← Book details Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 48

Sashe 29

Babban Yaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ne kawai yakawo su gida lafiya, domin kuwa Huzaifa yana ganin irin gyaran da akayi Waheeda saiya susuce bashida aiki saide yajuya ya kalleta, yana driving yana Kallan ta, Maya ta godewa Allah data ganta a kofar gidansu sunzo lafiya, tana futowa daga motar ta leqasu ta window tace "to wallahi ango kakula da qawata sosai, nide na godewa Allah tunda ankawoni gida lafiya"

Dariya huzaifa yayi ya shafa sumar Kansa, yasan Sarai taga halin daya shiga ne shiyasa tayi masa wannan maganar, Waheeda ma tayi mata murmushi tace "to Sai munyi waya qawata, gobe karki shirya da wuri, saida yamma zamuje, saboda da safe, Asbiti zamuje"

Maya tace "to shikkenan qawata, Allah yakaimu, kikula mana da angon namu"
Ta qarasa maganar cikin tsokana

Huzaifa yaja motar suka tafi, har zuwa lokacin Maya tana tsaye a'inda suka sauketa, saida taga sunbar layin gaba daya,memakon tashiga gidansu sai ta tare adedeta tashiga,tayi masa kwatance sukad'au wata hanyar

** *** **

Tafiya suke cikeda nishadi, kana ganinsu kasan suna cikin tsantsar farinciki, qamshin turaren sa yahad'u da Nata ga Kuma sanyin esi Sai abun yaqara bada armashi
Kallan sa tayi "Bae kadinga sauri muje mana, kana driving kamar baka so"

Kallan ta yayi "so kike nayi sauri Dan muje asbitin mugama da wuri kitafi kibarni ko?"

Murmushi tayi batare da tace komai ba, yasake Kallan ta yace "inason murmushinki Waheeda, yana birgeni, musanman idan Naga wannan dimple din...."

Kallan sa tayi "da gaske? Aikuwa koda yaushe zan dinga yima ka shi, saboda inci gaba da birgeka a koda yaushe, Dan banasan wata Rana kaga wata yarinyar itama ta birgeka"

Kafad'a ya d'aga yace "ai Bana tunanin akwai yarinyar dazata birgeni Bayan ke Waheeda, nifa banga amfanin zuwa wannan text din namu ba, saboda nasan kede lafiyarki kalau, Kuma Nima haka,idan kinada wata cuta ma ai saide in nine nasaka miki, tunda nine nabaki jini batare da angwada jinin nawa ba "

Cikin rashin damuwa tace"dansu Daddy sun matsa ne ai, Amma yanda nake jin ka acikin zuciyata ko wacce irin cuta ce dakai, zan iya zama dakai Bae"

Murmushi yayi ba tareda yace mata komai ba, suna qarasa wa asbitin sukayi wa nurse bayani,dayake tasan Huzaifa tun tuni, Nan asbitin suke zuwa duka family d'insu, cikin qanqanin lokaci aka d'auki jininsu aka basu wajan zama

Basuyi awa d'aya ba, doctor yakirasu zuwa office d'insa, zama sukai ya Kalle su yayi murmushi yace "Huzaifa kace ankusa angoncewa"

Murmushi Huzaifa yayi, "Eh wallahi Doctor, ga madam Nan"

Yace "To Allah yasanya alkhairi, Allah yabaku zuri'ah Dayyiba"

Ahankali Waheeda dake wasa da yatsun hannunta tace "Amin"

Takarda ya miqawa Huzaifa yace "toga result d'inka, Congratulations, baka d'aukeda kowacce irin cuta...."😃

Huzaifa ya kar6a yana fadin "to Alhamdulillah"

Kallan ta Doctor yayi yace "Waheeda"

'Dagowa tayi ta Kalle shi sannan tace "Na'am"

Yayi ajiyar zuciya yace "Waheeda duk abinda kikaga yasamu Bawa, to anaso ya yarda da qaddarar sa, ita cuta ba mutuwa bace, sannan idan kin yarda da shawarwarin dazan baki Zaki zauna lafiya, sannan Zaki rayu kamar kowa idan nad'oraki akan magani,kuma....."

"dan Allah dakata Doctor Mahmud, mekakeso kace ne?"

Cewar huzaifa daya dakatar da doctor

Doctor ya kalli idon Waheeda da yayi tsilli-tsilli tana Kallan su duka su biyun, sannan yace "Waheeda kiyi hakuri, Amma abunda bincikenmu ya nuna shine kina d'aukeda qwayar cuta me karya garkuwar jiki"

Lokaci d'aya, Waheeda da Huzaifa suka miqe tsaye

Huzaifa yace "What...? HIV fa doctor, tayaya?"

