babban Yaya yamiqe tsaye yace "Anty zanje gida, uncle yana nemana, da alama nayi masa laifi bansani ba"

Cikin damuwa Anty ta d'auki wayarta tace "A a, me zakayi wa Uncle d'inka? Kaide kayi tunani me kayi masa?, kokuma inkirashi? "

Kwata kwata Babban Yaya ya manta da batun Waheeda, asalima tunani yake irin dad'in da zaiji idan yakoma gidan, saboda yasan idan ta bud'e takardar daya bata taga abinda yake ciki zataji dad'i Kuma yau zasuyi kwanan farinciki, saboda haka baya tunanin wannan Kiran yanada alaqa da Waheeda

Girgiza Kansa yayi yace "karki kirashi, nasan banyi masa komai ba, Bari inje kawai"

Tashi tayi tace "saide mutafi, muje gidan kawai"

Futowa sukai dukansu, suka tafi gidan Ummah, suna zuwa shida Hajiya Anty sukaga kowa a zaune, Daddy, Uncle, Ummah, dasu Sa'eed tareda yanbiyu, Kowa jiran zuwan Waheeda yake

Babban Yaya yazauna aqasa tareda gaida iyayen nasa, Daddy ne kawai ya amsa, Amma uncle Usman kawarda Kansa Gefe yayi, mamaki yasake kama Babban Yaya, meya aikata haka ne?

'Dago Kansa yayi ya Kalle shi yace "Uncle Gani, meyake faruwa ne?"

Cikin 6acin rai yace "abinda kayi ka kyauta kenan? Harme Waheeda zata Maka kasake ta?"

Zaro ido Hajiya Anty dasu Sa'eed sukayi, yanbiyu kuwa har sun fara kuka, Sai yanzu ne suka San dalilin taruwar iyayen nasu

Babban Yaya d'ago Kansa yace "Uncle wallahi ni ban...."

Katseshi yayi batare da yaji abinda zaice ba "babu abinda zaka fadamin"

Yanbiyu ne suka tashi zasu wuce d'akinsu ganin yanda ran iyayen nasu ya6aci, kuma basa masa fad'a agaban su, Amma yau Idonsu ya rufe da masifa harsun fara yimasa

Ummah tace "Alhaji Usman ninace yasake ta saboda iskancin Waheeda yayi yawa"

Uncle Usman yace "kuma saiya saketa? Yanzu kamar shi idan akace yafad'a wuta saiya fad'a?"

Kafin Ummah tayi magana saiga Waheeda tashigo gidan hannunta aka, tana runtuma ihun kuka, ita kuka yanbiyu kuka, su Sa'ad jikinsu duk yayi Sanyi qalau

Waheeda tana zuwa ta fad'a jikin Hajiya Anty tana kuka,kwata kwata bata lura da Babban Yaya dayake falon ba, idonta ya rufe take fad'in"Anty Babban Yaya yasake ni, wallahi Ina sonsa, Allah bazan dawo gidaba "

Hajiya Anty ta goge Hawayen daya zubo idonta tace" kiyi hakuri, wallahi saiya maidake d'akin ki "

Babban Yaya ya shafa sumar Kansa tareda dafe Kansa 🤦🏻‍♂�, Sai yaushe ne Waheeda zatayi Hankali? 🤔

Daddy ya kalli Babban Yaya yace"Naufal, kar6o min takardar "

Babu musu ya qarasa wajan Waheeda yazare takardar daga hannunta, Hajiya Anty tazabga masa wata irin harara, bece da'ita komai ba Sai qeyarsa daga Sosa, ya ninke takardar yariqe ahannunsa yaqi basu, saboda yana kunyar suga abinda ya rubuta a takardar

Uncle Usman yace"kabamu takarda akace malam, kariga kayi abinda kaga yadace ai saika bamu takardar muga saki nawane "

Babu musu Babban Yaya yabashi takardar, saboda bazai iya jayaiya dashi ba

Uncle Usman ya bud'e takardar ya karanta abinda yake ciki, Gani yayi anyi rubutu da Babban baqi cewa I LOVE YOU SO MUCH BABY WAHEEDA

Tsaki yasaki, yayi wata irin ajiyar zuciya yace "af..., Alhaji Allah ya shiryi yarinyar Nan, duk ta d'aga mana Hankali"

Daddy ya kar6a Shima ya karanta, ya jijjiga Kansa, sannan ya kalli Uncle Usman yace "muje Alhaji Usman"

