← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 68

Sashe 60

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta koma ta zauna dafe da kanta, wanda alamunta ya nuna mini ciwo yake yi mata. Duba da yadda take yamutsa fuska tana girgiza kan nata idonta a rufe.
Ficewa na yi daga ɗakin jikina babu kuzari, saboda magriba ta gabato amma ko sallar Zuhur ban yi ba balle Asr. Ban bi ta kan yarana da na hango ɗakin Inna Kulu ba, arwala kawai na ɗora na koma na shimfiɗa carpet na fara sallah. Raka'ar ƙarshe ta sallar Asr aka fara kiran magrib. Hattama su na yi duka sannan na buɗe hannuna sama ina roƙon sauƙi da sassauci a wurin Ubangiji.
Na jima a kan sallayar har aka kira Isha ban tashi ba, sannan na ajiye carbin da ke hannuna na gabatar da ita.
Zama na yi ina ta zuba addu'o'i'n da ba zan iya kawo su duka a kaina ba. Saboda tunanin Maman Taufiƙ da inda za ta shiga a faɗin duniya idan ta bar gidan mijinta, kuma ta ƙi komawa gidansu ko wurin wasu 'yan'uwanta.
Inna Kulu ta kawo mini tuwo kuma ta matsa sai da na tsakura. Ina zaune a wurin su Aunty Asabe suka zo yi mini sallama za su tafi gidajensu. Sai da safe muka yi suka tafi suna mini addu'ar samun sauyi a cikin rayuwata.

****
Daren ranar daga ni har Umma kwana rabi da rabi muka yi, saboda duk na motsa sai na ji ta ce, "Lafiya?" Na ce da ita babu komai sannan na gyara kwanciyata.
Da safe bayan mun karya ni da yaran, Umma ta ce su yi zaman su kada su je makaranta. Na ce da ita ta bari su je in sha Allah babu abin da zai faru.
Tare da su muka fito Najib ya ajiye su bakin makarantar. Na fita da kaina muka gaisa da maigadinsu na ce da shi,
"Don Allah Baba kada a bari wani ya sake zuwa ya É—auke su, idan ba wannan da ya saba zuwa É—aukar su ba kullum."

"Kada ki damu Hajiya. In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Wannan karon ma don ban san yadda tsarin naku yake ba."

Ɗari biyun da Umma ta ba ni na fito da ita a jaka na miƙa masa. Ya karɓa yana ta godiya muka juya. Shiru ya ratsa tsakani bayan barin mu wurin Najib ya ce da ni,

"Don Allah ki yi haƙuri Maman Haidar, ban ji daɗin abin da ya faru ba."

"Kada ka damu! Ai ba laifinka ba ne. Kawai dai ka yi ƙoƙarin zuwa da an tashi ka ɗauke su."

Daga haka na ja bakina na tsuke, bayan na ce da shi ya kai ni Asibitin Uduth. Kaina tsaye na doshi ɓangaren masu wuta, saboda babu inda ban sani ba a cikin asibitin. Domin awo da wasu ciwukanmu ni da yara duka a nan muke zuwa.
Tun da na tunkari doguwar barandar ƙirjina yake bugawa, na ciro wayata na kira layin da Sajida ta kira ni da shi jiya. Wanda ta sanar da ni wutar ba ta ƙone ta ba, kira ɗaya biyu aka ɗauka.

"Hello!"

"Don Allah Sajida nake nema, wadda ta kira ni da wannan layin."

"Sajida!?"

"E, wadda ta ƙone da wuta."

"Ok! Ke ce Auntynta kenan? To karaso ina dakin nasu yanzu na zo ba su magani."

Maganarta cikin rashin cikakkiyar Hausa ya sa na gano yare ce ita, kuma ga dukkan alama matar ma'aikaciyar asibitin ce.
Da kuzarina na shiga dogon É—akin, ina ta faman gayar da marasa lafiyar da ke kwance suna jin jiki, gwanin ban tausayi.
Na wuce ɗakin na faɗa wani sannan na hango Sajida a kan wani gadon da ke ƙarshen ɗakin. Wani sanyin daɗi ya shige ni saboda gani ɗaya da na yi mata na hango sauƙi. Duk da jikinta da fuskarta duka sun yi baƙi tamkar gawayi, da sauri na isa bakin gadon murmushi a kan fuskata ina jera mata sannu.
Gani na ya sa ta ƙi karɓar maganin da ma'aikaciyar jinyar ke miƙa mata, ta fashe da kuka tana faɗin,

"Aunty kin ga yadda na koma ko?"

"Daina kuka, karɓi maganinki ki sha. In sha Allah za ki ji sauƙi kwanan nan ki dawo yadda kike."

Da kaina na karɓi maganin na ba ta, ganin ta ƙi barin kukan, matar tana murmushi ta ce da ni,
"Kanwar nan naki, tana son ki sosai. Tun jiya take zancen ba ki zo ba, ta damu ta gan ki da yawa."
"Allah Sarki! To ga ni na zo. Me kike so na je na kawo miki?"

"Babu komai Aunty! Daman magana ce nake son mu yi ni da ke..."

"Babu wata magana da za ki sake yi da ita! Baƙar natau mai baƙin nacin tsiya. Macen da ta haɗa kai da ƙawarta suka nemi salwantar miki da rayuwa kike wani rawar jiki a kanta. To wallahi in dai ni ce na haife ki, na raba ki da wannan azzalumar matar, kilibabba, mai fuskar munafukan farko. Allah ya isa tsakaninmu da ke Zaituna, daga ke har Uwarki da ba ta san darajar surukuntaka ba. Wai har ita za ta saka hannu ta daki Mukhtar a gaban kuliya, kuma don an mayar da shi banza a ɗauki yara a miƙa miki. To wallahi ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin karnukan farauta ire-irenku azzalumai, ya ku haram, ya ku halas!"