Gaban Waheeda yayanke yafad'i, tasaka hannu tadafe qirjinta, kanta take girgizawa kwata kwata takasa magana, lokaci d'aya jiri yad'ebeta tazube qasa sumanmiya "

Cikin sauri Huzaifa yabita, jijjigata yafara yi, yana fad'in" Waheeda!! Waheeda kitashi Dan Allah!! "

Office d'in aka turo, wata matashiyar budurwa tashigo, taci Gayu iya Gayu, tana ganin Huzaifa tace"Yaya Huzaifa lafiya Kuma? Meyasame ta?"

Huzaifa ya kalleta baice mata komai ba yasaka hannu ya d'auki Waheeda cancak, yafice daga office d'in

Yana fita matashiyar budurwar ta kalli doctor tace"meyake faruwa ne doctor?"

Kai tsaye yace "ta tsorata ne sakamakon gwajin da muka mata, muka Gano tana d'aukeda cutar qanjamau,but ni banga abun suma ba, kowanne Bawa da irin qaddararsa,Kuma ba lalle saika yi iskanci ne zaka sameta ba, akwai hanyo yi dayawa, wasu a wajan mahaifiyar su suke dauka, wasu ta hanyar hada jini Dame irin cutar, kokuma ayima allura da sirinjin Wanda yake d'aukeda cutar, kokuma sex, ko amfani da wani qarfe kamar su kibiya, to gashi ita tun kafin ma nafada mata magungunan daya kamata ta dinga Sha harta sume"

Cikin razani budurwar tace "mene? Wallahi saina fad'awa Hajiya, Kuma akan me qanjamau din yake wannan rawar jikin?Huzaifa d'an'uwana ne, cousin d'inane, bazamu Bari ya auri me wannan cutar ba, ta shafa masa masifa, ita tasan inda tasamu cutar ta"

Tana fad'ar haka, tafice daga office d'in, Doctor yayi murmushi sannan yabud'e wani file yaci gaba da rubuce-rubuce

Motar ya bud'e yasaka ta aciki,har zuwa lokacin Waheeda bata farfad'o ba, Shima yashiga, dube dube yafara anan yaga wayarta cikin hand bag dinta , Kai tsaye contact d'in wayar ya duba, mutum d'aya ne yafad'o masa, dayake wayar Ummah ce yana ganin Ansa Naufal Son,yakira wayar, Babban Yaya yana gida yana motsa jiki, yaga Kiran Ummah, dayake ringing d'inta daban ne, saiya daina abinda yake ya d'auki wayar

Cikin damuwa Huzaifa ya zayyane masa komai, Babban Yaya yadafe Kansa da hannun sa🤦🏻‍♂️yakasa cewa komai,banda innalillah wa inna ilaihirraji'un babu abinda yake maimaita wa a ransa, lokaci d'aya yarasa a'ina yake, a zaune yake ko a tsaye, gabansa banda Dukan uku uku babu abinda yake,Hiv Kuma? Hasbunallah..... yana jin Yanda Huzaifa yake fad'in "hallo hello, baka jinane?"

'Dif yakashe wayar, cikin tashin Hankali yazura kayansa yanufi Airport, ko wanka bai tsaya yiba

** *** **

Suna zuwa gida yad'aukota a hannun sa yafuto da'ita daga cikin motar, yanbiyu dasuke daukan photo a compound sukaga Huzaifa ya 'Dauko Waheeda, cikin sauri suka nufesu, Adede lokacin Didat da kakarsa da babansa suka shigo gidan, ta window din motar ya hango Wani ya dauki Waheeda a hannun sa, tun kafin babansa ya qarasa tsayawa da motar, yabud'e yafuto ya nufesu, yana zuwa ya cakumi wuyan Huzaifa "ubanwa yace ka d'auki wannan yarinyar...?"

Huzaifa ya kalli gaban rigarsa, yaga yanda Didat ya riqeshi cikin 6acin rai yasaki Waheeda tayi qasa, 'yanbiyu suna ganin haka sukai kan yar qanwar su suka cacimeta Sai jijjiga ta suke, Ihsan tayi gudu cikin gida ta fad'awa Ummah abinda yake faruwa, intisar Kuma tayi wajan fomfon da'ake bayin fulawa ta 'Debo ruwa ta watsa mata, lokaci d'aya ta farka tareda sakin wani irin kuka

Huzaifa yakama Didat, suka fara dambe 🙆🏻‍♀�
Baban Didat ya kamashi yace "wuce mutafi gida, banason tashin Hankali son"