Hajiya Anty tabisu da kallo, ta janye Waheeda daga jikinta tatashi ta d'auki takardar, a fili ta karanta abinda yake ciki tace "I LOVE YOU SO MUCH BABY WAHEEDA"

Su Sa'ad ma sukai murmushi suka koma d'akinsu, yanbiyu kuwa Waheeda suka kalla, haushi yakamasu kamar su daketa, tasa sunyi asarar Hawayen su a banza 😂

Waheeda ta d'ago da sauri ta kalli Babban Yaya, taga yana mata wani irin Kallan soyaiya ko kunyar su Ummah bayaji, wata irin matsanan ciyar kunya ce ta kamata, tatashi tayi d'akin Ummah da gudu tana rufe idonta da tafin hannun ta

Dariya su Anty sukayi mata tareda yanbiyu.😃

Ganin hankalin su Ummah baya kansa yasa ya shafa sumar Kansa,sannan yabi Bayan Waheeda Dakin Ummah

Yana shiga 'Dakin ta d'ago kanta ta Kalle shi, cikin sauri tatashi ta fad'a qirjinsa ta rungume shi, tareda sakin kukan shagwa6a

Sake rungume ta yayi sosai, yafara magana qasa-qasa cikin rad'a ita kad'ai ce zata Iya jin abinda yake fad'a

Sunkuyowa yayi da Kansa, dede Setin kunnan ta yace "kiyi shiru mana, menene abun kukan?"

Kukan shagwa6a tasake sakar masa tace "uhm... Uhm..." tareda Dukan faffad'an qirjinsa ahankali

Murmushi yayi yasake rage murya yace "nine ko?, nine nayi Miki laifi ko?"

Kasa d'ago kanta ta Kalle shi tayi, tanata mamakin sa Dama Babban Yaya ya'iya magana haka ahankali irinta masoya? 🤔Kawai d'aga masa Kai tayi, takasa had'a ido dashi

Cikin sigar lallashi Yace "to kiyi haquri... Bazan sakeba kinji?"

Sake d'aga masa Kai tayi,bata yarda sun had'a ido ba

yace "kin haqura?"

Yanzu ma sake d'aga kan tayi 😂

Murmushi yayi yace "kiyi magana mana"

Ahankali ta motsa lips d'inta, cikin sigar shagwa6a tace "nifa naqura, ni bakamin komai ba"

Tunda tafara magana ya zubawa lips d'inta ido yana kallo, ahankali yasaka hannun sa biyu yariqo fuskarta, yahad'e bakinsu waje d'aya, ahankali yafara tsotsar lips d'inta, wannan Karon wani irin dad'i Waheeda taji, ahankali ta Lumshe idonta tana kar6ar saqon, kusan minti biyar yad'auka yana kissing d'inta, ahankali yacire bakinsa daga Naga, ya kalli qwayar idonta, cikin muryar rad'a yace "your turn..."

Wata irin kunya ce takama Waheeda, mamaki yagama kashe ta kamar ba Babban Yaya ba, tunani tafara kode ya manta acikin d'akin Ummah suke? 🤔
Babu yanda ta iya haka takama lips d'insa na qasa tafara Sha ahankali, wani irin dad'i Babban Yaya yaji, ahankali yasake rungume ta yana sakar mata wani irin numfashi, tun yana haquri yanajin yanda take tsotsar lips d'insa harya kasa haquri ya qwace lips dinsa, tareda kama Nata yanasha cikin fitar haiyaci

Kwata kwata mutanan falon sun manta dasu, Ummah ta kalli Hajiya Anty tace "Antynsu Bari inje toilet in dawo...." 🙆🏻‍♀�

Zuciyarta d'aya takama handle d'in 'Dakin tabud'e, a tsaye ta gansu cikin wannan hali, cikin sauri taja musu kofar tarufe gabanta yana fad'uwa 🙊

✍�
1/28/22, 20:52 - Ummi Tandama😇: JH

Qaran rufe qofar kawai Waheeda taji, tayi tunanin zai daina abinda yake, Amma saitaga yaqi daina wa, cikin sauri ta qwace bakinta, Kallan ta yake da idanunsa dasuka fara canjawa,duk jikinsa yafara mutuwa, Waheeda ta Kalle shi cikin tsoro tace "kamar qaran rufe kofar nanfa naji, waye yashigo?"

Kafad'a ya d'aga yace "Ina zan Sani? Ni banji Bama"
Chapter 37 · 0% Book details