Sakato na yi ina kallonta tamkar wata doluwa, saboda gaskiya ta sa ban san me zan faɗa wanda zai zo daidai da lafuzzanta ba. Jakata kawai na saɓa a kafaɗa ina murmushin yaƙe na ce da Sajida.
"Ni zan tafi! Ubangiji Allah ya ba ki lafiya."

"Idan ke kike da lafiyar ki hana ta."

Zancen da ta raka ni da shi kenan, har na yi gaba na dawo baya saboda ina so na san halin da Aminu yake ciki.

"Amm! Jikin Aminu fa? Shi ma da sauƙi ko?"

Sajida tana goge hawaye a kan fuskarta da ta sha baƙi tamkar an yi mata fentin gawayi ta ce,
"Yana ɓangaren maza, ya ƙone da yawa ba kamar ni ba."

"Ya Salam!"

Ita ce kalmar da na iya furtawa, ina ƙoƙarin juyawa idona a rufe na ci karo da mutum. Babu zato na ji saukar mari a kan fuskata,

'Tau!!!'

Gabaɗaya kallon mutane ya dawo kanmu. Daga ni har wanda ya yi gangancin saka kuturun hannunsa ya mare ni. Dafe da gefen da na sha marin nake kallon shi tamkar a ranar na taɓa ganin shi a rayuwata. Zuciyata cike da tunanin abin da zan yi na rama tozarcin da ya yi mini a cikin mutane.
Hannuna na ware iya ƙarfina na sauke masa nawa marin, sannan na duƙa a lokacin da zai dawo mini da wani marin, na kai wa jarumarsa kutuball da ƙafa.
Sai ga shi ƙasa dafe da gaban shi yana ihun na kashe shi, mutane suka yo kansa aka rirriƙe shi. Yayin da ni ma wasu mata suka fitar da ni cikin ɗakin ina ƙoƙarin tirjewa. A kan babu inda zan je sai na ga ƙarshen rashin mutuncin da yake taƙama da shi.
Muryar Yaya Maimuna na tsinkayo tana aiko mini zagi, tare da boren da take yi wa mutane a sake ta sai ta kashe ni.
Da ƙyar wannan ma'aikaciyar ta shawo kaina na amince zan tafi. Saboda na kafe a kan babu inda zan je sai Yaya Maimuna ta zo ta kashe ni, kamar yadda take ta ihun faɗa ana tausar ta.
Matar ta raka ni har compaund É—in Asibitin inda ake ajiye motoci, sannan ta fara sauke numfashi tana faÉ—in,

"Na fa'imci kuna da masala a sakaninku. Saboda tun jiya ita yarinyar nata take ta zancenki ita kuma tana ta zagin ta. Dun Allah kada ki daina kula ta wallahi tana kaunar ki da yawa. Mamar ce kawai ke da masala amma ita ma za ta daina ne ki yi akuri."

Zaman jakata kawai na gyara tare da ɗaga mata hannu na fice Asibitin zuciyata tana ƙuna. Saboda zagin da Yaya Maimuna ta yi wa Ummata na shanye albarkacin Sajida ban rama ba. Da kuma takaicin marin lusarin maza, namijin ho-ti-hon da ya yi wa mazan duniya rakiya a tsugunne.

Shin wane ne wannan? 🤔🥲 Yaya Maimuna dai ta hana mu ji maganar da Sajida take son faɗa wa Zaituna🙁😟

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*AM BACK MY FANS.*

*ARBA'IN DA UKU.*

Ban iya zuwa wurin aiki a lokacin, sai gida na koma saboda babu kuɗi a jakata. Kuma ban ce da Najib ya jira ni ba sannan ba na so na kira shi, gudun na katse masa uzurin da yake yi. A ƙafa na yi tattaki tun daga cikin asibitin har zuwa har bakin gate, dalla-dallan motocin alfarma suna ta shiga da fice a cikin Asibtin tamkar ana gasar gwadin ranttsun motocin da suka ji gishiri.
Idan na ga mace da mijinta cikin mota suna hira ko dariya sai na ji sun burge ni. Saboda rabon da na yi hirar arziƙi da Mukhtar mu yi raha da dariya har na manta. Kullum faɗa masifa ne yake haɗa ni da shi mu yi doguwar magana, ba ya shawara da ni, ban san komai a kansa ba duniya, idan ba shi da nake gani da ido ba.
Shigarsa fitarsa duka bai damu da sanar da ni ba, domin wani lokaci ba na sanin ya shigo gida kuma ba na sanin fitarsa. Matuƙar ba ina tsakar gida ko falo ba, wanda babu yadda za mu yi dole mu ga juna ko ba ma so.

Da tunanin na shiga gidan Kawu Sale, na karɓi kuɗin mai adaidaitasahu na kai masa sannan na dawo. Tun kafin na zauna Inna Kulu da Ummata suka fara jefo mini tambayoyin.
"Lafiya kika dawo yanzu?... Ko yau ba a aikin ne?"

Wuri na samu a kan kujerar tsugunno na yi tagumi, sannan na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi na ce da su.
"Asibiti na fito ban je wurin aikin ba."

"Ya jikin Sajidar? Allah dai ya sa lafiya?"

Tambayar Inna Kulu kenan, na amsa mata cikin yaƙe na ce,
"Ita kam da sauƙi, amma mijin nata ne aka ce ya ƙone da yawa. Na so zuwa duba shi na manta shaf sai bayan na fito asibitin na tuna."
Chapter 60 · 0% Book details