Ummah ta qaraso wajan itada Ihsan cikin tashin Hankali take tambaya ''menene yafaru?"Didat dayake ta haki da kumfan baki yace "Ummah saboda me wannan banzan zai dinga d'aukar Waheeda? saboda me Ina son yarinya wani qato zai dinga riqeta"

Cikin 6acin rai Huzaifa yace "nafi karfin a kirani qato, tunda nine Nan zan aure ta"

Didat yanuna shi da hannu yace "Dan zaka aure ta shine hakan yabaka damar ta6a jikinta? Aibaka aure taba"

Hajiya Anty tashigo gidan ta shirya tsaf zata wuce Asbiti, tabiyo wa Ummah zasu gaisa,kamar yanda tasaba, tana zuwa batabi takan kowa ba tanufi Waheeda, datake kuka kamar ranta zai fita, tambayar ta take "meyake faruwa?"

Amma Waheeda tayi shiru tama kasa magana.

kakar Didat ce ta matso ta kama hannun sa tace "muje" ta sake Kallan Ummah tace "Hajiya zamu dawo daga baya"tana fad'ar haka tajuya tashiga motar su, shikuma Didat babansa yakama hannun sa, yayinda Huzaifa yake sake gyara gaban rigar sa da Didat ya cukwikwiye masa, mutuqar tashin Hankali Hajiya Anty tashiga, jikinta Sai rawa yake tana kallon Waheeda, bata taba ganinta tana irin wannan kukan ba, gashi taqi yimata magana, Cikin 6acin rai ta make Waheeda da duka,tace"Dan ubanki bazaki fadamin abinda yake faruwa ba? "

Cikin kuka tace" Wai... Waii.... Ninn nice nake da qanjamau... "ta qarasa maganar tana rushewa da Kuka

Yanbiyu suka zaro ido😳 suna fad'in"qanjamau Kuma?"

Didat da babansa suka juyo da sauri, kowa Idonsa akan Waheeda sunaso suji ta amsa abinda yanbiyu suke tambaya, ahankali ta daga musu kanta alamun hakane

Didat ya kalli Waheeda ya jijjiga Kansa, sannan yayi gaba, babansa ma yabi bayansa suka tafi

Yanbiyu ne suka ja Waheeda sukayi ciki da'ita, gaban hijab dinta duk ya jiqe da hawaye, hannunta ta dora aka, tana rusa uban kuka, Hajiya Anty tabiyo bayansu cikin wani irin yanayi, kwata kwata bata sanin inda take jefa kafarta, kawai tafiya take, Ummah kuwa jitayi kamar tana tafiya akan is'ka, kalmar qanjamau d'innan Sai yawo take acikin zuciyar ta,Huzaifa yashiga motarsa yaja yabar gidan

ihun da Waheeda take ne yafuto da Daddy daga cikin daki cikin sauri, Nan yafara tambayar ba'asi, Amma kowa yakasa bashi amsa, da Yanbiyu da Waheeda kowa Sai kuka yake, su Sa'ad da Sa'eed ma suka futo daga daki kowa yana tambayar ba'asi

Hajiya Anty tadauko wayarta ajaka takira Uncle Usman tace "Alhaji gidannan fa babu lafiya, katashi daga baccin Nan kazo" tana fada masa haka muryarta na rawa alamun kuka zata fara, daga Nan ta kashe wayar ta

Ko minti biyar ba'ayi ba saiga uncle Usman yashigo dagashi Sai jallabiya, Daddy yace "Hajiya, mu duk munzo Nan mun zauna, muna tambayar ku meyake faruwa kunyi mana shiru, Yara suna kuka kunbarsu babu Wanda yake lallashin su"

Ummah ta Kalle shi "Alhaji Wai Waheeda ce me qanjamau..." tana fad'a masa haka hawaye yazubo daga idonta

Daddy da Uncle Usman suka nemi waje suka zauna suna fadin "innalillahi wa inna ilaihirraji'un...."

Hajiya Anty tadafe kanta daya ke ciwo kamar zai fado,Waheeda tanajin furucin Ummah tafara girgiza kanta,cikin kuka tace "wallahi ni banida komai, Allah sharri akamin" yanda take kukan abin tausayi shine yasake karya zuciyar yan'uwan Nata ma, Nan da Nan falon nasu ya kaure da koke-koke,
Ahankali Hajiya Anty tatashi ta janyo ta jikinta ta rungume ta, idanun Waheeda yayi jajir, fuskarta ma haka, Sai ajiyar zuciya take, Hajiya Anty ta kwantar da kanta a qirjinta tana bubbuga Bayan ta, Amma kwata kwata takasa cemata komai, ita kadai tasan metake ji acikin zuciyar ta
Chapter 29 · 0% Book details